← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 176

Sashe 22

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayayin da programe ya soma zafafa mayor Aseem bai bata lokacinsa ba ya soma cuccusa nashwan akan harkokin businesses din da yakeyi saidai har yau akwai amanan su na tun abokan takar su da abokan sa dabai watsar dashi ba shiyasa yau ya saka nashwan din ya saka hannu a charity nd human development businesses dayawa amma kwata kwata bai sashi a miyagu ko kazaman harka ba.

Shi babban burin sa yanzu shine BMF ya farfado yasamu ya mallake dukiyar hakeem wamako wanda badon sumewar da nash yayi a kauye ba hala da an wuce wajen a yanxu

tsaye suke agaban top business men suna tataunawa sukaji wata husky familiar voice yana tunkarasu

"Assalamu alaikum..

da sauri nash ya waigo jin muryan lawyar mahaifin sa mr mahdi yazid abayan su"

"wasalam"
Duka aka amsa shi bayan nan kowa ya dauke wuta basu ce masa komi ba,da karamin murmushi nashwan ya bashi hannu yace "hi mahdi"..dan ajiyan zuciya ya sauke yanata kallon sa yayi double smirks
Yace..to sannu da zuwa..Mr mahdi ya tamke hannun sa in a warmer hand shake yanata kallon yanayin sa yace thank you KON,yana me dada jadadda kalmar K.O.N din duba da yadda wasu agefe suke binsa da kallon takaici,"can i see u in private pls?

Nash ya gyada kai
ayayin da kowa awajen ya bisu da wani irin kulallen kallo wanda basai an fada ba kusan dukanin mutanen mayor aseem basa son mr mahdi Dan mayor yasha gaya musu cewa mahdi ne munafukin,kuma shi yake xuga nashwan akan karya saka qaddarorin sa da na wasu bare acikin harkan BMF shi kuma ayanxu ya riga ya cika musu kwakwlwa da karyan cewa yana so ya kawo jama'a cikin harkan ne sabida kowa ya mora arxikin sa ajikin jama'ar kasar sa.

Yace yanxu shi daya ya rage cikin abokan sa amma nashi kason 20%ne kawai,kuma part din mayor wasim is a lost,nd a heir of 60% share na bmf din hakan yana nufi nashwan yafi shi karfin yanke wannan hukunci na tada wajen

Ajikin Wani Katoton zanen tambarin BMF da akayishi da shiny golden Tabard wanda yake killace kamar amarya an sakaya duk jikin shi da huge silk banner
acan tsakiyar filin akayi attaching dinsa da katoton bugle inda dole idon kowa ya haura kai

Ajikin abun nashwan da mr mahdi suka tsaya wani Kallon kurel ya masa sannan yace
Son Are u ok?dan shiru yayi yanata kallon sa like he have alot in his mind amma bai san meye zaice ba..
boyayyiyar ajiyar zuciya ce ta kufce masa a hankli cikin nitsuwa yace mahdi
Yaushe ka dawo..na dauka ma bazaka zo nan ba...so whats happening?

Mr mahdi ya murmusa yace
Hakki ne akaina in zo nan.. I dint come to party thou.

'So meke faruwa?nash ya mayar masa tambayar a dan shashance kuma cikin sauri
shikuwa saida ya nitsu sannan ya fidda takarda daga aljihun wandonaa ya mika masa yana me cigaba da maganan sa but in a cooler tune alaman baison ko acikin kuskure ne wani yaji shi.

yace nashwan
nazo ne in maka tuni akan maganan mahaifin ka..nd i can see u have alot of talented business investors here...
Mutanen nan sunxo ne duk dan su cuce ka ta inda zasu samu damar gurbata tsaftataciyar dukiyar mahaifin ka daya bar maka amana danasu kaxamin dukiyar...

Ayanzu ka amince kaine jigon BMF ko?in babu kai babu wata magana da zaiyu anan"nawa dai In fada maka gaskiya ne,i have no right to stop u akan duk abunda zaka yanke'..."bt son u hve to think abt ur father kafin kace zaka dau wani kwakkwarn mataki..is vry important pls..
..mahdi ya karashe maganan yana satar duban baya da gefen gefen sa dan ya kayyade iya mutanen da suke kallon su

Alokacin Idanuwan nashwan akafe suke akan takardan yana karantawa dan haka baice mishi uffan ba amma zuciyar sa bakaramin nauyi tayi ba.. ji yayi ya dada yarda da cewa muddin da babu shi din to lallai babu BMF tunda 60% na shares din nan na shi ne Dama can shifa wannan abun badamun sa yakeyi ba .

Wannan Takardan alkwarin da iyayen su suka dauka ne tun tale tale akan BMF bazata taba zamowa class of business ma yan kasuwa ko gwamnati ba koda kuwa bayan ransu ne

"U are the real BMF Nashwan wamako.. pls Kar ka taba mantawa da abun dayake cikin wannan takarda.
I have to go..
ansamana idanu dayawa

Nashwan yace
"Ok Thank you.
Nan su kayi sallama mr mahdi ya fice abunsa, nade takardan yayi ya cusa a aljihun wandon sa sai ya koma wajen mayor Aseem da zimman dada gano manufar su shida mutanen sa

Sosai mayor Yaso yaji abunda suka tattauna atskanin sa shi da mr mahdi amma kuma yasan baxai tabayin tsammanin ji abakin nashwan din ba

Dan haka ya basar da komi cikin salo irin nasu na goggun manyan qasa,Atake ya shiga kawo hirar cigaban da BMF da can ya kawo a matsayin idon mikiyar wannan hidimar ma abokan sa na arxiki kuma

Hakan Shi Ya dada jawo mahaukatan masu kudi da mahandaman share
Holders da sarakuna dabbaka kwadayin su na son shigowa cikin sabuwar salon cike da mummunan burin su na son saka hannun jarin kamar yanda sukayi ta dora buri tun da chan abaya da rayuwan mayors guda ukun nan bai watse ba

Kowa yasan Kamfanin BMF na kasuwancin mutum
Uku ne,amma da shike anga duk sauran sun shude kuma ana saka ran mayor Aseem ya mallake nashwan a matsayin dansa kuma bazai taba iya kasuwan cin shida nashwan din kamar yadda yace ba, sai kowa ya hau dokin kwadayin son shigowa cikin sun kai da fata,wannan kusan wata babban dama ce wanda kowa baiso ayi bandashi dan an dade ana kwadayin shiga din amma sai ba'a samu wani hanya ba.

anan kowa yafara saka BMF a jerin babban burikan kasuwancin sa na nan gaba Wasu har sun fito fili sun nuna maitar su wasu kuma sunata bidai a hankli tunda kowa yasan nashwan ne mai 60% na arzikin kamfanin har yanxu
Ba mayor aseem ba kuma nashwan yaki ya sake cewa komai akai ko yanxu ma ido kawai yake binsu da shi

Jikin Mayor tuni ya riga ya basa cewa Zuwan attorney mahdi cikin taron ya wargaza masa komai mussaman wajen fallasa manufar sa na cewa dayayi shida nashwan ne kadai zasu tada BMF kuma yanasane da hakan yayi ne dama danya samu amincewar sa a ranar da zasuje kauye,shi dama bawai ya fito fili ya sanar da nashwan din gaskiyar cewa wnn karon zai karbi hannun jarin sauran mutane bane.

A tunanin nashwan su biyun zasu daga abunsu tunda dama na family ne amma yau da aka zo partyn clearly nashwan ya fahimci cewa mayor aseem yanada wani boyayyar manufa akan bmf wanda bai sani ba duk dama hakan ta dade acikin manyan harsashen mr mahdi

Haka mayor yayi ta amfani da wannan daman in evry little conversation kamar ace suna hira da wani shahararen king to bayayin shiru da bakin sa akan nashwan, sai yayi ta hanyar da lallai wayannan manyan mutanen zasu sa masa baki wajen yi masa tuni da nasiha akan muhimancin kara tada BMF dan haka nashwan baima samu daman zama ba trout tare suke da mayor yajasa nan yakaisa nan har ma zaka rantse kace hala nashwan babban dansa ne

Saidai haryanxu ko sau daya nashwan bai budi baki yayi wani magana me ma'ana ba,shiru hka nan xaka gansa komai akace baya bada tabbacin sa akai.

Fannin jasmine kuwa da rayuwar yarta hanadi ta damu dan itakam tasan tariga takai kololowar cin nasara arayuwan ta

ta dade da aikawa akan akira hanadin amma sabida tsananin son jin gulma sai tayi burus batazo ba,can data gaji tazo daknta ta same ta tana tsaye da wine glass ita da manyan kawayen ta
Subaya,sameena and Aleesha babu abunda suke sai gulman nala khaleepa da irin kayan datazo da shi
Suna cikin haka sukaji murya akan su

"HANADI, da sauri ta juyo setaga maman ta. Can i see u"..lady Jasmine ta furta tare da sauke karamin yake tana jefa mata hararar kasan ido,ajiyan zuciya hanadi tayi tace ok mum,nan ta taho ayangace tana furta xcuse me guys ma kawayen ta

tana barin wajen aka cigaba da cafter nala dan sosai take basu haushi gashi itakam tunda taxo bata zauna ba she act very classy sosai take nuna wayewar ta wajen iya muamala da mutane bata wani damu da yarantar banxa ba

"Mumy ina zaki kaini wallahy na gaji"...Cike da sakalci hanadi ta furta hakan tana yamutsa fiska inda lady Jasmine tayi banza da ita dan yau batajin zata iya amsa wani kwainanen maganar ta ita dai ta tsani laxiness da rashin kamun kai
Irin na yarta hanadi.

suna daf da isa sashen mutanen ta na fashion ta saki murmushi mai fadi
Ta cakka ma hanadi mutsini a baya
..cikin salo tace mata.."Behave..

Hanadi ta juyo zata amsa taga ashe ta furta maganan ne batare da ma ta kalleta ba amma dai tasan da ita tayi,hakan yasa hanadi ta nitsu ta biyo bayan ta cikin taku dai dai

"Hello hy guys .

Zunzurutun gawurtacun fashion designers da brand owners duk suka juyo suka kalleta

Lady jasmine tana murmushi tayi numi da hanadi
"wannan ce yata danake gaya muku"
She is Hanadi Aseem mimiko..
Hanadi tayi wani yaken bazata
..kusan mutane uku ne suka miko mata hannu inda ta gaisa da kowannen su a sama sama

Lady jasmine kam bayanin ta ta cigaba dayi tace "yata ma tana cikin wannn babban harka tamu ta isnt dat amazing?
...yeah yeah..
Duk akayi cheering ana mata murmushi dayawa suna ce mata congrats

"She will soon be the top fashion designer of south song nd of couse the BMF investment proposal da zamu tada nan gaba"..so ku shirya fa domin daga BMF ya tsaya kusan kowani rana my doter here will give u a grand fashion show...

Hanadi ta sunkuyar dakan ta kasa tana murmushi jin babban karyan da uwarta ta sake.
Chapter 22 · 0% Book details