← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 176

Sashe 34

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kafin agama nuna ma zairah ko ina har lokacin azahar ta gabata wani sabuwar kwakwma cikinta ya soma yi alaman yunwa ga wani tsami tsami da kafarta yakeyi dan sun hau steps steps kam babu laifi wai dan ma umma barakan tana binta da karin bayani then Finally umma baraka ta jawo ta suka nufi inda aka Rabbatul bait wato sashen lady J

Zaune suka same ta tana zuba wani azazaben qamshin turaren indivutuel mai gauraye da sandalwood da amber, tayi matukar kyau jikinta yasha uban wankan farar code lace tsadadde wanda kamfanin soltis daga france suka kerashi,wani ubansu dinkin riga da zani aka mata na bubu da zani,both wuya da hannun kayan ya ci uwarsa da zubin aiki me dan uban tsada..

Wata arniyar 5inches heel na valentino garavani shiny silver rock stud dinsa taci ta dora kafar daya akan daya da white medicated gogles akan damammen fusknta hannunta dauke da wani exclusive fashion Catalog na
Kamfanin rahul arora's fashion brand dayan hannun ta ta kimesa akan lallausan deep brown sofa,hannun yaji zobe da agogo da bracelet din gold

tana duba cataloque din a nitse kwarjinin ta ne yayi saurin dasa musu fargaba da nitsuwa

Ummu baraka tayi saurin matsowa gaba ta fada kasa cikin girmamawa tace "Allah shi taimake ki Lady jasmine...fatan na sameki lpy?
ba laifi lady j tace Lpya batare da ta dago ba"..meya kawoki?...ta maida tambayar kamar batama san da wata mai kama da zairah a wajen ba

Ita kuwa zairan Tsaban tsoron haduwar siffarta ne ya nakasa ta,she dint look friendly at alll lady j irin matan nan da maza ke jin shakkar su tsabar jinin iya iko da girma da jidakai dake bibiyar yanayin su
.kasa kasa umma B tayi da sautin ta tace"my lady Wannan ne yarinyar..Private maid din sir nashwan..Allah ya kara maki girma...a shirye take kuma yau zata fara aikin ta..Can Sai ta dago atake ta kalle zairah cikin kankanin lokaci ta wani yamutsa fuskanta
tace"Kuma bata iya gaisuwa ba?sautin kuuu cikin xairah ya bada,tun kan umma baraka ta budu baki tayi mata magana zaira tayi rusunun dole ta soma gaisuwan cikin i i na kallon banza kawai ta samu wajen lady j wacce ta yi banza da ita tacigaba da duban jaridarta nadan mintina after like 30 scnd ta aje agefe ta zare glases din idanun ta tana sauke ajiyayyen numfashi,can sannan ta kalle zairah din a tsanake
Meye sunanki?
A sanyaye Tace
Sunana zairah..

To ki saurare ni kiji abunda zan fada miki duk abunda baki gane ba u better call my attention ok?

Kai a tsunkuye zairah tace yess ma.

Nan lady J tace
Game da ayyukan ki asashen dana As early as six u are up,ki tabbata By 7.00Am na Ko wani Safiya zaki na shiga dakin sa bance kuma kije ki tashe shi ba kedai ki tabbata kin aje mishi fresh spearmint tea,and dont forget little or no Sugar,inkina son kanki da lpya ma honey kawai Za kisa Masa like 2 teaspoon sai ki gauraya,inkin gama anan dakin san Zakiga dark glass side table leave it on top sannan sai ki fita

Zai tashi Zai fito motsa jiki karfe 8.00 ock Dai dai dan haka kiyi kokari Yana bada baya ki shiga dakin ki canza bedings Dinsa ki tsaftace dakin,kar ki manta bawai zallan dakin baccin sa ne aikin ki,sauran part din san ma duk kece zaki saka ido

Yafi son cin abincin safe dana dare dan haka Akan lokaci xaki na kasancewa a kitchen din dake sashen sa an gaya miki kitchen din nashi ne shi kadai ko?A Dan Sanyaye zaira tace eh.

Tace good to Kar ki sake Kiyi masa abinci awani wajen inba A nashi kItchen din ba wannan babban Doka ce,if anything hpen to my son i wll personally kill u

Cike da fargaba xairah tace yess maam

Sannan Karfe 9 inya taho dinning dinsa cin breakfast u have to wait,mena ce?
Xairah tace"i have to wait..lady ta dauke idanun ta cigaba da magana
"Kullum ki tsaya ki yi serving dinshi kuma ki nitsu ki Zuba mashi ko wani nauin abincin da akwai ba tare da kin tambaye shi mai yake so ba, Bayan kin kammala da nan ne zaki iya ki koma ki hada mashi ruwan wanka kominshi da akwai study the instrument first then set it at exctly 40 degree..kinajina?

A hankli Zairah tace eh..

"Kar ki damu da serving dinshi abincin rana musammn inya tafi asibiti,he is alwys absent till the nex morning sai dai Idan ya dawo da dare ne hala zaki kawo abincin daren shi dining dinsa kar kuma ya taba zarce misalin karfe 8.00 in ya wuce haka ki barshi,sauran lokacin da kike free zaki iya amfani da shi kiyi sauran ayyukan Daya dace

Iya kallon bakin ta zairah tayi, aranta tace hmm Ikon Allah shikuma hakan rayuwar sa yake komi a kayayyede Hmm tabb di,Umma baraka ce ta dakatar da tunanin nata bayan dan kiran sunan ta datayi Afirgit ta dawo hayyacinta ta amsa da naam..

Tace Kinji abunda aka ce miki ko?

A dan sukurkice tace naji insha Allah zanyi Duka..

Nan Lady J ta sallame su Fuskar Ta dauke da Wani irin fade expresion irinna"huhhhh finally am off the stress'.
dama kula da nashwan yana daya daga cikin abunda yake shake mata wuya arayuwa
Aranta tace
"Suje can su karata ni barin musu kasar ma xanyi..

Daga nan zairah tayi sallama da kowa asashen maids inda aka barta da ummu saliha awani daki

tana idar da sallan zuhr Tace Tashi muje na kaiki sabon dakin ku ai Zaman ki anan ya kare kuma..

da sauri zaira ta dago tace sabon daki kuma?Ummuh tayi murmushi cikin son kwantar mata da hankali tace zairah kenan,kin manta full term maid ce ke?daga yau babuke babu nan wajen,kuma inkinga kin bar gidan nan to wani babban uxuri ne

zairah tayi jim Daga nan dai batace uffan ba,Hannu ta mata ta taso jiki a sanyaye ta fara biyo ta a baya Basu tsaya a ko inaba sai a cikin wani sashi Ta cikin resident din nashwan Mai kamar sleek duplex apartment Amma bashi din bane

design Ne kawai irin na dormetries da gadajen bacci up nd down guda uku biyu suna kallon juna daya na can gefe shi daya duka snjji blue nd white bedsheet kalar atamfar aikin su da aka babbata na aiki

Tace yenge da bingel zasu taho anjima yanxunma dan an aike su, ke ki xauna anan ta mata nuni da right bed tace ga naki gadon tare zaku na kwana ku uku, Zairah tace toh sannan suka fito atare

Kafin ummu saliha ta wuce Sai da ta nuna mata Wani huge zigzag stairs dayaji kwalliyar flower verse da alamu nan zatabi ya Sada ta da sashwn nashwan na asali a saman nasu dakin yake,daga nan umma saliha ta mata bankwana ta bada baya nan zairah ta dawo dakin ta abunta,zama tayi abakin gadon tana sauke ajiyan zuciya komai ya burgeta sosai ba irin tarkacen kayan duniyar nan but Its a very Exotic sleek style bedroom So simple and elegant babu hayaniya

Ta cigaba da kalle ko ina ga big big wardrobes ga lockers ga manyan dressing mirror da dakin wanka mai bari uku na mutane uku gadajen su ma Yan madaidaita ne Ga brass lanterns da lamps Masu fararen haske akan kowani gefen gado, komi awajen design din Sa fari ne kar gwanin sha'awa.

Tafi minti goma tana cikin wannan yanayin kafin ta ciro small nokia phone din ta wanda tsaban bamai kiranta ma zaka ce bata dashi ne kwata kwata number Surajo mai shagon chagi ta kira dan ya hadata da maman ta wafiyya
Inda taji dadin jin sautin muryan tan sosai,she seem fine alhamdullhi hakan ya dada kara mata kuxarin fuskantar abubuwan dake gaban ta..

Tana gama jejjera kayan ta a locker ta ta cire kaya ta dan fetsa freshner ta kara gudun ac
bathrum din dake setin shatin gadon ta ta fada ta wanke jikin ta tas ta fito tana qamshn mayukan wanka nan ta gabatar da sallan la'asar inda tayi tagumi xuciarta cike da kokon ton ko taje sama taga sashen nashi ne koko ta bari seda safe,hakan ya hanata samun sukuni dan yaune dama zata fara duties dinta a haka har wani gajiiyayen bcci yayi awon gaba da ita Ta dade tana baccin harda minshari Saukan ruwan sanyi me blocks din kankara dataji akan fuskarta yasa tawani irin ware ido at once kafin tasaki wani irin uban kara tana kalle kallen dakin a firgice,wani uban tsawa aka dirar mata "ke malama ki natsu" taji an mata maganar kamar daga sama, dago kanta tayi atsorace taga Bingel ne akanta rike da bottle water mai sanyi wanda tana kyautata zaton na ruwa ne kuma shi aka zuba mata

Tana lekawa a bayanta taga hanadi a tsaye it seem like ita tace akawota nan din sede girman kanta yace Allah ya sawwake mata ita dakanta ta rike goran botle water bayan ga baiwa a kusa da ita.
Chapter 34 · 0% Book details