← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 176

Sashe 146

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A miskile Ya musu kallo daddaya yaga kyaunsun ma ya wuce gaban a kirasu da kyau Aransa yace
"God forbid yaci amanar matarshi
Da yan matan aljanu...tambaya goma da ashirin sun
Masa amma baice dasu uffan ba,sho jira ma yake yaga sun bace don ya bazama jeji neman matarsa,shugabn su farida tace toh mukaishi gida wajen mama,aira ta mike tsaye tace ni zan kaishi,faridan tace a'a ba aikin ki bane,shikenan kuma musun hakan yaso ya kaure tsakanin su da zafi zafi

Wajen ne ya dada gaurayewa da hayaniya da alama aira tana so tanuna kamar har ta kamu da sonshi ne nashwan bai hankara ba yaji an turasa cikin ruwan da uban qarfi,fatima ce da dayan yar team dinsu na marasa goyon bayan halayen maza,Fatimar tana masa magana tace ya koma inda ya fito acewarta dama ta fada shi namij ba alheri ba,gashi daga xuwansa har ya wargaza musu zaman lpyarsu sai dayan wacce ba musulmanba tafara kiran sprit din land dinsu akan ya bacardashi kawai a katse rigimar,ganin wajen ya kacame da surutayya mai zafi yasa zaira
Ta dawo inda suke da dan saurin ta
Wani irin wainuwa ruwan yakeyi sabida incantation din da akeyi,kamar ruwan zai yagashi haka ya dinga juyi da hakarkarinsa sai wullashi cikin ruwan yake nemanyi.

dayake basu dena hatsayaniyar ba yasa ruwan bai komar dashi akan lokaci ba,Kowanni taku daya zaira tayi xuwa gaban ruwan sai taji dirin saukan bugun zciyrya,da yadda sautin kirjinta da numfashin ta yake karuwa har kmar zai fito sarari

Shugaba farida na kokarin raba fada tsakanin su fatima da aira,zaira ta iso daf bakin ruwan,dan kyallarawa tayi aikuwa ta gano fuskar mijin ta yanata kokowa da ruwan rafin datake juyi dashi kamar zata cinyeshi

Wani dif wajen ya dauke kamar an danna musu pause jin Wani axaban kwalalar da zaira tayi tana ihu,da uban gudu ta taho gaban ruwan kamar zata fada ciki faridan ta rike ta, tajawota baya a birkice"wani matsanancin kukan da bata san daga ina yafito bane ya kufce mata,tana mika mai tsiraran hannayen ta.."sir nashwan?...duk da jigatar da yayi jin muryanta sanda yasa komin sa suka yanke masa cak ya tsaya yana kallonta
Ta kara fashewa da kuka tana mika masa hannu a hnkli ya mika mata nashi hannun,nan dukan su yan matan nan suka tsaya akansu sunata kallon ikon Allah,ruwan yana tsagaita juyinsa farida ta saketa duk tsorontan nan ta basar ta shiga ruwan ta gefe gefe ta bashi hannuntan da kyau ya kama ta taho dashi har bakin ruwan da iya kkkrinta ta fiddashi
,malala yay akasa da jikinta yanajin ko inan sa na masa balain ciwo,a hnkli ya juyo yakalle fuskarta yanajin tsananin azaban farincikin samuntan can cikin disashiyar numfashinsa yace wife,zairah..are u ok baby?im sorry..dan Allah kiyi hakri kiyafemin...zair...
Bai karasa ba Saiya dauke magana
..hawayen ta take ta sharewa,dan daga yanayinshi kawai ta karance cewa yasha baqar azabar nemanta.

Tayi shiru tanajin wahalalliyar numfashinsa har ya dauke kwata kwta,kuka ta farayi yan matan suka taru suna lallashinta harta gaya masu faridan cewa ai mijin ta ne
Daga nan shikenan fada tsakanin su ya wanye tsakaninsu a tare suka taimaka mata sukaje dashi gida,tun a hanya fatima ta gama lura da yadda zaira take kafafa da aira da tun farko ta nuna yay mata hartayi fada akanshi,koda suka isa gidan ma itace kadai tanace akan cewa zata zauna dashi a wajenta har saiya farfad,Zaira tun datayi zaman ganin sa ahaka acikin yanayin wahala da jigata hanklin yay mummunnan tashi.

A Daren ranar ma da kyar ta zauna cikinsu aka musu wanka,duk tambaya da akamata akansa ta amsa, amma gaba daya hanklinta baya jikinta sam Takasa sake ranta ta basu qamsashen bayani,gangan jikin ta da hanklin ta kaf nagare shi,ana gama musu komi bata wani jiraba ta wuce dakin inda aka kwantar dashi ta zauna agefenshi tana lura dashi,haka tayi baccin ranan bata iya samun nitsuwa ba ko tasa komai acikinta ba

Yanayin Nashwan ya matukar bata tausayi,cikin dare tayi ta hawayen nadaman abunda tayi masa amma awanni fannin zuciyarta batajin hakan datayi laifi ne,akan me zai karbe mata pride dinta?

Sassafe matar tazo ta buga musu kofa nashwn tsaban gajiya har ynzu bai farka ba zaira ce ta fito tana mtsika idanun ta bude kofar,matar ta gani da bahon ruwan zafi agabanta yanata turiri,a ladabce ta shiga gaisheta bayan tagama amsawa tace budurwa,mijinki yazo zaku tfi kenan yau ko?zaira tayi shiru,sai matar tayi murmushi tace to ga ruwan wankan sa,zakuyi wankan yanzu kafin sauran su farka a barci,in kin gama kixo ki sameni zaira ta rusuna kasa kamar yadda ta saba ganin yan matan nayi tace godiya nake mama
Matar tana barin wajen ta dawo dakin da ruwan cos she perfectly got her hala bata so azo musu wankan safe ne wani namiji yazo yana wullawa har yaga tsaraicin su
,ita kanta Tasan bazata so hakan ba,dan haka ta kai ruwan daki ta rabashi biu daya yafi daya yawa ta surka dayan dadai wanka tukun ta nemi tsumman gashi mai kyau sannan ta dawo da zimman ta tashe shi Hakan sai baiyu ba , he is too weak ko zama baiya iyayi,dan haka ta rusuna agabansa ta tallafoshi jikinta

taimaka mai tayi ya xauna idanunshi a lumshe kamar yana bacci sannan ta kwashe duka shimfidar da kayan dake tsakiyar dakin ta bar zallan kasa dake kasar dakin
,button din rigarshi ta balle ta cire masa harda wandonshi,ya rage dagashi sai boxers bakaramin kallonta da wutsiyar idanunshi yakeyi ba itakuwa bata ko kallon sa kanta ma can kasa yake batasan meyake cikiba,Babu jira ta gyara zaman sa akan dan kujeran data aje a tsakiya ta debo ruwan dumin da irin sabulur su ta fara wanke mishi fatar jikin shi,cizon sauro da kwari sune radada, harda ta fuskan shi da aka wanke su tas sai suka dada nunawa
,magana takeyi a xuciyan ta ita kadai wai shin Har yaushe ne basa tare daya babbata jikinshi haka?tagani fa wai har ya rame ya dawo kalar tausayi?,hmm,can ta dau summan tana tsomawa aruwan zafi tana daddana masa kafafun sa,da bayansa da tsaban yaci yawo suka kumbura suka haura

,,bayan tagama wankan ta tsaftace shi tsaf batako yi yunkurin masa tsarki ko alwala ba ta mike sadaf sadaf ta wuce dakin basarakiyar inda ta hadota da sutura da abinci da dan kyallen da zata gogeshi,tana bude kofar ta ganshi still akan kujeran ya dukunkune kansa idanuwanshi a lumshe yana sauke ajiyan zuciya,ajiye abincin tayi ta taho da kayan sai ta warware ta daura ma kugunshi zaninta sannan ta yafece boxers dinsa tayi dashi yay tsarki nan ma yaki sam ya bude idanunshi daga karshe itace mai zuba masa ruwan tsakin yanayi agaban ta har ya samu yay alwala,
kayan da aka kawo mai kamar jallabiyace kuwa
Dan haka Ya dau tsawon lokaci yana biyan sallolinsa.

zaira ta gama tsaftace wajen tayi ta nemi waje ta zauna tana ta satar kallonshi tsawon bai idar ba

Bayan ya idar din abincin kawai ta tura masa gaban sa,tace yaci sannan tasa kai tayi waje ta kyaleshi Jikinshi ne ya bashi cewa har yanxu bata dena fushin nan nata dashi ba,haka yaki cin abincin har sanda tadawo daga nata wankan tazo same sa a haka haushi taji aranta dataga baicin ba amma bata ko kulasa ba,yan matan ne rututu abayanta da alama suma sunxo duba sa ne,dukan su sunsha kyau da charm dinsu na saurin sabawa da mutane,sanda ya kalle zaira din sannan ya kalle su aranshi yanata mamakin ta ina ta sansu har yaga alaman kamar har sun saba haka?,kowacce ta zauna kusa dashi daf sunai masa murmushi,baqin yololon gashin su da jikinsu daya gama jin steam sai kyalli yakeyi yana dauke mai ido shikansa he cudnt resist sai kallon su yake tayi abunshi yana dan murmushin shima zaira dataga hakan sai ta maida kanta kasa takima ta dago kanta bare ta kallesu,can taga suna kokrin tursasa akan yaci abincin Su taran nan kowa sadda ta deba a hannun ta wai xata bashi a baki,zaira tafarajin kamar zuciyarta zata tarwatse wajen dan kishi,sosai takeda wani irin balain kishi,wani haushin kanta tafaraji in ta ja abun yay mata yawa sai tace so what nida Bama yafe mashi zanyi ba?daga bisani kuma in taga ya budi baki zai amsa abincin zaitaji kamar zuciyar ta ake yankawa
Bai jima da fara karban ba kuwa ya kware sabida yanayin kyaun halittar fuskarsun ya wuce inda namji zai iya dauke kansa cikin sauki,yana fara tari zaira ta taho da haushi ta kwaceshi a hannun su,sai gani kawai sukayi ta bata ranta cikin sanyin yanayi tace musu su fita waje aiya koshi ne,yan matan nan har suka bar wajen suna balain mamakin ta While ita kam ma bata san tayi musu wani abu ba,in abun ya mata yawa a zuciyarta kishin tunkudarta yakeyi yasata tayi fushi da kowa, Shima hanashi abincin tayi ta kawar gefe ta hade kanta da giwa tana sauke hucin ta cikin fushi.
Chapter 146 · 0% Book details