← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 176

Sashe 4

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aganin ta tanayi ma nashwan Irin son da mijin ta yay mata ne koma rubinsa,..
hakeem ya sota sona bilhaqqi dan tunda ya same ta gidan marayu ya zame mata uwa uba miji gata sannan ya bata dukkan rayuwar sa,ko sau daya bai taba sata kuka ba bare kunci.
He spend his life loving nd worshiping her ita da dansu kwalli daya wanda ayau takeji kamar babbar butulci ta aikata ma mijintan data bari aka raba ta dashi.

His words were more than clear to her ayayin daya umarceta data kare musu dansu ta rayasa karta barsa duk rintsi duk wuya amma meyafaru ayanzu?wasu Sabbin hawayen da suka fi kowanne rauni kwayar idanun ta suka sake ayayin da duk gabobn jikin ta dana zuciyarta suke tuhumarta da laifin gazawa da cin amanan mijin ta mayor alhakeem wamako

Cikin wani daki mai dauke da gadon yan boarding schl up and down bunk guda biyu aka tura ta ciki, ko daga kai batayi ba ta sulale kasa kan gwiwarta ta fashe da wani marayar kuka mai gigita kwakwalwa.

Duk surutayya duk tsawa da tsiwan inmate dinta baisa ta dena kukan ba bare ta dago kanta dan kansu suka gaji sukayi shiru suka tsura mata idanu suna kallon ikon Allah,numfashi taja can ta yanki jiki ta fada kasa"
Suma tayi?

Wacce ta taba gefen wuyar ta ta furta..

Su uku ne a dakin wafiyyar ce na hudu,biyu ne akanta suna surutun,na ukun tana zaune shiru a saman gadonta atakure batace da su uffan ba har wafiyya ta farfado.

Tsintar kanta tayi akan motsatsan katifan ta wasu munanan mata guda biyu na tsaye akanta cikin uniform din waden.
Wanda Tun kan ta gama dawowa hayycin ta suka tursasa ta taci abinci,kuma tun data fara ci suke mita suna kashe mata gargadi kala kala while ko kallo itakam basu isheta ba

Daga nan Dabiarta na shiru shiru da tsinannen zurfin ciki kyaliya da rashin sabo saima abunda ya karu.

Babu ta inda matan dakin tan basuyi ba amma wafiyya macece wanda basu taba ganin irinta ba,hafsa da jennifer sune masu surutun maimoon itace shiru shiru mai lura da komai sosai da alaman suma bawai sun dade anan din bane.

Aganin su wafiyya is mentally rertaded,
Bata da lpyar kwakwala dan babu mai halayya irin nata face me ciwon kwakwalwa.

Yau kwanan ta goma sha takwas amma Ko sau daya bata taba ce musu cikanku ba bare ta musu kwakwaran kallo haka zasu karaci magana tsiwa watarana harda zagi saidai suna muugun shakkar tabata dan har yau basu san me zata iya yi musu ba.

Duk abunda take bukata zata fita ne dakanta ta duba kota nemosa awani wajen ita sam babu ruwanta da kowa da komai,she will spend her nigh praying tana mika kukan ta ma ubangij i sauran lokutan kuwa zuciyan ta acike yake da tunanin rayuwarta da danta nashwan kan kace wani abu wafiyya tayi suna a cikin prison bana waasa ba.

Kowani daki akanyi gulman yanayin ta,har aka samu tsageru da suke so su mata duka koda zasu maidata baiwar su cikin su harda jennifer da hafsa.

Ana cikin hakan ranar aiwatar da hakan ya zo,rana ne na labour so acan filin dake bayan dutsen dake bayan prison aka watsu su,duk an shirya kallon drama amma bazaka kalle wafiyya kace tasan me sukeyi bama,she is totally absent minded duk yawan yan prison din nan har yau bata kama fuskan kowacce ba bare muryanta duk da hakan yau da aka fito da su dukan su saitaga yawansu bai wani bata tsoro ba kwata kwata bazasu fi dari biyu ba.

Bayan Jami'ai Masu kulawa dasu sun rarraba musu labour dutyn su wayanda babu ruwansun ne duk suka kama aikin su atake,wasu na noma wasu na shara ana dan duba su lokaci zuwa lokaci har yamma ya farayi yan iskan cikin su kuwa sai mugunta suke ma juna suna wake waken iskanci da neman tsokana.

Abunda ya hanasu taba wafiyyar tuntuni baifi aikin da sukaga tanayi ba.

"Fasa dutwasu takeyi da duwatsu
She look scary tough and furious.
Kallo daya zaka mata kasan tana cikin tsananin fushi da duniyar kamar in mutum yazo kusa da ita zata iya masa mummunar lahani hakan yasa dayawa
Suka sha jinin jikin su amma su jennifer da sauran tsegerun inmate suna kan bakansu har aka zo aka kira security matron dake tsaye akansun tana dudduba su tana barin wjen suka soma wasan banza suna watso yashi ajikin wafiyya wacce bata ko kulasu ba altho matron din bata jima ba ta dawo hannun ta dauke da wata karamar baby wacce batafi shekara guda zuwa biyu ba bbyn tana kuka da alaman wajen uwarta aka kawota

Sosai hanklin wafiyya ya koma nan cikin tuno da nata dan har matron din ta mika ma wata mata babyn ta bar wajen matar wacce bata komai sai zaune,gaba daya tayi kama da marar lpya sosai fuskanta a lullube yake da baqar kyalle duk iyawar ka bazaka tantance kamannin ta ba,wafiyya ta kare musu kallo sannan ta dauke kanta tana me cigaba da tuno nata dan...

Can sai taji kukan babyn ya tsananta sosai,da kamar zata share cikin tuno da kukan nata danta yasa ta juyo,gani tayi su jennifer sun taru akan matar da alaman suna sone lallai su yaye kyallen fuskanta haka kawai abun sai ya sosaa ma wafiyya rai sosai.

Ayayin data mike zata je ta same su taji an rikota,yaune rana na farko data daga ido ta kalle maimoon.

Tace kiyi zamanki
"Karkije.

Wani kallo wafiar ta mata A hankli ta fincike hannun ta ta wuce batare da tace mata uffan ba sai itama ta biyo ta abaya.

" let me be..bana so,ku kyaleni in bada yata nono..
Matar ta furta hkn ranta a bace tana kare yarta da hannu daya daya na kare fuskan ta

"Ki yaye ta mana
Hafsa ta fada tana dada jan mayafin

" ke dadi takeji in ana sha mata nono

"Ure horny huhn
Hahahaha Babu namiji tana ta cutar da yarinya..

"That wont make u cum...hahahaha"

Sunkai su takwas gaba daya suka rudata da maganganun banza.

Fuskanta a killace yake amma Duk da haka zaka iya gane alamun hawayen dake zuba mata,inbanda wannan kukan da yawan boye fuskantan datakeyi da sai ace babu maraban dabiun ta dana wafiyya,itama kowa ya shaida ta da shiru da jan jiki da mutune, itace matar da aka kawota da danyen jego gashi har bbyn nata tayi shekaru da yan kai,Banbancin ta da wafiyyar shine ita tana iya yin maganan da zai bayyana maka halin kunci datake ciki ita kuma wafiyya sam bata da alqibla.

"Rungumar yartan tayi sosai tana dan jijjiga ta har kasan ranta takejin zafin magananun su,Suna ta mata dariya da alama babyn bata son hayaniyar dan ko kadan bata dena kukan ba.

Kawota..ko bata koshi bane?

Wani diff wajen ya dauke da shiru kamar mutuwa ce ta gifta,rudani ne ya mamaye wajen ayayin da kowa ya kasa idanun sa cikin mamakin jiyo tsadadden sautin muryan wafiyya lokacin data miko hannu tana shirin karbe babyn daga hannun uwarta.

Gaban matar na faduwa sosai ta soma tunanin mika mata babyn batare da tayu kokwanton komai ba dan tun data ji sautin muryan wafiyyar zuciyan ta yayi mummunan bugawa

"Charaf jeniffer tayi Saurin sa hannu ta kwace babyn"..

"Bazaa bayar ba
Nace baza a baki ba,kinfi uban waye anan da zaki zo gatsau muna mata magana kina tsoma mana baki?..nono a kirjinki kuma shine a kirjin kowa.

Ke kuma munafuka tun zuwanki nan kin taba bada yarki ma wani ya rike?wato kinga munafuka me kalar siffar ki na munafukai bugu daya tace kibata har zaki mika mata ko?
"To an kwace yar naki,bazamu baki ba sai munga wanda ya daure miki gindi a gidan nan.

Matar tace kuban yata..bana son fitina kubani ita..baby bata bar kuka ba.

Caa sauran sukayi akanta suna daka mata tsawa suna dada razana babyn dan ganin wafiyya a tsakiyar sun ya mugun saka tsumin su ya harba kowacce ta taso ne haikan tana huci cikin neman ayita ta yau ta kare

Cikin kunan rai Babu abunda wafiyya take tunawa
Face kukan da nashwan yayi lokacin da za a rabata da shi,bata san ya akayi ta shiga tsakiyar su ba

"Nine nan na daure mata gindi..abata yarta.

Kamar saukar wuta haka nan kalman nata ya diro a kunnen su hafsa da tawagarta

Daya daga cikin su ta tuma Ta doki kirjin ta cikin razanannen murya tace" hehehe Zakiyi damu?aimu Dama wannan lokacin muke jira..yaukuwa zaki ci ubanki

Kubata yarta nace!

Cikin izza da ikon da basu taba ganin irinsa ba wafiyyar tayi comanding dinsu

Babbar cikin su lutiya me suna maira wacce kusan kowa yake shakka tayi umarnin abada babyn amma ba mahaifiyar bace ta karba wafiyyar ce ta amshe babyn tana kallon babyn da dukan nitsuwarta cikin ikon Allah babyn sai tayi wani shiru.

Basu so hakan ba
Sunso ne ana rabasu da bbyn su ma wafiyya dukan taron dangi harsai sun mata lahani

Ita kuma wafiyya tunda ta amshe babyn taji hankalin ta yay mugun tashi,tuni taji aranta tana mutuwar son taga fuskan matar nan.

Matsoraciya Kin wani rike jaririya ki bata yarta ki ji damu,tunda ke kika kasa damu wallhy sai kin kwashe.

Can kasan idanunta ta dube su daki daki wani Kallon debar albarka tayi musu cikin miskilallen jan aji kamar bazata tanka din ba,can tace Wayake jin tsoronku?Jira nake ku taba yarinyar a hannu na kugane kuranku

Keeeeee marar kunya ki iye bakinki kona yayyaga ki anan,sai na kashw ki na kashe banza kinsan maza nawa nakashe sannan nazo nan wallhy ke karamar yar iskace
..cikin daka mata tsawa mai zafi maira tayi maganan
Wafiyya ta juya ta mika ma matar babyn ta batare da ta kalle ta ba hankli kwance ta dubi kwayar idanun maira ta soma magana da sanyin murya saidai acike sa jarumta da rashin tsoro yake
Tace
"Sannu babbar yar iska,wacce ta rako mata duniya,ina jarumtar anan in baki da sa'ar yi sai yar jaririya,tuntuni baki nuna isarki ba sanda aka kawo jaririya wajen uwarta?..na tsani mata jakunai tinkiyoyi matsorata
Koba komi nasan wannan matar tasha gaban ku
Chapter 4 · 0% Book details