← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 176

Sashe 105

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannun ta ya kamo suka doshi hanyar sink ya kunna mata kan famfu ruwa ua fara tsiyaya ya tare atafin hannun sa ya shiga zuba mata tana wanke fuskar ta,sanda ta wanke hawayen ta tas ta dago,taganshi yana kulle tap din,wani asirtacen kallo ta mishi na scnd guda sannan ta dauke kanta tun kan ma ya dago yana gogge hannunshi daya jike da towel can ya mata nuni da saman kitchen island yace mata sit over there,zaira ta wuce gaba tana tfiyarta a hnkli,harta dale kan teburin ta zauna,jim kadan noor ya karaso dauke da kofina biyu na ruwan sanyi daya ya dauka ya fara bata sannan ya dau dayan shima yana me dalewa gefe kusa da ita,2 sip tayi ta cire abkin ta sabida yadda tagan sa so quiet rike da ruwan a hannun sa kuma baisha ba,he was nor lookin at her,he was looking at the wall kamar jikinshi yay sanyi sosai

Cikin sanyin shangwaba Ta makalle wuya da sirirn murya tace mutumin Lpya kuwa?murmushi yyi atake sannan ya zuki ruwan ya mata zuka daya yana maida ajiyan numfashi yace
"zairah,?tana lura dashi tace uhum Yace in rokeki wata alfarma mana..,tace uhm inajin ka nan ya juyo da fuskarshi yana kallon nata a tsanake,"yace
..rayuwa wani lokaci abubuwa suna faruwa masu ban mamaki,amma dukan abubuwan mamaki da suke duniya basu kai boyayyen halin mutum bada mamaki ba

Kowa da kika gani a duniya fuska uku gare shi,daya ya nuna ma mutanen duniya,daya ya nuna makanshi,daya kuwa baya taba nuna ma kowa sai Allahn shi.

Kinyi kokarin zama da abokina,dan ni na sanshi fiye da ke,
Zairah karshen hakri fa nasara ce,i really hope u will achieve that one day,ure a strong woman kinji?so cheers.. ya daga mata cup dinshi yana murmushi ta dago nata a sanyaye ta hada da nashi sannan suka shanye ruwan atare.

Sauka yayi yana duban agogon sa zanje in shirya yau zanje can gida'sai ya kalle kan gas din yace ohh "Our food?zaira ta sauko ta nufi wajen da sauri ta karasa kashe gas din.,"see u later ta dago tace ok,sai taga har ya isa bakin kofar ya fice abinshi Har tagama zuzzuba abincn a wamers bata dena tunanin kalaman daya gaya mata.

Sauke ajiyan tayi ta fito dauke da tray din dishes,with 2 plates 2 cups da fresh pineaple juice
Takai musu dinning,
Inda taci karo da dukan su cikin shiri
Kowannen su da kalar nasa kyaun dayayi

Nashwan ya saka deep blue suits mai kyau wacce ta amshe shi ta haska kalar fatarsa
hakama noor khalil
Ya saka wata hadaddiyar casual blue jean ne amma takamma masa cinya ta mugun bayyana dirin sa na hadadden namiji mai dogon kafa,sai rigar sa light colour mai kamar sweater irin mai hade da hularnan amma ita tana da laushi sosai,baisa hular rigar ba sai ya saka blue base ball cap mai shegen kyau,wata hadaddiyar lanvin boot ne a kafarsa.

Dukan su sunyi kyau matuka,zaira ta kuma gaishe su nashwan baiko kalleta ba har tagama ta barsu after 40 mint ta sake daukar hanyar dawowa kasa tahowa take tanajin yadda zucirta yake bugawa jin wajen ya dau wani shiru ga iska ta waje sai zanca yanayin sama yake da alamar ruwan sama zai iya saukowa a bazata...

Can tafara sauri sauri tana karajn tahowar karfin iska tun daga waje, kanta akasa take tafiyar dan hakan kusan dabiarta ne
Tana bude kofar falo kunen ta yaci karo da karar caccakar hannun sa da alaman yana da danne danne ne a system dinshi, wani sautin kuuu cikinta ya bada sanin cewa dashi da sa ita ne kawai a gidan

" Saukowa ta inda yake tayi batare datasan dalili ba before she realise that sai taga mutum a kime he look so unfriendly,sikini ta kama hanya kamar zata juya Kamar daga sama taji ance
"Zaliha"sanda ta amsa da naam kafin ta dawo ta rusuna kadan agaban sa agefe,bai kalleta ba idonsa fixed akan abunda yakeyi,"Finish evrythng u are doing nan da awa guda zamu fita bana son latti..tace ok sannan ta tashi ta fara haurawa sama tana tafiyarta cikin kwanciyar hankli da tattalin kanta kamar babban mace maiji da sanyin qasaita da mulki,yana danne dannen bt he cudnt resist the serenity of her calm nature,da gefen idanunshi yayi ta kallon ta harta kusa kurewa quietly ya jingina bayanshi akan three seater yanajin wani yanayin kasala kasala a dukan jikinshi,wani irin burge buryewan sa takeyi,shiyasa har yau yakasa yarda da ita,he cant trust her nd get betrayed for once in ya tabbata cewa wayannan calm naturen ba asalin hayarnta bane haka haukacewa zaiyi
,she is charming nd soothing yarinyar kyau take nasa bana wasa ba,he keep seeing his babies in her warm beautiful eyes

Ya dade bayanshi na jingine da chair cikin tunanin fuskar zaira da halayayyar ta,kuma dama yasan duk sanda ya fiye kuntata ma mutum,sannan mutumin yay hkri dashi bai tsane sa koya rama ba,sai yaji gaba daya yana matukar kishin abun da kaunar sa.

But small part of him yakan hanasa sam,yakance masa mata ba abun yarda bane duba da yadda ya gama karantar rayuwar su abhay da yadda yan mata suke daukar fuska biyu dan kawai su yaudare su sucika burkan sa na duniya akansu.

Hannnun shi duka biyu ya daga sama cikin yar karamar hamma,yana kuma mika,kofar data bin ya dada bi da kallo yana sauke double smirks sannan ya Kyabe bakinsa yy hmmm.,can ya jawo computer sa ya cigaba da abunda yakeyi,..

After 30 min zaira tana daki,taji kamar qarfin iska ya dadu,ajiye husnul muslim din dake hannun ta tayi da sauri ta sauko daga gadon ta ta nufi wajen window danta rurrufe kar iskan yayi mata yawa,dan ta fiye kashi Ac wani bin cross ventilation daga waje ma kawai yakan isheta

Ta kama tana shirin rufewa,ta dan leke waje taga wani bakin haddari ne ke tasowa daga kasa can,tayaya kenan zasu fice nan da minti goma ta furta cikin nazari,haka dai ta gama ta bar wajen ta taho ta gaban madubin ta shirya cikin neat maid uniform dinta,
Ta daura dankwalin ta,so simple amma ya mugun tsaya mata sabida dunkule suman ta kawai tayi ta daure su aciki ta cuccuda sosai suka mata dan daidai din acuci
Ta zura fararen sawun kafarta ta cikin yar takalmin rubber ta,within 10 minutes har ta fita waje tana tsaye tana jiran fitowar sa.
Within 3 minute da tsayuwarta kuwa saiga shi ya fito

Da Wani kallo take binshi ganin irin kasaitaciyar shigar suits ruwan kalar toka dayayi"

,kamfanin girgio armani ce ta kerasa ta musamman dan kyankwashe siffar hadaddun gayu masu jiki mai shape irin nasa,da alama iya sauya sutura yana daga cikin ababen da basayi ma nashwan wuya
Komin shi yayi kyau abun kallo,zaira tana lura da yadda ko maxan ma ke bibyarsa da kallo ta kyabe baki ta shiga motar data saba bi
.tabiyo bayan sa.

Almost 1 hr drive yakaisu wani waje mai babban filin da babu komi se motoci da body guards tsatsaye agaban motocin kowannen su rike da manyan bindigogi a hannun sa,sun tsaya kyam kamar ba uban haddari baqirin ne akansu ba,itakam ma tun a mota ta sadakar dan kuwa bakaramin iska da duhu bane yake barazanar gauraye wajen .

Nash ya umarce kowa daga cikin body gurds dinsa ya ya zauna a motar sa
Amma sai ya kira zaira yace ta bishi abaya,rurin hadarin ma kawai yagama ruda mata ciki bare ajega mugayen halittun dake gaban su da bakaken kaya da bindigogi.

Daga dan nasa taga an aje ma nashwan kujera,yana zama ta tsaya agefen shi tana wara idanu itama dan taga isashhen dayake cikin wancan motar da'ake karewa,..

Leke wuyarta keda wuya aka bude kofar motar,wani hadadden saurayi sanye da kayan larabawa an balbale kafadun shi da wata hadaddiyar black arabian alkyabba

Karshen takun qasaita da jiji dakai da tafiya cikin muguwar izza game da hatsabibiyar salon iya shan taba to an qarkare sa awajen gayen

Yana tsakiya zaratan maza goma ne a bayan sa tun kan ya karaso aka aje masa nasa kujeran da baifi taku goma sha biyar tsakanin sa da nashwan ba ya zauna a kasaitance
Dan shi dan sarki,dan sarkin jordan cikin wata gawartaccen masarauta masu tarin kayan yaqi amma basada tsaban arxiki na kudi,yana zama sanda yy ma nashwan kallon tofin Allah tsine dayaga kamar mace kawai ta rako sa,hakan ya na nuni da ya rainasu kuma yana ganiin daman sa,abunda ba'a taba kwatanta musu a duniyar su ba kenan sultan jalaludden dama yaji labarin nashwan tun kafin jiyan ma daya nemesa,ance masa wannan kon din bakamar dayan kon din bane,ance masa nashwan wamako yana da ji da kansa da taurin kai,dan haka yau ba zallan meeting din kawai ya fito ba,yaxo ne yaga waye ma nashwan wamakon nd his first blow was to see him witout body gurds sai mace?
,abun sosai ya tabashi Ayayin da nashwan ya natsu tsaf sai da ya karanta shi ya gane hakan yake rayawa aransa.

Wannan meeting din akan wani Deal ne mai karfi da nail yakai musu akan nashwan wamako da nufin a ruguza fannin plan din na 70% din north dayake shirin kwacewa shida uban sa a hannun nashwan din

Mayor aseem ne ya tabbatar ma mr mahdi hakan,bayan mahdi ya tabbatar shine ya tursasa zancen a kunnen nashwan dan yyi saurin daukar babban mataki

Wani meeting aka shigayi daga nesa tsakanin nashwan da sultan,Magana ce na Izza cikin izza,iko da tsananin taurin kai suna famar arangama da juna ba'asan na waye yafi wani ba,zaira ce yar aiken sa in abun ya kama na nuna paper ko signign,to da daga nan inda suke zaune zaira tayi jeka ka dawo tsakaninsu yfi sau ashirin iskar ruwa sai gilui gilui yakeyi da ita kamar zai dauketa sama,

har sanda sultan jalal ya qamsu da cewa ko agidan giya ma akwai babba sannan ta samu hutu,sultan bai taba ganin namiji mai tsananin ji dakan sa kamar nashwan ba,aransa kacokan ya hada shigen sa da shaidan ne wajen taurin kai,dan iya abunda ya fada awajen baya sauyuwa yakan nuna cewa shi baida kayan yaqin amma yanada kudin da zai sayi na kingdom dinsu ya kuma siya na wasu kingdom infact sai ya siye ubansa ma inyanaso .
Chapter 105 · 0% Book details