← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 176

Sashe 143

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace
Sai Kazauna da baqin halinka..bada ni ba..Tana shirin fixge hannun ta ya wani jawota da karfi ta fada kan kirjinshi
Kokowa suka shigayi har sanda yay nasarar hade bakinsu waje guda
Ya matseta jikinshi ya dade yana kissing dinta ahaka

Daga ita har shi saida gabobin jikinsu ya rusuna yay sanyi,wani muguwar rawa jikin sun yakeyi,ji yayi kamar kafafunsa sun bazata iya daukar su ba,har kasa ya rusuna da ita bakinsu yana jone,zaira tana kwace bakin ta anashi ta dubi setin fuskar sa sanda ta takarkare sannan ta wanka masa wata makuhuwar mari.....
[12/16, 2:49 AM] Pretty KITTEN: *72*

Bai damu da zafin marin ba ya dafe wajen ahnkli Yace wife u slapped me?tsaye ta mike tana kallon sa,dis time ba acikin yanayin ta na rikici ba da gefen idanunta ta kalle bayan kofar taga key dinshi na jiki yana reto atake sai ta dauke kanta cikin basarwa tana kallon shi a miskilance ta furta"..im leaving u...tunkan ya mike tsaye ta daddage cikin wata kakkarfan juyi ta fincike keys din ta fita dasu a hannun ta da mugun gudu ta ja kofar ta waje ta kulle shi ta ciki,bata gama zare key din ba Nashwan ya fara bubbuga kofar da iya firgicinsa da tsoron sa Zaira...zairah...wife pls dont do these
Dn Allah karki rabu da ni,dan Allah karki tafi wani waje ki barni,zaira..zairah
Sai bam bam bam
Ya buga kofar da iya karfinshi kamar zai balla amma ina Jefar da key din ma tayi akasa,...jin yadda ko ina ajikinta yadau radadin zafi da zugi ababu yadda ta iya tayi zaman ta a falon akan kujera tanakan jin maganganun sa da rokon sa,Da can abun baima dameta ba baiya ma shigarta har can can,shirun datayi masa na tsawon mintina ashirin yasa yakejin kamar har ta wuce ne bata wajen,
Kuka ya fara mata tsakanin shi da Allah yana rokon ta karta tafi ta barshi
..shi da koma ta xauna karta kulasa har kwana biyun axo a dauke su, tun ayadda ya fara buga kofar da zafi zafin firgici yana kiran sunan ta cikin matsananicin damuwa da tashin hankli zaira ta fashe da kukan tausayinshi Saima yanxu ta gane ashema dauriya yakeyi tun tuni agaban ta bai rikice har haka ba

Bugun da yake ma kofar har yaso ya tsoratata kamar zai tsaga kansa haka yake kiran sunan ta yana rokonta.
Tanajin kukanshin sai tarinka jin hanklin ta na matukar tashi dan bata tabajin abu mai tada hankli kamar sautin kukan shin ba,ita kanta tasha mamakin yadda sontan yamasa mummunan kamu har haka,his sobs is filled with love nd emotion and sicknesss bata san tunaninshi abu daya yake rawaito masa a lokacin ba, ya za'ayi maman shi ta rabu dashi yana kiranta yana kuka bata dawo ba, sannan yauma matar shi itama ta rabushi?..,iya firgicin daya ki nunawa agaban ta shiyayai ta nuna makan sa a dakin yana buga kofar da tsananin axaban rashin ta.
Sosai ta durkusa kasa awajen tana kallon kofar tanata hawaye kwakwalnta yana tunxira ta data bude kofar amma abunda yake cikin zuciyarta yafi danne ta,jin kamar bazata taba gane abunda ya dace tayi ba yasa ta mike tsaye ta nufi backyad din ta deba kayan auren nata da jika jikan sun ta maidasu jikin ta ya mata das ta rufe kanta da mayafi.

Kin dagowa tayi bare ta kalle kofar komawa cikin gidan,gaba ta jefa kafufuwan ta ta baya ta fara babbanke ciyayi.
Jim kadan wani uban tsantsi ya kwashe ta zuuuuut yyi mummunan wullla ta can cikin wani katoton ruwa...

Wasu yan mata ne ata daya bangaren suna tattara kayansu a yar local woven basket dinsu da alaman zasu kara da gaba sai fanjam suka ji karar fadowar abu acikin aruwan,dakatawa sukayi,sanda suka duba da kyau sukaga lallai mutum ne ya fada aruwan kafin suka aje basket dinsu cikin sauri suka shiga cikin ruwa suka kinkimo ta sukayo waje da ita..

Zaira kam tuni ta sume dan dama data fadin bakaramin tsorata tayi ba tangare gare sukayi da ita su kusan su hudu suka wuce da ita gidan su.

Fannin nashwan kuwa babu irin firgicin da baiyi ba
Dan tsaban tunanin dayakeyi na kala kalan abun damuwa saida ya fara tada ciwon kwakwalrshi
Ya fara cewa brain din hala haka rayuwar sa zata kare,Life has neva nd will neva be fair to him,yace makansa he is soo unlucky nd meant to suffer out of depression nd loneliness,He cant take it in wani abu mummuna yaje yasame matar shi,ga tsoron rasata har abada kamar yadda yaketa tsammanin ganin maman sa da har yau bata dawoba, tsaban kishi har gani yake duk wanda ya ganta a jeji gallant ai dolene yaji sha'aawarta
Sosai ya zauna kasa yanata jimami duk dabarar sa yayi amma ba hanyar da xai iya kufcewa ga ramin windown dan karami ne, yana zaune anan har aka kira magrin baiyi xhr
Da asr ba,da kyar ya aikata hakan,cikin ikon Allah kuwa yana idarwa ya murda kofat yaga har ta budu,ledan abincin su yagani daf da bakin door din kamar anbude ne da niyyar shigowa aga ko lpya sai kuma aka gansa yana sallah sai aka bari,haka ya tsallake abincin ya dau kayansa a backyard da jika jikan shima ya xura ajikinshi ya fantsama jeji saidai hannun riga sukayi
Shikam ta inda aka shigo dasu yake bi ita kuma baya tabi,hakan yasa bai wani ja sosai yana tafiyar ba ya fara haduwa da kurtayen sojoji,duk wanda ya tsare a hanya sai ya masa tambyar "hav u seen my wife? Dukan su
No answer,saima warning dinshi da aka dingayi akan ya koma inda ya fito yau akwai sabbin wayanda zasu bar jejin he was told dat in suka gansa ma yanayi musu yawo zasu harbe sa amma haka yay kunnen uwar shegu
Ya wuce gaba gaba yana kusawa jeji yana neman matar sa,agalabaice yake tafiyarsa,tsaban ya cusa damuwa aransa ya riga ya cusa aransa cewa baima jin tsoron shigewa ko ina.

Sosai yay nisa da gidansun,wani dan karamin hanya yagani ya mike nanma tafiyar kawai yaga yanatayi gaba jeji baya jeji,har dare ya tsaga bai samu madakata ba wani kakkarfan jiri ne yaso ya yardashi saiya hkra ya neme waje agindin wata itace ya zauna ya dafe kanshin yanajin wata uban fargaba na mamayeshi Shiru yyi na wasu yan mintina yana kan tunanin cikinshi dataji azabar baqar yunwa tana murdawa,tunowa yayi ashe yauma kwata kwata baici komi ba sai 2 cups of coffen dayasha tun da safe,yunwar ma haushin ta take basa ayanxu,shi damuwar sa baifi yasan yadda zai juya akalar tafiyarsa ba dan har yanxu bai cire ran zai ga matar sa adaren nan ba,hakan yay ta sake sake aranshi,jin wajen ya dada nitswa dabbobi da tsuntsaye sun fara fitowa nashwan yaji tsoro ya kasa barin wajen,karshen ta anan ya lafe yana jiran wani qarfin gwiwar dazata taimaka masa ya kusa cikin jeji,toh
Zaman da bai iyayi ba kenan,to top it duk jikinshi radadi yake masa na ciwon kwari da mugayen sauro bai ko iya runtsawa ba ya mike tsaye yana korar su kozai same salama kan yace wani abu yaga wai har safiya tayi hanklinsa ne ya tashi sanin cewa fa ko sallan ishai na jiya baiyi ba kuma yasan baiga wani mafakan ruwa ba daya taho,ya kalle kasa yaga duk ciyawine babu ma kasan da zatai masa taimama
,daga kansa sama yay ya rinka lura da movement din tsuntsaye can ya shiga bin direction dinsu.

Fannan zaira kuwa farkawan ta na fari da suratayyan mata tasoma cin karo ta shiga bude idanunta a hnkli ta soma ganin kanta kamar awani waje,tana karasa bude idanun ta taganta acikin wani daki,tsayawa tayi tana kare ma wajen kallo cikin gigin farfadowa taga kamar ko ina
AWajen a kimtse yake.

"Nya, mama...
mama...sai ma yanxu zaira ta lura da budurwa dake tsaye akanta wacce tayi waje da gudu tana kwalalar farfaduwon ta mama budurwan ki ta farka ta gatan can bude idanun ta
Within seconds zaira taga wasu dalla dallan kyawawan yan mata wanda bazasu wuce 18 19 ba, su kusan su tara suka shigo dakin kuma duk atare suka zuba mata idanu suna kallon ta.

Zaira kusan rikicewa tayi, She have to pretend dat she is not yet back into her right senses dan tunda aka halicce ta bata taba ganin dogaye kuma kyawawan yan mata masu curvy slim shape da zololon baqin gashi kamar na sadaka yalla ba sai anan dakin,gashin ta cigaba da kalla dan dukansu sunci uban ado ne da dogayen abaya amma basu daura dankwali akansu ba,wani malala gashin yake ajikinsu gashi da balain sheqi ga uban tsayi kamar banasu ba
,lullumshe idanun ta ta shigayi tana jn yadda tsananin tsoron su yake shigarta,kaf ta kalle fuskokin su amma bataga mummuna ba kuma bataga wacce tafi wata kyau ba,dats when she knw is official tasan hala tafado ne cikin yayan aljanu,Kuka ta fashe dashi acan cikin axuciyar ta tana jin tsananin dana sanin rabuwa da mijin ta..

Yan matan basu ce mata komi asif sun jeru mata ne danta kalle tsaban kyaun su da annurin dake haske ayanayinsu tun daga xuciyarsu har kan kyakwan fuskansu,zaira ta lumshe idanun ta kenan tana neman kawo ayatul qursiyu sai caraf wata mahaukaciyar mata ta shigo,a firgit ta bude lumshahen idanuntan tana jin yadda yan matan nan suka hade bakinsu waje guda sunayi ma wannan matar kirari da wani yaren da bata tabajin irinsa ba.
Nan da nan zaira taga matar ta sallame su kaf sunyi waje

Waje ta nema daf da ita ta zauna zaira tayi maza taja jikin tayi nesa da ita kadan jin yadda takasa samun nitsuwa ga tsananin tsoro da bugun da zuciyarta yake mata,matan tayi mata yare tayi mata yare,can taji shiru zaira bata ce uffan ba, sai can tayi shiru tace Sannu ko yan mata daga ina kike?zaira ta bude baki kamar abun kirki zata amsa maganan wani matsanancin kukan tsoro ne ya riga maganan fitowa..
Chapter 143 · 0% Book details