← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 176

Sashe 14

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cak wajen ya dauke ayayin da hanadi ta fasa ihu tana me zubewa ajikin sa a rikice"
"Nashwan, nashwan naash, nashwan, honey...wayyo Allah na shiga ukku..me kukayi masa?ta maida tambyar kan zairah da wani irin fusata da bacin rai jiki na rawa zairah ta mike tsaye arude ta taho kusa da nashwan din, ta dan kallesa da kyau ta tsuguna agabansa kamar zata tabasa da alaman arikice take bata san tayi hakan ba data lura kamar suma yayi sai ta dago cikin rawan murya tace "nothing hapen ma..,pls we are sorry ma..suma yayi if u want i can help ma,bata kammala rufe bakin ta ba hanadi ta fincikota tsaye

Wani gigitacen mari ta sauke mata sanda ta kuma kifewa kasa.

"I will kill you..
How dare u come close to him... kazama,..mayya.."
Yau senaga gatanki a duniya.
Zaira ta tsorata matuka..Hanadi tana masifan tana duban nashwan tanaji kamar ranta aka taba,nan saiga isowar sauran yan uwanta kowa na tambayar meya faru?hakan ya kau da idanun ta akan zaira dake rawan dari

Tun kan wajen ya dada zama security tight zaira tayi saurin dauke wafiyya datake kwance akasa kamar tababbiya suka bar wajen nan taje gida ta boye ta gashi sosai gefen fuskanta ya haura sabida marin

Nan da nan Waje ya kacame taro ya watse kowa yanata kansa,sai bakin bindigogi da weapons kake gani a iska an watsa tear gas ana korar mutane gida daga gani ba tambaya kasan nashwan wamako is a highly important person cos anan babu wanda baiga madaran zunzurutin tashin hankli ba.

within 10 mints Emergency plane dinsa ta iso nan da nan akyi da shi Babban asibitin sa dan dama shikadai ne yake da dan karamin villa.

Villar tasa wata Anguwa ne mai dauke da 1000 estate ana kiran wajen, _Grand brew Auto villa"G-BAV._ .
Komai na unguwar iri daya ne dana ubansa wato brew paradise banbanci shine na nashwan estate ne kawai ba babban matattaran jamaa kamar na babansan ba,so duk wanda yake zama a anguwar Grand brew a karkashin mulki da ikon nashwan yake

A matakin karatu fannin likitanci Nashwan yaje ya karanta irin pure medicine din nan,so shi medical doctor ne amma ba na mata ba shiba na zuciya ko brain ba amma babu abunda bai iya ba.
Sannan ya karanta business and finance under 2yrs special skill course a kasar honkong dan dokar gidan sun ne yaxo da hakan sabida babban ma tattalin arxikin da suke dashi thy r all future business investors.

Anan unguwar sa ya gina baban asibitin sa wanda yaji kayan aiki na zamani da kwararun likitoci da masu kula da tsaftar muhalli,uwa uba high grade technology medical equiptment dan ko a kasashen europe ne ba kasafai ake samun irin naurorin asibitin ba.

Sunan asibitin "wamako international hospital mutane su ka masa inkiya da "WIN" hospital Kuma duk wani mazaunin anguwan a kyauta ake masa jinya amasa komi cikin kulawa,amma na waje ne in sunzo sai ace su biya kudi.

Kuma a tsarin asibiti akwai "....generic medicine.. wato tsarin dayake rage farashin kudin magani da jinya domin a raga ma talakawa wahalan neman ingantaccen lpya..

Cikin tashin hankali kaf family members din mayor aseem suka zagaye private ward din da aka aje shi,polisawa suna famar tambaya akan tambaya.

Is nothing serious amma dayake ya shafi nashwan sai aka zafafa shi aka maida sa babba
musamn fannin hanadi data dau zafi tana masife head security a cewar ta aje marmaza a kulle mata wayancan mata tun ma kafin ranta ya baci ita ta dau mataki da kanta,amma sai hajiya turai tace a dakata tukun aga farfadowan sa
Nan da nan labari ya isa gidan su wato SOUTHSONG MANSION inda hankalin lady jasmine ya tashi ta shiga neman layin mijin ta dan shi bai cika zama ana nan ba.Tun da tace masa nashwan na asibiti a sume hanklin sa yayi matukar tashi har ya kasa samun nitsuwa domin yaji asalin kan labarin sai maimaita tambaya yake
"Jasmine nace Meyasamu nashwan din?is he fine at all?and wher the hell is doctor kabeer.

Shi doc kabeer din family doc dinsu ne wanda suka matukar yarda dashi lady jasmine tace"ka kwantar da hanklinka,pls calm down mayor,..bafa wannan bane kadai abun damuwa,
hanadi ta fada min wai wasu mata yagani suna hada ido ya sume,Aseem inaga hala nashwan yaga wani wanda ya sani ne and im afraid its his mum wafiyya or bahiyya kasan dai matayen nan suna raye basu mutu ba ko?

Cikin runtse ido mayor da rashin son yaji zancen yace
"Ohhh jasmine pls cut the crap naji ma ance matar wasim ta dade da mutuwa..
Kinsan prison din da muka aje su kuwa?ta ina ne ma zasu fito mmm?nasan da akwai wani labari da tuni angayamin.
Tsaki yayi kafin ya cigaba da maganan "Amma bazamu shagala ba,kisa a binciko matan sannan kice ma doc kabeer ya kira ni a waya yanxun nan

Tace ok sannan ta katse wayar,nex call ta dialing number doc kabeer bugu daya ya dauka cikin bada girma yace

Good day maam lady J..
Bata amsa shi ba cike da kasaita tace how is my son?

Doc kabeer yace Alhamdullh ya farka just now dama suma kawai yayi no any medical complication

dagajin haka ta sauke karamar Ajiyan zuciya "thank god ta furta kasan makoshi,call my husbnd now yace ka kirasa..yace ok maam tana kashewa ya kira layin mayor Aseem wanda baiyi wata wata ba ya soma tambyar sa cikin yanayin matsuwa
"can you tell me whats goin on?meya jawo nashwan yake hakan kabeer? sanin kanka ne taron nan yana da muhimmaci a rayuwata and nashwan is the key,he cant be sick..wai ance wasu mata yagani ya sume ko? so what does that mean? kaika tabbata ba aljanu bane ko wasu da suke so su dagula masa kwakwalwan sa?

Dan shiru Doc yayi kafin ya numfasa cikin rawan murya da nitsuwa dan suna balain tsoron mayor so suna bashi high level of respct.

"Sir...akwai abunda na fahimta

Mayor yace say it

Gyara tsayuwarsa yay sannan ya dube nashwan din dake baccin sa peacefully yayi gyaran murya"sir inada tabbacin cewa koma wace ce nashwan ya gani awajen nan toh tanada da alaka me karfi da past dinsa..

Adame Mayor yace what?

Doc kabeer yace yes sir,da aka kawosa nikadai na duba sa kuma lokacin daya farka sunan maman sa yaketa kira
..inaga hala yaci karo ne da mai muguwar kama da ita ko yaji irin muryan ta zak zak..
But for sure an tuna masa wani abu ne..

Damn it..mayor ya furta a zuciyar sa yana me dunkule hannu baice komai ma doc kabeer ba tukun wani Shiru yy cikin tunani, shi dama Ya dade da gane hakan "ya lura har yau memoriyn iyayen nashwan basu shafe a kwakln sa ba
Yace..kabeer..ya kira sunan doc cikin wani dakakkiyar yanayin da yasa shi ya tsorata..
muryansa na rawa ya amsa da yes sir.

Yace kanajina? doc yace yes.wata baqar nunfashi ce ta subuce masa,yace "Wipe it,..erase his last memory now,marmaza ka goge masa abunda ya faru karma ya sake tuna abunda ya same sa a kauyen...and i will make aure bai sake xuwa wancan wajen ba,doc yana amsawa da done mayor ya kashe wayar sa nan da nan doc ya dauko ruwan allura na maganin aikin da aka bashi ya juye a cikin ruwan da aka jona ma nash,hakan ne kawai zaifi masa sauki dan yasan daga zarar nash ya farka to bazai iya masa komai ba sakamakon taurin kansa da kasancewar sa babban likita.

Hakan kuwa ya faru bayan awa biyu nashwan ya farka amma sai ya qumshe idanun sa yay shiru sabida dagulewar da kwaklwakr sa yayi
"Idanun sa a rufe suke amma He is looking at a strange face,fuskan wata kyakywar yarinya ne yake ta maimaituwa a brain din sa kuma ya kasa tunata,duk sanda ta bijiro masa sai ya shagala wajen kallon cikin kwayar idanun ta wanda ba manya ba kuma ba kanana ba and the colour of her eye ball is grey,dark grey kuma a bushe yake ,farin ta kamar an wanke shi da madara tana da saje cikar suman goshi sannan suman kanta baqi kirin ne yana da cika da tsayi kamar tsiririn hancin ta and her lips is dark red dan cakwal dan karami..gaba daya ya rasa ita wacece sannan a ina ya santa?abun tun na wasa sai ya soma jin kamar zaucewa zaiyi..

Fannin su hanadi kuwa da kyar akayi calming dinta daga diddigin datakeyi akan lallai sai an nemo mata wayancan matan,she just want to pissed them tana so ta walakanta su ta kaskantar da su ta nuna musu banbacin su,in batayi hakan ba batajin zataji sauki aranta,nashwan tamkar shine rayuwar hanadi dan ji take da ataba nashwan gwara a kashe iyayen ta

Wani irin makahon so take masa mai zafi mai rikita kwakwalwa
Wanda ita kanta bata san mafarin sa ba.

All she dream waz to be with him,ta kasance matar sa sarauniyar sa, zuciyar sa, duniyar sa, ya zamto nash baya iya numfashi sai da ita.

Dumbin walakancin sa tun suna yara tana shanyewa cikin halin ko in kula da nata feelings din.
Muddin nash nata ne to duniyar ma zata iya zubewa agabn ta bata ma san anayi ba.

Da akace ya farka kuma lpyarsa lau sai Abhay da abhi da haj fulani suka wuce gida,ita kuma hanadi ta tsaya da banafsha takan so banafshan ne sabida duk gidan babu wacce munanan halayen nashwan baya shafa kamar banafsha.

Haka kawai Yake matukar kaunar yarinyar baya son abunda zai taba ta
She is like his favourite pet dan ko wasa zaiyi da ita yakeyi and no one else,itama tun da taga ya suma ta kasa samun nitsuwa amma bata da rawan kai kamar hanadi she is calm and majestic,wani irin nagartacen sanyin hali take da shi.har kasan ran hanadi bawani kaunar kusancin ta takeyi da nash ba amma babu yadda ta iya cos in nashwan yace yana son abu al'dan sune subarsa da shi kamar basa da ikon hanasa.

Hanadi tana tsaye,ita kuma banafsha ta dora kanta akan cinyar kakar su hajy turai tana dan shafa kan nata kadan.
Chapter 14 · 0% Book details