← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 176

Sashe 49

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahaka cikin kwanciyar hankli har tagama aiki da dafe dafen abincin daren sa,whith all what umma baraka told her akan ta dage tarike aikinta sai ta mance da fushinsa na dazu da dokar sa na cewa kar ta sake shigo masa daki, ajiye papers din tayi agefe tanayi tana kallon su kamar rayuwanta ne akai haka tayi sneaking ta shiga dakin ta kai mishi babu wani matsala yau a daki ma tasame sa akan black sofa yana zaune as usual remote din tv ne a hannun sa yana cancanza chanels baice mata uffan ba kuma Baiko kalleta ba

Har tagama serving dinshi, yaci abincin baice mata komai ba sai ma taga kamar shirin mikewa yakeyi zai shiga main dakin baccin sa
Ta dan dafe kanta cikin jin dadi dadi aranta "Ohhh Alhmadullhi Kenan ya mance da batun papers din?

Tuni taji wani sanyi na neman mamaye cikin ranta Sai dai Kafinn ta sake wani motsin sai taji miskilin muryansa kamar yace "ina aikana?

Wani Dumm gabanta ya fadi sai ta tsaya kamar wanda aka kira mata kalman mutuwa Gaba daya ta rasa ta ina zata fara bayanin dan sam bata shirya ba.

Amma da shike tasan hala bazai maimaita tambayar ba sai ta juyo ta rusuna kai kadan ta dan kalle sa ta shiga jero ...i..i. . cikin rawan murya tace

"Ummmmm,..sai ta fiddo papers din daga qasar mararta inda ta adana su,tana kkrin mika masa tana magana.."pls im sorry sir....kayi hakku..ri..dan Allah forgive me..
I re_typed it gasu nan sai ta aje agaban sa..
Wani irin kallo ya bi hannun nata dashi Shi dai Bai sauya fuskar sa kalar bacin rai ba kuma yaga typing din was very neat kamar yadda ya batashi a original,karamar tsaki yay sai ya dauke kansa cikin mugun shan qamshi da nuna yana ji da kansa sosai

"..these are not my paper basu na bayar abaki ba"asalin wanda na bayar shi za'a bani yanxu .yana gama fada ya dada tamke fuskan sa kamar me.Sai tayi shiru cikin damuwa,paper ta daga ta dada matsowa daf dasu dama kuma tasa aranta cewa ba a cikin sauki zaice ta tashi taje komi ya wuce ba,ta dada sauke muryant kasa tace Sir...sirr nace wayancan din sun baci sosai..na sake yin wasu ne..pls im so sorry sir..abunda nayi daxu ban kyauta ba

Yayi kamar badash takeyi...maganan ma tana can kasar makogoron shi ba lallai akejin fitar su ba Yace.."papers dina nake so..

Da sauri ta kuma ce masa wayancan sun bace sir

"yace hmmmm Shikenan kije ki cigaba da neman sa inkika samu zaki iya xuwa yin bacci yau

Kaiwa nan ya haura saman gadon sa ya zauna ya barta a tsaye tayi durus kamar wata shanyayya tana bin bayan sa da kallo

'Haka ta ja kafarta cikin dare zuwa industrial building god knows bata ma san ina ta watsa wayancan din ba taci minti arbain tana neman su batagan su gashi fes fes tazo ta samu masu aiki sun tsaftace wajen probably an tattara komai ankai incinerator,da sauri cikin yin shahada ta taho wajen da aka aje bolar,She was reliev dataga ba a kona ba,cikin daren haka ta cuccusa hannun ta a dustbin din yana wari yana tsami ta daure da kyar ta cicciro su

Taga duk sun turmushe sun yayyage sunyi dukumdukun,bata damu ba karkade sukayi tsaf ta mimmikar dasu ta hada su waje guda agefe,tare da wayannan sabhin ta tattara ta koma kofar dakin sa da su
Zuciyan ta na bugu sosai ta shiga sauke ajiyan zuciya
"yaya zatayi ta basa wannan dirty papers din to?Wani zuciyan yace ta gwada takurawa wajen bashi hakuri mana ko zai fahince ta

Haka ta tsaya da su a hannunta ta kwankwansa kofar kimanin minti 13 sannan ya bada izini ta shigo

Yana zaune Ko kayan shi bai sauya ba,ya wani hakimce gaban system yana kallon horse ride tutorial asalin na zaratan mazan turawa

'ita duk wannan bai darata ba domin kuwa tana shigowa batayi kasa a gwiwa ba ta rusuna kan duka kafafuwarta tayi kneeling agaban sa da papers din a hannunta boldly tace

" im back sir,..na same su amma dan Allah kayi hakuri sir sunyi datti,sir nasan nayi kuskure. ....nayi ta gogewa ma yaki fita ne pls am soryy sir,Tana karasawa tayi shiru Thank god dai muryan ta baiyi rawa ba,the embrassment will have been muchi danko kallon arxiki baimata ba bare ya san tanayi.

Haka tayi ta maimaita masa bayananta ta har wajen sau uku,shi baima dubeta ba bare ya amsa.. she became so cold and scared of him Duk Sai ta rasa me ke mata dadi,ranta ya dagule ya baci sabuda gajiya da bacci dake ciccin gangan jikin ta,Sanda taji wani ruwa mai gishiri gishiri nabin labbanta kafin ta san hawaye ne ma suke sauko mata masu zafi,nan ta yi sauri ta goge sai taga ma dada tuluwa suke yi,haka kawai taji takasa hakuri bacci sai galabaita idanun ta yakeyi tana kkrin cijewa ,gashi bata da ikon yin wani rashin kunya ko magana da karfi
Duba da yadda ya basar da existance dinta kamar baima shina akwai abu mai rai akusa dashi ba

Da shirun san sanda yasa zuciyarta ya azabtu sheshekar ta ma a sadade takejan su dan kar ma yaji ta ya harzuka shi yace zaimata wani abu.

Haka ta ci kneeling har na rabin awa agaban sa rike da papopin, idanunta sukayi ja duk sun gaji da fidda ruwa dan kansu suka bushe

Bacci ya dame ta sosai dan tagaji sosai Wani bin ma shiru takeyi dan batasan me zatace masa ba kuma

Shiru shiru tana kneeling har tayi bacci mai nauyi ahaka da paper din a hannunta..

Kafin ya kwanta Yafi awa guda yana kallon fuskarta cikin rasa a ina yataba ganin ta shidai ji yakeyi kamar ma yasanta a wani waje.

Can da asubahi sanyin ac ya wani buso fatar jikinta atake ta farka a gigice ganin inda ta kwana,tasha mugun mamakin ganin shi axaune akan sallaya
Fara kat din jallabiya ce ajikin shi ta masa kyau kwarai bana wasa ba

Cikin rudani ta daga kai sama ta kalle agogo taga har karfe 5.30 ya gauta
Garin mikewa tsaye cikin gigitacen yanayi taji tayi wani tumbul tuni ta sulale ta fada timm akasa ta buga kafarta da drawer gefen gadon sa, it hurt really bad atake wajen ya tsit da jini har Bata san ya akayi kalmar uch yayi escaping bakin ta Gaba daya taji ta a kidime duk ta tsorata da yanayin datake cikin..

..Data ga dai baiya da niyyar kallon ta ko yin magana sai kawai ta tattara kanta cikin sanyin jiki ta tashi ta bar masa dakin sa da tarkacen papers din

Da take fitan ma hanklin ta sam ba akwance ba duk ta kidime tadauka zai daka mata tsawar cewa ta kwana masa a tsakar daki ko yace tafita wajen batare da tambaye shi ba,amma shiru baice mata uffan ba har ta rufe masa kofar ta bar site din..

Tsaban damuwa da gajiya sallah kawai tayi bata kuma hutawa ba ta dawo site dinshi normal aikin ta a kitchen ta shashare ko ina ta kai masa spearmint tea sai Tasamu har ya fita motsa jiki
Nan tadan gayyagara mashi gado kafin dai ya shigo ta kimtsa ko ina tayi waje,can ta wuce dinning tana jiran dawowar sa..

Ko minti ashirin batayi awajen ba saiga shi ya taho fuskn sa normal yana daddana wayarsa,wayar san ya cusa a aljihu sannan ya ja kujeran dining ya xauna a qasaitance
,tana shiru agefe tabishi da kallon kasar ido aranta tace Bataga alaman tausayawa a idon gayen nan ba zama yayi agaban abincin yau kam ma bai bari ta xuba mashi kamar sarki ba shi yayi aikinsa da kansa ya zuba abincin dayawa ko dan jan aji da rigimar baiyi ba ya shiga ci baiya ko kallon inda ta tsaya
Wani shuru tayi a waje guda gim kamar wata gunki

Kare masa kallo kawai takeyi asace har sanda wani dan karamin voiceless cough ya tona mata asiri,ya juya ya balla mata harara a hantare yace get lost tayi sauri ta bar wajen

Hakan ya bata daman hada mashi ruwan wanka kafin ta dawo ta samu ya gama ciye ciyen sa har ya bar wajen

Bayan ta tattara ta kimtsa komai
She have to wait again domin tabashi tarkacen takardun sa

A kirjinta ta rungume su kamar wata tsohuwar headmistress in kauye Chan taje har bakin kofar dakin shi tayi knocking atleast 10 minutes tana tsaye kafin yace ta shigo

Tasamu Har yaci uban wanka ya shirya He is all dressed in casuals,wasu cute dickins nd jones colection rigan ja sosai an rubuta gifted agabanta da bakar wandon sa mai laushi yayi matikar kyau yana zuba uban qamshin turare

Gaishe shi ta sa keyi kafin ta rusuna dan tasan bama amsa ta zaiyi ba.

Cike da jarumta da nitsuwa ta fara magana a takaice batare da tayi bare baren baki ba

Tace sir dan Allah kayi hakuri akan abunda ya faru jiya
Ga sunan,na kawo kamar yadda kace....sai ta danyi shiru don sosai jikinta yakanyi sanyi xuciyarta saiya karye ganin ko daga ido ya dubi inda take baiya iyayi bare ya amsa ta Hasali ma idanun shi ya kai kan system dinshi dake kunne kamar shikadai ne a gaban shi as usual babu alaman rahama ko sauki atattare dashi

Ahaka ta dada taro courage tace nazo na nuna maka original papers din ne,pls may i drop it on ur table?

Nan Ba tare da bata lokaci ba ya dago kansa ya mata wata wulkantaccen kallon daya sata tayi saurin jin haushin kanta na takurawa wajen masa bayanai, da wuri ta sauke kanta kasa a sadade tana jiran jin mezaice mata,a hnkli yayi maganan kamar kalmomin suna fitowa kamar me jin kyashin fitar dasu

"Incinerate it"

Yana furta hakan ya dauke kansa ya dada tamke fuskar sa kamar bashi yayi maganan ba..

Batasan sanda zuciya ta ta furta "incinerate what? ahujajan ta dago fararen idanunta ta kalle shi sai taga kamar ma ba shi ya yi mata maganan ba
Chapter 49 · 0% Book details