← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 176

Sashe 165

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka dawo dakin Duk dama ya amince amma kallo daya xaka masa kasan baiso ba,shi dai bai son abunda zai rabasa da daya daga cikin su koda na yan dakika ne,zaira ganin sun ta tsakiyarsu kirjinta ya fara bugawa,su biyun suka lallabata da maganan akan ta shirya taje,zaira har kuka tayi ma wafiya tace ita bazata je ba inba dai tare su ukun zasuje ba,but haka wafiyya taki mata fir ta rinka mata alkwarin zasu zo daga baya...
Nashwan ne ya tattara mata kayanta shima yana me kara lallabarta
Da cewa zaizo Adadi babu dadi da kumbure kumburen fuska haka dai ta bar gidan tabi wayancan mutane suka tafi..

Kwana biyu bayan tafiyarta sosai wafiyya tayi fama da shi sakamakon rashin samunta a waya da akeyi da kyar da fitina ta ganar dashi cewa cikin babban daula zaira take zai iya yuwa sun hana reaching dinta ne for strict security reason,bai sani ba ita kullum takanji labarin lpyarta awajen mr mahdi.

Dan mas'ud ya gaya masa cewa har wani karamin biki akayi na tarbanta a can daularsu, sanann tun da tazo ake nunata ma yan uwa,sashi sashi na masarauta kowa na tururuwar zuwa ganin ta a inda take,sanda aka ci sati guda ana abu daya kafin duk zuria suka san dawowar ta....
Wani bin wafiyya sai taga kamar baida lpya dan tunda zaira ta bar gidan yafara shiru shiru da shegen son kwanciya mata a jiki
Dama can bata fiye sa masa baki akan maganan gina north dinsa ba but danta kaucar masa da yawan tunanin matar sa daya kwallafawa ransa yasa ta fara involving dinsa cikin maganan business da louching din north din Hakan kuwa sosai yay motivating dinsa ya fara sa hanklin sa akan abubuwa dayawa bisa shawarwarin data dinga bashi wasu takan masa misali ne da yarda mahaifin shi yayi nashi mulkin cikin jarumta.

***
Fannin mayor Aseem dama ko ajikinsa dan tun asali bai ji dadi da hanadi tace wai har sai nashwan ya dawo daga tafiya kafin ayi meeting din ba,kawai ya aje ne akan bata isa da shi bane,haushin ta ma yakeji sosai aransa,..duk gari an karade da labarin cewa an gama gina north tun kan lokaci saidai rashin fitowa da cewar nashwan komi yasa media da yn jarida suketa kame kame.

Kwana biyu wafiyya bata ga mr mahdi ba hanklinta saiya fara tashi ta shiga damuwa dan bata tabaji ya kashe wayar sa,koda wani waje zaije yakan fada mata anma sai gashi tun jiya take neman sa kodan ma taji labarin zaira amma shiru.

Wani babban case ya hada wanda yazo ydan dameshi but as an xperieced lawyer sai yake ganin hakan shine kawai musu mafita
Akan case din gawar nail khalefa ne da suka hada baki da PAn boss suka ajiye,tunda yaji kishin kishin cewa boss yana hanyar dawowa neman dan sa nail ya kasa samun nitsuwa aransa,ba sani ba sabo ya kuma kwakwalo criminl case file,dan ya daure wuyar pAn boss da wasu legal crimes dinshi na saida kwayoyi da kisan kai dayayiyyi aka danne,yace in yana so ya rufa masa asiri akansu saiya bashi hadin kai akaro na biyu sun hada fada tsakanin mayor aseem da boss khalepa akan mutuwar nail...

Ranan da mr mahdi ya bayyana sarari aranan gari ya dauka da news din mutuwar nail khaleepa cos he make sure dat komi anyishi ta inda zargi bazai taba hawa kan nashwan ko wani ba.

Boss khaleepa cikin tsananin jimamin ganin busashiyar gawar dansa da aka kawo masa a kwati suna sauka a jirgi sumewa yayi sai bayan da ya farfado suka samu aka binneshi, tsaban ya raunana da afkuwar abun sai bai tsaya yin wani tunani ba shi duk abunda PAn shin ya zayyana masa ahaka ya dauka ya rike...

Yadda zaka san PAn shin babban makiri ne baiyi koda batan kalma akan yadda ya tsara lamarin ba,
Yace ai tun tafiyar su yaketa binciken inda nail yake da gang dinshi,shine garin binciken har ya samu labarin cewa da hannun mayor aseem acikin lamarin mutuwar sa yana dada kafa kakkarfan hujja da zakuwar da kowa ya san myor yay akan maganan tada BMF,probably bazai taba bari nail ya taba nashwan ba.

Boss khaleepa was really pained sanin cewa koda ya tabbata mayor ne yayi kisan nan it will alwys come out clean witou any evidence,duba da matsayin power sa,da munafurcin sojoji na iya murkushe laifi suyi shiru kuma aga kamar basu suka aikata ba,sosai yaji zafin abun nan aransa,wannan wani babban zunubi ne da aka aikata masa wanda yake ganin kamar daukar fansarta bazaiyu da gaggawa ba,dat millitary solidarity ba kamar nasu da ake zuwa gane daga baya har a aje criminal record akansu ba amma yau yasha alwashi koda abakin ransa ne sai ya dauki fansar mutuwan dansa kuma cikin gaggawa,ga yarsa nala data kwanta ciwo anrasa gane kan ciwon,sanda aka zo aka san da mutuwar nail kafin likitoci sukace masa wai normal ne in ma zata farfado to sai kurwan su yadan rabu da juna.

Shikadansa da mutanen sa yayi jimamim mutuwar dansa kamar baqin kafiri kwana bakwai sukayi suna saka bakaken kaya,wat pain him d most shine kowa ya masa ta'aziya,da abokan shi da makiyanshi amma ko kare bai kira daga South song ba bare suzo yi masa jaje,that terrific feeling of knwing that thy r responsible for the demise of his son kuma yanzu kmar sun nuna ma duniya cewa mutuwar dansa ba komi bane awajen su,hakan ya bakanta masa rai bana wasa ba,he was bitter abt dis daga ya zauna saidai kaga yanata shan giya masu zafi da daci,ganin nala kwance ma dada haukatasa yakeyi..

A fannin mayor kuwa ganin har anci sati guda nashwan bai hadu da hanadi anyi magana ba zakuwar san nan ta tursasa shi ya kira doc kaber ya umarceshi da yayi ma banafsha Alluran nan da suka shirya,so innocent ranar dan complain din ciwon kai kawai tayi,sai lady jasmine ta hau kai tasa aka mata alluran agida shine tun lkacin har yau banafsha bata gane jikinta ba..

Za'ace ma Kusan abunda ma ya dauke ma yan SS hankli kenan kwana biyu,daga ciwon kai ciwon sai dada zanca salo yakeyi with each mrning yarinya tana dada ragwabewa an rasa gane meke faruwa da ita,doc kabeer sai zabga masu hanadi dasu abhay karya yakeyi kwananta hudu kwance gida aka kaita asibiti aka bata gado,...
Hankalinsu ya tashi sosai da akazo ma aka dena barin kowa yaganta lady jasmine cikin hada manakisarta ta bada umarnin karma agaya ma nashwan da mahaifiyarta fulani har sai sunji asalin menene kan ciwon...

Ranar da burial din nail ya cika 10 days cif ranar boss khalepa yaje mafia meeting dinsu na kungiyar asirin dayake ciki mai suna"HOLYBOSSES" aka masa wankan tsafi na daukar fansa ya sha jinin jarirai,daga dawowar sa ya maida dukan arzikin sa da qaddorinsa akan sunan nala as the only heir na komi nashi a duniya koda allura bai bar makanshi ba..
Ya riga ya sadaukar da ransa da zuciyar sa akan cewa lallai zai dau fansa ma dansa ko yakashe ko akashe shi.
Nala tana cikin gigin ciwo amma haka ya zaunar da ita ya gaya mata sirrin komi na gidansun harda kudaden da dake boye wanda baitaba kaisu banki ba,shidai bai gaya mata yanzu filin yaqi zai shiga da SS ba kawai dai ya gaya mata cewa zai nema masu mafita zata iya yin komi da kudade da abunda ya bar mata koda bata sake ganinshi ba,a ranar still daga asibiti fannin su doc kaber result din ciwon banafsha ne ya fito,kamar dai yadda suka tsara da su mayor a tun farko aka baza abun a media da zimman nuna kamar basu taba ganin kalar cutar ba bayanai kawai likitoci suka dingayi akan ciwon
Inda ya jawo mutane dayawa suka balain tausaya ma banafshan...

Nashwan yana gida yana sha'anin sa da maman baima ji ba bare ya gani,don tunda zaira ta tafi basu fiye mazaman daki ba saidai su fito farfajiyan gida ko garden dansu yi hirar su

Ko hanadi da ba wani sonta takeyi ba saida taji hanklinta ya tashi ganin ranar da aka nuna musu ita kamar ba ita ba.

Da zarar jinin ya langwashe ya fita daga asalin shape dinsa shikenan ta fara ganin azaba kenan kala kala She is in pain all over her body,duk ta galabaice idanunta yay kwarmi ta rasa meke mata dadi a duniya gashi saida taimakon machine take numfashi...
Daga ta samu sararin magana ta rinka kuka kenan tana neman nashwan dayazo ya warkan da ita..
Gashi kwana biyun Su abhi sun kirashi har sun gaji baiya dagawa kuma bai taba bude sakon su ya karanta ba,time dinshi na daga maman shi sai hidimar shirye shiryen lauching dinsa dayasa agaba shida mr mahdi dan ko sau daya rubibin mutuwar nail da akayi bai darashi ba.
Ahaka har maganan ciwon banafsha ya zama babban labari anata magana akan cutar hanklin yan ss ya tashi sosai jama'ar su sunata jimami...

Shikuwa boss khalepa shige da ficen sa kawai yakeyi yana bibiyar duk wani motsinsu yanata shirya ta inda zaifi shigarsu ya musu lahani mai gigitarwa, rananr da abun ya cika sati biu kwasam sai aka
Sanar a tv cewa an same yaduwar cutar ajikin mutane goma da suka ziyarci asibitin doc kbr a satin kafin yammacin ranar ya rifa har karin jimillan mutane yakai 100 kuma harda kananan yara
Chapter 165 · 0% Book details