← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 176

Sashe 117

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da dauriya ta hadiye duk zafin masifa da hantarar dayake mata ta sauke masa muryan ta kasa kasa cikin sauke kai

"Kayi hakuri baba dan Allah kayi hakuri ka jini, Dama mama na take hannunshi yana jinyarta,Wutar gobara ne ya dan kuskure ta harya taushe mata hanyar numfashi,shine mukazo dashi nan asibitin watanni uku da ya wuce akan zai bata gado anan yana kulawa da ita seni in nabiyanshi kudin magani da aikin da akace za'a mata.

To Ranar nazo haka bansame shi ba,amma ya kirani yace min sunje adubata ne awani waje,kay hkri so nake in ga lpyar mama na,dan Allah ka taimaka min baba dan Allah na roke ka da darajar Allah,sai ta fara hawaye a hankli,can ta rusuna gaban sa ta durkusa kanta tamayar kasa,ya dade yana kallon ta cikin sanyin yanayi dan sosai ta fara bashi tausayi"
gyaran murya yay ya basar me sunan mamankin?.tana tare hawayen ta tace sunan ta wafiyya yace to to,..kidai je waje
Ki jirani tukun
,batare da tay musu ba ta mike sum sum tana tafiya kamar wacce kwai ya fshe mata ta fita waje,ta bakin kofar ta labe cikin rasa meke mata dadi she become so confused nd mixed up,nan ta lafe da bango tafara kirar lambar doc din nan kamar zata kirashi da kurwan ta ya dauka,can aka fara danna mata busy busy,can taga call divert...sai kuma switch off..

Looking so dispointed ga dare na dadayi yasa ta sauke wayar jim kadan tafara shakar muryan mutumin nan ta ciki kamar yana magana a waya,zaira ta taho a hnkli cikin sanda ta kasa kunnen ta tanaji,"wallahy kam
Nima ban tabajin me kalar sunansa ba,amma ka duba mana duka dakunan?sunan marar lpyar wafiya,yay jim can yace to Allah ya kyauta,daga nan bata karajin komi ba sai da mutumin ya bude kofar ya ganta atsaye alamun tashin hanklin da tsoro duk ya dabaibaye ta

Bayabo babu fallasa yace to kinji ance ba a sanshi ba nima danai 25yr anan ina aiki ban taba cin karo da me sunan sa ba,amma kun tabbata anan kikaxo dashi?kuma kinga mamankin tare dashi?cike da fargaba da rawan murya tace eh,muje ki nuna min inda yafara kaiku,zaira tace to ta shiga gaba mutumin yana biyota abaya,zafi zafi da kafartan yake mata ma sam ta denaji sai sauri takeyi har takai mutumin inda da an taga doc saad tare da wafiyya,..suna isa wajen taga
Mutumin ya dan kada kansa,jirani anan ya mata nuni da kujera ya kusa kansa can ciki,

Wannan shine Offishin jamian gwamnati na cibiyar asibitin mai hadin gwuwa na masu karban jinya kyauta da kungiyoyin humanatarian daga united nation comission for fight againts porvety da tallafawa wayanda basada galihu wanda kungiyar human activist suka tanadar

Babu wani suna ko alama da zai nuna hakan ajikin wajen sabida ginin sabone shiyasa tuntuni zaira bata lura da komai ba,sannan yawancin wayanda suke wajen are badly injured or half dead,an sarkafe su a engine ko ansakamusu takunkumin taya numfashi

All she tot was abu dayane ake musu da mamanta,ganin yadda ranar doc saeed ya jajirce anan yana shige da fice she neva imagine dat tallafin jinya kawai yaxo nema ma maman ta awajen gwamanti batare da ko sisin sa ya tabu ba

So wafiya was registerd under wayanda basama da family,yace musu daga kauye ya daukota ta rasa gidan ta a gobara da sana'arta shine ya kawo ta nan ko zasu taimake ta.

Jim kadan dukan wayannan bayanan suka iske kunnen zaira duk dama da kyar kwaklwata ya dauke zancen dan sosai ta rude tana musanta su,babban jami'i mai lura da wajen yace mata tabbas an kawo mai suna wafiyya,amma ba'ayi rgistan da cewa tana da wani family ba,sannan doc said din ya tabbatar musu da cewa taimakon ta kawai yay yanxu haka ma baza'a iya gaya mata komi gameda wafiyyar ba harsai an sameshi
Ya musu kwakwarn bayanai Ya kuma tabbatar musu da cewa yasanta..

Zaira dake jin notinan kanta suna kukkuncewa ta fara kuka tana basu labarin kaf abunda suke ciki batare komi tafara tun daga kan basa kudin datakeyi da cewar shi dayake wai shi jinyar harkan sakon da suke xchnging kaf ta nuna musu komi

Mutumin daya rako tan da jamian wajen duk suka taru suka tabbatar mata
Cewa karya ake mata kuma cutar ta kawai akayi..sukace gwamnati ne ke daukar nauyin komai anan, sannan su kace saidai tayi hakuri ta tafi yau inyaso gobe ta dawo da safe karfe goma sai ayi case din da kyau ,sukace su dakansu zasu neme sa tunda sunada information dinsa na hannun su numbersa dake wajen ta ma duk sun karba,sai suka nace da cewa taje kawai dan bazasu karya dokokin su su gaya mata wani abu akan wafiyya ba for now,se sun tabbatar da labarin..wani complain foarm aka bata ta cika,dauke da numbobinsu suka kuma karbi nata number

Iya raki da fitinan duniyan nan zaira tayi amma basu wani kulata ba,karshe ma data ishe su sai suka sa security suka mata rakiya har can waje bakin titi akace kar akara barinta ta shiga sai washe gari da safe in an same shin..

"
[11/27, 8:14 AM] Pretty KITTEN: Zairah tana tafiya cikin tunani tana kuka dukkkan jikin ta rawa yakeyi inka ganta tamkar wata mahaukaciya at same time Tana tafiya tana kirar lambar doc sa'aed,ta ttuara mai sako,cikin bacin rai amma still off

Almost 7.30 pm ta iso gidan tana ta hawaye,she dint knw how she make it ganin kanta acikin dakin ta kawai ayi akasa a zaune tana tunanin duk abunda aka gaya mata a asibiti,daurewa tay ta shiga bathrum alwala tafarayi ta fito ta gabatar da sallan magrib da ishai wanda shima da kyar ta gama shi tsaban yadda ta fice a hayyacin ta,wani jiiri jiri ne ke debarta yanayin baya da ita kamar wacce ta kwaso giya ta bugu.

Akan daddumar ta kwanta a rigingine ta nade kafafun ta,cikin ta taji na kugi da alamar yunwa na cinta ta daga idanunta taga samn table dinta wayam da alaman ba aiko mata abinci bama, cike da yar dauriya ta tashi ta dau wayarta ta kalla har cikin ranta tna so ta dada tabbatar da cewa abunda taji duk karya ne, tana sonjin ance miskila kawai aka samu
..she is finding it really too hard to accept that all this while doc sa'ad ba taimakon ta yakeyi ba kawai kudinta yake ci,tfita tana jajjan kafarta dayake mata tsami tsami,a sanyaye ta turo kofar kitchen din ganin sa neat da alama baa shigo ba nan ta aje wayar ta agefe ta kunne water keetle tana saurarar sa,caraf wayr nata ya fara kara,wani sauri tayi ta kashe keetl din sakamakon ganin number doc sa'ed akan fasashen screen dinta,hannun data rike wayar har na rawa rawa da sauri takai wayar kunnen tace salam doc,bai amsa ba babu ko kunya a muryanshi ya haura mata da fada,"ke ashe ke dakikiyar yarinyace, Ashe haka kike?wawiya marar mutunci kawai mani zakiyi ma cune?zaira taji wani garas atake ta mugun hade ranta ta fara tuhumar sa da questions kala kala cikin zafin rai da zafin zuciya babu wani boye boye sanda tagaya masa zak zak abunda ake ciki kaf Cike da matsuwa da tuhuma Tace sai kamin bayani wai meke faruwa?ni bangane komi ba kullum naje bakama daukar wayata likita meye gaskiyar lamarin game da abubuwan dana fada kuma ina mamana take zanxo gobe in dauketa nafasa jinyar

Doc yay shiru kamar bai wajen haka yy shiru sanda ta daga wayarta a kunnen ta duba taga call din na reading sannan tayi shiru tana jirar amsar sai taji baice komai ba,..Can taji kamar
ance hahahaha kina jina?zaira tace eh,yace to bari kiji
Ni da kike gani na ba kanwar lasar ki bane,,yarinya na wuce saninki,ni baqin qumurcine da ba'a turmusa shi nace kibn jikinki kika zage ni yanxu n da nace karki na zuwa asibitin ba kinki ji ba?wato kina so kiga iya kurewa ta ko? Danai miki sauki ban walkanta rayuwarki ba shine har kinje kin dauko mana wani cleaner daga offishin directa yaxo har yana samin ido ko?to kinyi makanki,..

Kuma daga yau kisani Duk abunda kikaji a ofishin nan gaskiya ne,ni bana aiki da asibitin su,yaudarar ki kawai nakeyi dan in dau fansata sannan register kawai nayi ma uwarki dan ki yarda dani naci kudinki na koya maki hankli dan haka kisani Kudin ki na banza ne,ko sau daya bai ma uwarki amfani ba

"wani tamfatsaen tsawa ta daka mai
Kai dakata malam ni bazan saurare shirmenka ba dan gobe goben zaka san ni ba kanwar lasar kabane,u better prepare to pay kuma ka tabbata mama na tana cikin koshin lpya,ai bakafi karfin hukuma ba wani tamfastsem dariya ya fashe mata dashi wohoho yaro man kaza,to bari in miki gwari gwari
Ni ban kira dan muyi musanyar yawu ba,na kira ne in tabbatar miki da cewa gaskiya ne kudinki kawai nakeci,sannan uwarki tana hannu na can a asibitin mabarata na ajeta tuntuni,ynxu da kikaje kika baza maganan a asibiti magulmata sukaji na dagata na kaita wani waje,wayancan jami'an da kike gadarar zasu taimake ki to ki shafa kiji nine ma ogansu kuma harkammu daya yaudararki sukeyi suma suna sane sarai da abunda ke faruwa kuma ina gargadin ki muddin bakije kin goge maganan nan abakin mutumin nan da kikaxo musu dashi jiyaba,na miki rantsuwa keda ganin uwarki sai a lahira...

Numfashin xaira ya fara haurawa can sama sama ta fara bari sosai,can maka mugu azzalumi Allah saiya saka min, inba ana jinyar dole ba aisaika ban mamana...da balain karfin zuciya ta furta hakan

Yace tirr in baki ita kin gama biyana ne?ai saikin biyani kudin ki na wata biyu caaass kamar yadda mukai kamun ki sameta,wani kukan dabata sanda shi bane ya kufce mata,jin haka ya dada azama sa ya fara fallasa asirin su kaf sunayen masu taimaka masa da irin manakisar da suke hadawa a asibitin sanda ya fada da zimman ya dada tsorata ta...
Chapter 117 · 0% Book details