← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 176

Sashe 162

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan shiru tayi tana kallon sa,sannan ta maida abinci ta debo wani shima yaki amsa,haka ta dingayi har sanda ransa ya gama harxuka,"me kake sha'awar ci to?jin ta masa tambayar kamar bata sanda fushin dayake yi ba ya dada jin kamar ana yankashi
hawayen sa ne suka gangaro da azaban yanayim fushi ya yaface su akan fuskan sa wafiyya ta mike tsaye kamar bata san yanayi ba da alama zata je kawo masa wani abinci,harta sanda takai bakin kofa taji sautin muryansa,"ni fa bazanci..ko kin kawo ma na koshi..
Dawowa tayi cikin sauri ganin yadda yayi maganan yanajin dar dar ga uban hawayen da suka sake yanko masa ta zauna daf dashi tana kallon sa cikin sanyin yanayi tace kahran maman shi..Meyasa bazaka ci abinci ba?yana share hawayen kamar dan Yaro yace "nakoshi ne"
Murmushi tayi Ta kyabe bakinta kamar bata jin irin ciwon dayake ji aransa ta share rikicin shin tayi kamar bata san me yakeyi ba ta fara lallabarshi"kwanan ka biyu baka ci wani abu mai nauyi ba fa u have to eat kaji?,i have alot to tell u my son,dint miss mummy...i really missed u alot my little py,uve grown sooo turbakalla like the king u are,Allah ya dada kare munkai king of the north,farin cikin rayuwar maman shi,our very own kahraman Ohh Allah make my husband see our dream coming true
Nashwan ya rufe fuskarshi da tafin hannunshi ya fashe mata da kuka dan ji yay kamar tana zaginshi,tana kai hannu jikinshi ya fara mata da masifa,yana cewa bazaici abincin ba..
Still Ta share shi saima ta bige da tambayar shi ko fada sukayi da zaira taga itama ta fita tana kuka taki ta kulata,ai kuwa kamar ta tsokalo shi,yace eh din fada sukayi kuma bazai taba yafe musu ba tunda suka hadakai suka zalunce shi ita da mahdi..har da tuhumarta akan sabbin kayan daya gani ta siya masa a wardrob dinta kenan tuntini tasan inda yake ta barshi yana shan wahala

wafiyya ta zauna shiru tanajin complain dinsa da mitarsa har ya gama bambamin sa yay shiru dankansa dan bata ko tankashi batayi ba
Saidai Sosai idanunta sukayi ja

jin yadda yake ta cewa yasha wahala da rayuwar shi adalilin rashinta na karya mata karfin gwiwarta Sai dai ita mace ce mai fasaha,da sanyin nitsuwa dan haka ta kau da komi akan fuskarta da yanayin ta ta umarce shi dan dole da ya dau abincin ya faraci tana kallon sa,anan ma kadan yaci ya bar mata saura saida ta amsa ta rinka bashi dan dole abaki har saida cikinshi ya cika tam ta kyaleshi

kwanciya yay akan gadon ya rinka hawayen kin kula maganan sa datayi Tun daga nan zaka gane cewa sosai yake jin shakka da tsoron maman shi dan duk fushin shin nan daga ta hada rai ta umarce dayay abu sai yaga yayi batare da musu ba

Tattara kayan abincin tayi ta kaisu kitchen within 30 min ta dawo dakin tare da mr mahdi da zaira agefenta,a kwance yake har yanxu jin shigowar su ya sashi mike kafarsa daya nannade batare daya juyo ba..

Akan kujera mr mahdi ya sami waje ya zauna zaira ta zauna agefen ta na dama sai wafiyyar datake zaune daf da shi,hannu ta mika zata taba shi ya ja jikinshi,sai ta kirashi da asalin sunan tace nashwan tashi ka zauna ina son magana dakai,da kyar ya tashi ya zauna sanda ya zauna din ya bude lumsashen idanun sa ya sunkuyar da kansa kasa,..

Ita da bakinta ta fara bashi labarin komi,she dint hide anything frm him ta gaya masa yadda mayor Aseem ya tarwatsa rayuwar su da wahalda ita da maman zaira da yayi a prison suka rayu cikin baqar talauci da wahala
Har suka kubuto waje da zaira ta girma ahannun ta

Ta gaya masa tun bayan rabasu da akayi sau daya ta sake ganinshi arayuwarta kuma shine ranan da suka zo kauye yin abinda ya damesu..

,..nashwan da tuntuni ya mike tsaye baisani ba he was more thab shocked dayaji cewa abunda mayor ya aikata arayuwar shi kenan domin ya rikesa akan dukiya.

Mr mahdi ya kara masa da bayanai danma kar yace zai dau fansa,ya tabbatar masa da cewa bazai iya da mayor cikin sauki ba cos d power nd d bond dake tsakanin iyayensu is sumhow super natural..

Wafiyya ta dafa kafadunshi ta hada harda rokonshi akan karyasa abun aransa yayi duba da ita datayi zaman shekaru batare da shi ba ya kuma duba matar sa zaira da aka rabata da kowa nata a duniya aka kuma kwace mata dukiyarta.
Jin ance dukiyar zaira ne hannun boss khalepa tuntini abun sai ya dada harxuka shi ya fusata shi,...

Bayan sunyi wannan maganan kowa ya san komi amma nashwan bai dawo daidai ba sai bayan kwana biyu daya sami nitsuwa ajikin matarsa da suka kebe jiya dadaddare..

Nashwan Babu kalar haqurin da bai bata ba,yana rokon ta gafara data yafe mashi duk wani digon wahalar daya bata,wanda in aka duba duk ma shi tayi..

Kwatanta babban matsayin daya dorata akai acan cikin ranshi bazai fasaltu ba danji ma yake kamar itace rayuwarshin.

Yau da safe bayan cin abinci wafiyya take gaya masa yadda zasuyi su dau fansa akan Mayor aseem dan haka ta saka shi akan yayi kokari yay duplicating paper din bmf ta fanninshi yakai ma'adanan su na can saiya kwaso original din ya kawo mata su nan agida
Nashwan yace sam shi bazai bar gefenta ba sai dai ace mr mahdi yayi
Washe gari mr mahdi ya fara processing hakan

Suna wanzar da rayuwar su mai shegen dadi da tsafta har yau kwanan su goma sha biyu a gidan batare dama sun kirga ba,wani irin so da gata take basu zaira kam tuni ta saba dan dama ita kam haka aka raineta cikin kulawar wafiya

Nashwan ne sabon shiga kuma sosai ya lalata kansa da lalaci ya gama sangartan da kansa
Ko kwanciya zaiyi saidai kaganshi jikin maman shi,wafiya tana xama zasu mamayeta hira kala kala tasha,haka zataji na wannan tazo taji na wannan wani bin tayi dariya sosai wani bin subata tausayi, har sanda nashwan ya fara bata labarin yadda yayi ta wahalda zaira,zaira ta dena xuwa wajen dan bata so ya fada ba amma shikam sanda ya fada kuma ya sha fada da wa'axi kam ba laifi

Suna respecting dinta sosai musamman ma shi dayaga ta fishi fasaha akan komi duk da kasancewar sa namiji bai isa ya hada zurfin tunanin sa da hikimar sa dana maman shi ba,yaga kuma tana da ilimi sosai ko yadda take handling files da aikin likitancinta ya sha bambam da nashi,ga wannan xurfin ciki da sanyin halin nata dayake cusa musu jin shakkarta aransu..
Sosai da sosai yake kaunar ta komi nata na mugun birgeshi.
Musammam yadda take kulawa dashi komi takan masa dakanta kamar dan yaro,da safe in bai zaga ya kwana da matarsa ba haka zata zo ta tashe shi so lovely daga barcinshi mai dadi,nashwan haka zaiyi wanka da ruwan data hada mashin,in ya fito zai ganta tana jiranshi da towel danta gogeshi ta shafa mai mai ta kuma zaba mai kayan sawa in taga yana saibi haka zata saka mashi,all this while baisan abu daya ake musu da zaira ba,shi yadauka duk biyanshi ake lokutan da ba'ayi masa yana karami ba,zaira in taga yana mata rigima akan hakan dariya ma yake bata..
Dan nashwan shagwabbe ne nakin kari irin shagwabn nan ma na naci da fitina.

Wani bin wafiya zata gaji da kwakumarsa ta korashi yaje ya kwanta dakin matar sa amma in baiyi niyya ba haka zai fita yaje ya dawo saidai ta farka washe gari taga kanshi mashak akan kirjinta ko ruwan cikinta ya kananneda ta a jikinshi yana minshari...

Wani bin saidai tayi murmushi aranta tace thank god ma saida ta yayeshi ya girma kafin aka rabasu, badan haka ba halanma har nonon da baisha ba zai ce abiyashi.

Haka rayuwarsu ta kasance cikin tsananin kulawa nishadi da cin dadin zamantakewar su
Kullum wafiyya saita tattauna da mr mahdi akan rayuwar zaira,tana so ta san wani future ya dace su daurata akai dan tace bazata lamunce a azabtr da ita akan lamarin auren ta ba.

Mr mahdi ya gane sarai akan maganan komawar su cikin SSM take magana danya san dole ne in suka koma dole ne zasu boye matsayin su na maaurata dan kar agano su da wuri

Kamar da wasa saiga Wafiyya ta daga hanklinta tana gwada ma mr mahdi da nashwan cewa lallai suyi tunani akan yadda zasu karar da wasar nan da wuri dan kar ashiga haqqin rayuwar yarta,gashi wafiyya in tana bada comand cikin magana yi takeyi kamar bata san kowa ba,irin ba sani ba sabon nan.

Hakan datakeyi musu ya tursasa nashwan yin tunanin yadda zasu zauna da matanshin acikin gidan in sun koma,tare da gaya ma mr mahdi cewa a gaya ma mas'ud yazo yau ya same shi anan gidan domin ya karbi kudade ayi doubling ma'aikata dan ayi gaggawar karasa gama gina north nan da sati guda kafin su koma south song dan wafiya ta umarce su da acan zasu zauna ba acan agidan sa ba.

Washe gari da sassafe mr mahdi ya taho da mas'ud gidan duk yadda yaki jinin wafiyya ta nuna mashi kanta saida yaci tura dan ce musu tayi ai mas'ud dan arxiki ne ya kuma mata halaccin da bazata taba mancewa dashi ba.

Mas'ud kam ma da kyar ya gane ta saida xaira ta fito ya dago kan maganan
,amma basu gaya masa direct cewa itace mrs wamako ba, sabida yadda nshwan kwata kwata baya sake fuska da mutane

Su biyunsu sukayi maganan su nashwan ya bashi dukan abunda yake bukata domin gaggauta aikin yaukam har anyi musabaha da shi jin mama ta yaba da halinshi,...

Bayan mas'ud ya bar gidan da kwana
Takwas ya gama komai saidai baifara xuwa wajen nashwan ba ya fara xuwa wajen mr mahdi danyi wata muhimmiyar magana..
Chapter 162 · 0% Book details