← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 176

Sashe 51

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Tayi shiruuuu
Kusan mintina uku bata ma motsa ba can tace ok zan kula da komai din amma bazan dameka ba..aranta tana cewa duk abunda na aikata kaika jawo
,,doguwar ajiyan numfashi taja ta kalle sa da wutsiyar ido tana tahowa kusa dashi daf cikin sanyin taku mai tafe da rashin jin dadi aranta, bata ma tsaya ba seda ta zauna kadan a gefen sa 'Nashwan ka bata ranka ko?
"Ok im sorry'.zata kwanta jikin sa ya wani janye ya kai kansa can sama
..kayi hakuri mana..toh
Anjima zamu fita tare?Kafa min alkwari

Ba har cikin ransa ba Yace Ok..amma sekin aikata abunda nace miki

Tace ok me kace min?.

Nuni yayi da kofa yace "OUT.."
Kamar zata fashe da kuka ta kalli kofar,can ta mike tsaye ..da har zatayi magana se kuma ta fasa tayi waje a hatsale,har saura kiris suci karo da bingel data mannnu da kofa tana bibiyar maganganun su behind close doors

Wani daka takai mata a baki da jikin ta..."Ke jaka kawai..wai me kikeye anan?magulmaciya,tuni bingel ta kama sose sose Madam ba gulmanki nakeyi ba

'tace kimin shiru ai Duk ke kika jawo yaki amincewa ke sam jakace wallhy baki da tunani...

.bingel tace madam minayi kuma?a masife ta juyo tana zare mata idanu kamar zata mare ta
"Waike da kikaga stain din tun farko ma meyasa baki kwashe table cloth din kinje ki wanke ba?cike da bude baki da korafi bingel tace Ahh madam bake kikace daga munxo in nemi wani abu na aibu na nuna maki ke zakiyi sauran ba?nifa na dauka daga tazo kin kawo korafin ki zakisa mr KON ya koreta ne..
hanadi tace hmmm mswww Wani dogon tsaki taja bayan ta gama kare mata kallo da harara mai zafi "to ai gashi yace dai kema kazamar ce sabida ke kika nuna min dattin amma bakije kin wanke ba sanda aka kira wata jaka irinki..Ko yanxun ma Laifi na ne da brain dinki baya ja?bingel tayi shiru ta dan sadda kai,to ohon miki... next time zaki koyi yin abu cikin hikima kodan kisamu shiga wajensa.

Ina shegiyr yarinyar?bingel ta sauke murya
Cikin sanyin jiki alaman bahaka taso ji ba tace tana can loundry"ok xo muje"zanje in duba kayan zance basu wanku ba saura in munje gabansa da wani aibun nata sai kije ki kwafsa..

Bingrl ta girgixa kai looking relieved
babu bata lokaci hanadi ta wuce gaba bingel din tana biyota abaya.

Dakin wankin babban dakine mai girma da yelwatan kayan enginan wanki,zairah ita daya ne aciki babu kowa,gefe da ita dry nd bleach treatments ne da sauran presing machines da spread board kuma komi a kintse yake kusan babu abunda zaka nema ka rasa na kulawa da kaya awajen kowani iri ne

Shiyasa Zairahn bata wani dau lokaci ba shap shap ta hada kumfata jika kayan, gashi hartagama wanke sutas da vinegar da bleach ya fito kar kar kamar ba ataba tabawa ba, zubawa tayi a engine din yana matsewwa tana tsaye har ta ciccire wasu agefe da niyyar zata bushar dasu ta gogesu atake,
Tana cikin haka taji an wani banko kofar wajen atake taji gaban ta ya amsa rass ta juyo atakaice suna hade idanu dasu hanadi taji gaba daya kirjn ta ya fara bugawa,batace musu uffan ba suma haka har ta karaso gaban ta inda machine din yake kamar me aikin duba lpyar wani abu,wani Tsaki taja tana rau rau da idanun ta fuskn nan a tamke gata da mugun son girma da kyankyani

"yadda take nesa nesa da yatsunta daga cikin machine din da alama tunda aka haifeta bata taba iya wanke ko panties dinta ba.

Bingel tana nan so she does evrything for her like a godess da chan ma har wanka setayi mata seda lady j ta buda wuta tanuna mata bata son haka kafin aka barshi,amma har yau aikin na nan ko period takeyi bata yin komi, bingel zat'a jira tazo ta sa mata pad ita dai hannunta baya komi sai kwaliyya da rubuce rubuce a office da cin abinci

..nan ma hannu ta wulla can a rigime tayi ma bingel din alamar taxo kusa dan tana dadadgo mata kayan sama taga ko sun wanku,bingel tana karasowa zairah ta ja gefe abunta.

Tana gani suka karace tsiyar dube duben su tana bambami as usual tana kushewa,can ta dago rai a bace tace dukansu su biyota da kayan tuni kagansu bisa layi abayan hanadi

fuskar hanadin a murtuke tana diri zairah na gaban su sum sum tana tafiya zaka dauka lefin sata ko zina ta aikata suka kamata

Kamar yar akuya haka hanadi ta shiga tunkudota keyarta har cikin falon nash inda yayi daidai da saukowar sa daga matakala yaje ya sauya shigarsa yasha custard colour plain kaftan da hularsa baka kirin me laushi yana tahowa cikin sauri yana dada gyara zaman gold links dinsa daya saje gaba daya da kalar agogon sa hade dana kalar fatar jikin sa,tsaban sunsa rai ga abunda ke gaban su hanadi bata ma tambaye sa ina Zaije ba.

Ganin yadda yayi mata kyau,More than eva ta somajin zuciyar ta yana harxuka sam sam yaki aminta datayi sharing dinsa ita dai lallai tana burin ta aje bingel a kusa dashi domin tasan ina yake xuwa,wajen waye kuma da waye kuma akan mene?

Kwana biyun ma wai dan Bingel tana bakin kokarin bibiyar mas'ud a siyance tana debo mata rahotanni kenan amma ji take har yanxu wayannan basu ishe ta ba.

She want to knw evrytthing
Aganin ta hakan ne zaisa ta iya mulkan sa nan gaba..
burinta ta zama akalar sa.
Ta kasance itace mai tacewa arayuwansa na nan gaba

Kuma bata so tayi sanya wajen karawa da abokiyar gaban ta wato nala khalepa.

Yana ganin su ya dauke kai ya taho kamar ma zai bangaje su ya wuce

Nash..hanadi ta kirasa..yayi banza
Nash wait kaga wani abu..Baby Ya kamata ka dauki mataki yanxu yanxun nan
kamar baiji ta ba ta sake kiran sunan sa da dan zakewa
"Nashwan... yana ta tafiyar sa shiru Saida ta memeta kiran sau uku sannan yaja ya tsaya daga dan nesa ya juyo ta inda zai kalle su da kyau duka su ukun

Tafi karfin rike kaya so Da sauri tayi nuni da hannun bingel.
Looking like a complete silly brat..
Tace nash honey
"..kagani fa bata ko iya wankin bama..comon table cloth..comon table cloth.. tayi stressing "comon din" irin aga dan shi din nan..wani jan numfashi tayi cike da zakuwa...

"Nash..i think ya kamata a sallame ta..

Hey girl pack ur bags the garbage truck is coming

Da sauri zairah ta kalle ta cikin rudewa tace me..mene?

A fuxge Hanadi ta juyo da harara kamar idanunta zai fado kasa tace
Ure fired!!!!..
An koreki aiki kar kuma na sake ganin kafarki anan
..kin...gaa..ne?
Zairah ta maida kanta kasa batace uffan ba,hanadi tawani ja tsaki ta karashe tsayuwarta cikin izza..Da sauri cikin rawan jiki zaira ta rusuna kai ahankli tace..
"Pls Im sorry ma!
Dan Allah kiyi hakuri zanje na sake wankewa namiki alkwari hakan bazai sake faruwa ba.

Wano Banza da ita hanadi tayi ta juya kan bingel tana wani magana cikin karfin hali"itama kuma yar taran aradu da ka tasan nashwan bai tanka musu ba,amma ta wani kasa kunne tanaji kamar wacce aka bata aikin already hanadi tace ma bingel
"Kinaji Daga ta wuce ke xaki na kula da nan sashen
Ki tsaya anan a sallameta saiki tafi

Tsaban murna tana washe baki Tace yes ma

Hanklin Zairah duk sai ya tashi,tanajin wani fargaba da bugun zuciya kamar dai bata so arabata da aikin,maman ta ne tafara fado mata atake ta shiga tunanin yadda zata katse mata sabuwar rayuwarta najin dadi yau inta koma gida tace an koreta a yar aikin dayake shirin rufa musu asiri ya kuma sauya musu rayuwa me tayi kenan?..Worst part over silly thing...dama ace babban laifi tayi mana..

Cire duk wani korafi da dalili tayi ta kaskantar da muryanta ta shiga bada hanadi hakuri

Dan Allah kar ki kore ni madam
Kiyi hakuri madam

Nashwan kam har ila yau binsu da kallo yakeyi baice uffan ba kuma bai motsa ba

"har ranshi bason hayaniya yake ba,amma haka yabi yana dan tantance asalin halayyar kowa daga cikinsu musamman daga furucin dayake fitowa abakin kowannn su kuma lamarin Ya bayyana masa cewa hanadi ta tsani wannan yarinyar mai masa aiki ne,but why?sai kuma xuciarsa tasa tace Well,why not? me abun so ajikin yarinyar... daga gani dama bata da kamun kai..shikan sa matsayin daya aje ta kenan he dosnt like her nd trust her at all,gash fuskarta yana confusing dinsa
tunanin shi inbanda watsatsiya marar kamun kai wani neman kudi ne zai kawo katuwar budurwa kamarta irin wannan aikin....yaja tsaki aransa haka kawai yaji haushin hakan aransa yace"look at her?sai ya harareta da wutsiyar ido sam baya tunanin Allah zai bashi lokacin batawa yana kallon surar jkinta da kamannin ta

But to be frank yasan yarinyar tana da kyau kuma babu abunda ta rasa na saurin daukar hanklin namiji"

...sede awajen sa bata da darajan da zaimata kallon haka dan bata da wani kwakran bambanci da karuwai masu bibiyar maza,just a lil bit dfrnce to meye maid din?..like a call girl...like a mistress shidai layi daya ya aje ma'anan su..can yayi tsaki aransa again yana kara jin ma ya tsaneta,he feel she is definatly not a good one..ji yayi ma ta dada bashi haushi sosai kamar ya biye ma hanadi ya korata kawai amma no Baya so ya taba bada hanadi wannan damar da kuma ikon,already ma abubuwan datake masan yanxu ya gama ishar sa,shikansa yasan lokacin ta ne kawai baiyi ba, da koda kudi akace taxo tana damun sa haka bazatayi ba...
Washi za a kawo ma shashanci da yaranta?.

Can dai ya dago kansa Sai ya kalle hanadin kamar ba agaban sa tagama zantukakkar ta ba
Yyi kifi kifi Yace "whatz happening here?

Tace yanxu dama baka gane me ake fada ba,ta sa bingel ta warware partly wet cloth din tana famar bayani ya dage kansa sama har ta karkare baiji komi ba a karshe dai Tace
"na koreta ne.
She is fired...

Ransa a hade Yace who fired her?
Chapter 51 · 0% Book details