← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 176

Sashe 67

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan ta jajjawo soft chairs da tables,ta hada mini working table shima agefe,ta daidaita electrical connection da main pc dinsa da sauran gadgets kafin kace wani abu har komi yayi daidai,to dake dama Allah ya bata ilimin sarrafa kayan computer Bata dau lokaci ba ta sauko ta sanar dashi cewa ta gama,ba bata lokci ya tashi tsaye zaije dubawa ya kalleta"Yace Follow me..zaira ta shiga biyo sa abaya atare suka shigo har cikin dakin,Yaga babu abunda baiyi masa daidai ba amma tsaban kwaikwane da yawan complain saida zairah tayi awa biyu tana aikin zagaye sabida babu wani abu dabaiyi korafi akan mazaunin sa ba

Ba ita da barin dakin ba se karfe daya da rabi,hakan ma sallah zuhr shiya rabasu With lots of work files akan table daya ajiye yace mata in 10 min ta dawo ta deba daniel zaizo ya dauketa takaisu asibiti

Minti goma kacal ya bata,kuma acikinshi
take saka ran zatayi wanka zata kimtsa
To ko gama idar da sallahn batayi ba taji anata buga mata kofa da qarfi
.,"zairah are u der..kiyi sauri oga yana ta masifa
,tsaban sauri
da hijabin sallahn ajikinta haka ta fito

dakinshi ta nufa ta kwankwasa kofar ta shigo,no one was der Taje ta debi tulin file din daya ajiyen ta fito suka nufi WIN hospital dake asibitin anan anguwar da suke yake

,"...daniel yana parkin ta fito ta shiga biyosa abaya zairah tana ta kallon tsaruwar wajen sabida ya gama burgeta amma sam bata da lokacin yin masa wani isashen kallo,tana shiga daniel ya kaita wani office acan sama saida sukayi sallama sau biyu sannan ma aka san dasu...'Come in"
Muryan mace ya umarce su ciki
Gefe daniel yy yace.."gud mrning maam,zairah ma cikin sanyin murya tace"gud mrning.
dukan su ba a amsa musu ba sai sukayi shiru suna kallon
ta,"babbar mace ce zaune akan black leather arm chair Basai an gaya maka ba kasan babban likita ne kuma musulma anrubuta doctor noor dawood gaban identity palate din ta

She wore a white mini hijab akan wani nice xpensive gucci suite baki wanda ta dora hadadden lab coat din ta akai idanun ta sunsha fararen gilashi hannun ta dayasha agogon gold na rike da golden pen tana rubuce rubuce..."yes daniel where is d girl?batare da ta dago ba ta furta hakan Daniel ya juya ya kalle zaira, yace yes maam gata nan..."go on" ya fada mat zairah a hankli kamar baison ajisu..zaira ta matsa kusa da teburin matar ta tsaya se kuma ta rasa me zatace dan bata gane komi ba, dan lumshe idanun tayi ta kuma sauke ajiyan numfashi tana budewa da fararen idanun matar taci karo akanta"..ke ce ko?kafin zaira ta gyada kai ta amsa matar tace "have a seat"...ba musu zaira taja chair ta zauna.."u can drop ur files,"after like 3 mnt tace daniel ure dismiss, yace thank you maam sannan yayi waje..wani shiru wajen ya dauka kafin matar ta gama rubuce rubucen datakeyi ta kawar da komi gefe

Ruwa ta dauka a gora ta kwankwada sannan ta aauke Ajiyar zuciya ta jawo babban apple laptop me tambarin WIN abaya ta kunna,after like 5 minute ta dan leko ta kalle zairah
"Yan mata bude can ki dauko sauran files din,Zaira tace ok sannan ta mike
Ta isa gaban wani katoton file scrolls tsaban ya hadu kamar show Glass haka akayi mabudin dan haka ta budeshi ahnkki kuma cikin nitsuwa,ganin tarin file din dake tamke a ciki sanda taji gaban ya fadi,ba shiri matar ta umarce ta data fitar da kowanne,taci minti talatin a tsaye sabida yawan su kuma in ta cire akasa takejerasu.

Cike da gajiya take maganan zuci
"Kome za'ayi da wayannan file din oho,aikuwa tana kammalawa matar ta sakata agaba danko zama bata umarce ta dayi ba,one by one take daukawa tana karanta mata wasu abubuwa daga abunda yake ciki in review foarm suke duk dama bata san komi akansu ba
Da alama matar ne take daukan wasu bayanan nata akan computer ta still wani bin ma seta tsaya tayi nazari sosai sannan ta shigar da abunda zaira din ta karanto
,abun duniya duk yabi ya ishe zaira tarasa yadda zatayi,da Alaman wayannan delicate medical files ne daya kamata shida kansa ya aje yayi aiki akansu amma tsaban baida lokacin su yasa suka taru sukayi yawa,zairah tana ta karatantawa amma kamar batayin komai,har bata so ta juyo ta kalle gefe taga abunda ya rage,her leg became so sore nd heavy tsaban tsayuwa kuma matar bata ko kulata ba bare tace mata ta xauna,after 3 hrs lokacin fuskn zaira ya takune yay lui babu maraban sa dana wanda zai fashe da kuka,gashi saura files kamar guda arba'in ne akasa,matar ta mike tsaye dan fita break jim kadan ta dawo tare da wata nurse"Gata nan sai Kuje kiyi sallah..

Zairah ta amsa da toh tayi Marmaza ta bi bayan nurse sukayi waje tana ta leke ko zata ga wani wajen saida abinci amma bataga ni ba ,dan wani tsukun dakin allura nurse din takaita ta shimfida mata sallaya ta mata nuni da bayan gida anan tayi alwala tayi komi ruwan alwalan tadan sha kadan
,zaira tana sallamewa ko minti daya bata kara ba nurse din ta leko ta tsaya mata akai."muje ko"ta gyada mata kai Ga gajiya yunwa da komi amma haka ta mike suka koma ciki,nan ma wani sabon aikin aka bude mata sede wannan karon matar ta bata ixinin Zama akan kujera,shiru shiru,lokaci nata tafiya 4..5..har sanda karfe 6 ya buga sannan suka kammala komi

Nan ne ma matar ta lura da yanayin zairah sann ta bata ixini akan ta bude fridge ta dauko ruwa mai sanyi tasha,zairah ta bude fridge din tanata kallon soft drinks da velvet cake da short bread biscuits yadda aka jera su kamar kasa hannu ka dauka,wani kuuu hanjin cikin ta suka bada sauti,She look so weary nd tired, kuma tsaban ta jigata sanda labban bakin ta ya bushe yayi kayau,gajiya da yunwa ne suka mugun galabaita ta,ta bude goran ruwan tana sha wani haushin matar ne ya hadu ya tokare ta a kirji

"How unconsiderate of her,ace mutum tun safe yana aiki dakai baka damu ka bashi ixinin yaje ya ci abinci koya huta na minti daya ba,aiko da bazata bani abincin ta ba zata barni inje in nema awaje"this is not fair att all,kuma duk rashin sanin komi a wajen shiya dada karya ma zaira gwiwa cos evrything is new to her ita tun da aka haifeta ma bata san da akwai nan anguwan bama..

Bayan tafito Waje kulawar arxiki bata samu daga wajen kowa ba har daniel ya zo ya dauketa suka wuce gida,abakin gate daniel ya doka horn da alamar babu gate man Kirjin zairah ne ya kuma bugawa data tuno da maganan da nashwan ya gama gaya mata dazu,
"U will do evrything"
Ji tayi kamar tasa hannu aka ta kurma ihu,daniel yayi marmaxa ya bude gate din shima kamar yanayi yana tsoro suka shigo,ya kalle zaira dake shirin sauka
"Kije ki rufe gate oga ya ce a aje miki keys ya mata nuni da stall din baba mai gadi sannan ya wuce yayi tafiyar sa,har gaban gate din ta karasa sannan ta soma ja da iya karfin da Allah ya bata dan bata san ko nauyin gate din bane ko dan uban gajiya da yunwa bane yasa takejin ya mata muguwar nauyi
Tana gamawa ta nufi cikin gidan da ar sallama,jin karar tv ya sanar da ita cewa yana falon data shigo ta kalle sa seta ta dan ja gefe tace"Gud evening sir
Bai dago bama tsaban yadda ya kafe idanun sa akan laptop dinsa yana danne danne After like 10 secnd yace evrything done?tace yes sir.Shiru ya kuma yi sanda yadan ja lokaci..
yace"I need food"

A Sanyaye kamar bazata budi bakinta ba Tace ok sir,atake ya dago ya bita da wani muguwar ido ganin tana nasa saibi, yace"i said Now im giving u 20 minutes,"zairah ta ansa da dan karfi,ciki ciki yace kije zaki xo ki gaya min abunda ya hanaki yimin lunch yau"..kirjinta ne ya wani buga se batama amsa shi..a hujajan ta zame ta bar wajen,ji take kamar zata mutu yau tsaban takaici haushi da gajiya,
sha'awar komawa dakin ta ma bata ji dan har iyanxu ji take kamar purnishing dinta yakeyi sabida biye ma laushin gado datayi tayi wasa da aikin ta..

tana shiga kitchen ta cire hijab dinta ta samu socket ta jona water boiler, in few minute har ya tafasa by then tagama dama
Custard dinta da tsabar tsoron kar axo akamata tana cin masa abincin gidansa sai bata iya saka masa madara ba,sugarn ma adofane ta zuzzuba da zafi zafin sa ta shiga rusawa acikinta,jim kadan kamar wacce aka watsa ma ruwa haka zufa ya tsassafo ya wanke fuskarta,ajiyan zuciya kawai ta saukewa tana jan numfashi.

To Iya dn karfin data samu kenan ta jajjaba masa irish patotoe poridge da asalin ganye da busashen kifi
Sai tayi pineaple nd
Ginger drink kawai ta matse dan su akwai enginan yinsu asaukake,shap shap tabi kai da ice blck cos iya mintinar daya bata basu da wani yawa baifi saura minti biyar bama,haka ta dauko abincin ta kawo masa dinning ya gama kallon abincin
Sannan ya dubeta

Yace bai masa
Wai tuwo yake so
,karshen ta ma daniel ta xuba poridge din dake shine yake tare dasu a gidab yana driving din nashwan yana runing wasu kananan aiyukan da da can ma'sud ne yakeyi,haka tayi tuwon kuma tayi masa miya kusan kala biyu,kuma duk da haka bawai ya nuna qamsuwar sa bane,he look so unintrested ayayin dayake ci,kamar xaici kamar bazaici ba ahaka yafi awa guda yana caccakawa da cutleries zairah tana gefensa tana tsaye,finally arnd past 10 na dare ya tashi baiko kalleta ba yabar wajen ya haura dakin sa,tayi sauri ta tattara komi ta aje su a sink top
Batama tsaya yin wanke wanke da goge kamar yadda ta saba,sauran abincin daya ragen ta ci,sann ta saka dayan miyan a fridge nan ta ja kofar kitchen ta rufe ta nufi dakin ta batare da tayi komi ba.
Chapter 67 · 0% Book details