← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 176

Sashe 161

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Tasan waye mayor Aseem bare ajega matar sa jasmine mimiko
matar da sabida tsaban son duniya bata tabayin lokacin kanta ba ma bare na dan wani? babu tantama tasan nashwan bai shata da dadi ba,duba da yadda tasan danta da shagwaba da sakalci,da yawan kuka da taurin kai waya san ma ko da duka da muxgunawa aka raineshi aka axabtar dashi,tasan dai anbashi ilimin boko to koma an bashi ilimin addini da tarbiya oho?hawaye masu balain zafi ne suka shiga kwaranyowa daga kwarmin idanunta data tuna illar dake zagaye da hakan,ba dan duk abunda Allah ya tsara ma bawarsa daidai bane da yau sai tace ta shiga uku ta ina zata fara gyara rayuwar danta?
Kallon shi ta cigaba dayi tana hawayen tanajin kamar mijinta na tare da ita awajen,wani azaban kewarshi da tunaninsa takeyi har sautin kukan data keyi na fitowa waje batare datasani ba,nashwan yana baccinsa ta kwanta agefenshi ta rungume sa sosai har saida taji hanklinta ya kwanta sannan ta dena kukan ajikinshi,she really need him to wake up kodan yay wanka yay sallah dan zuriar su mutane masu tsananin kulawa da addini,ganin he is so deep into slumber bayadda ta iya face ta kama mashi gabobin jikinshi musamman ma kanshi da tafin hannun shi,anan ta rinka masa adduoin samun lpya da neman tsari daga sharrin shaidan har zaira ta shigo ta karbeta,Abincin ma kadan sukaci ranar su ukunsu akan gadon sukayi bacci as usual qashe gari wafiyya ce tayi musu komi cikin kulawa kamar yan yara kanana.

kwanan su biyu a gidan mr mahdi na xuwa akai akai yana dubasu with each day sai yaga improvmnt a saukin nashwan da tunda ya fara iya bude idanunshi saidai yay ta kallon su amma baiya cewa komi,sai yau wafiyya take dada ganar da su akan irin ciwon kwakwaln shi na odd,sunji tausayin sa sosai da suka san cewa tsananin bakinciki da damuwar rashinta shiya jawomashi silar ciwon,dake wafiyya tana hadawa da maganin asibiti da sirrin waraka daga qur'ani sai abun yay mugun sauki,altho she feared dat bazai warke duka duka akan lokaci ba sabida da ciwon ajikinsa ya girma so ya kai wani stage din da dole ne sai anjira saukin sa a hankli,But she assured them dat insha Allah danta zai warke dika

Yauma Da yamma lis ya farka jikinsa a muce yanata kirar sunan maman shi, wafiyya ta taho ta rungumeshi ajikinta tana shashhafa shi
Yana sauke ajiyan xuciya He is no longer on drips taji kuma jikinshi ba zafi,dan haka ta fara tunanin taimaka masa yay wanka ko zaiji dadin jikinshi aje kanshi yay akan kirjinta ya kwanta kamar yana so yay magana da ita amma sai yaji ya kasa bude bakinshi
Cike da lallabi Ta tambayeshi koya najin wani abu na ciwo ajikinshi ya girgiza mata kai,ta tambaye sa zaici abinci?nan ma kam taga ya kulle idanunshi da alaman bayason jin sunan abinci,sanda ta ambace wankan sannan ya dan bude idanunshi batayi wata wata ba ta dan tallafo shi kadan ta kama kwabe mashi kayansa ta barsa daga shi sai boxers dinshi,hannun shi ta kama ta taimaka masa ya sauka daga kan gadon ya tsaya a tsaye kamar bai san ina hanklinsa yake ba,tana gama abunda takeyi ta ja shi sukayi bathrum ta hada ruwa mai dumi a katon bath batare da ya cire wandon ba ta umarce daya shige ciki,nashwan yana jin dadin dumin ruwan ya wani lumshe idanun sa ya lafe,da tafukan hannunta ta deba ta watsa masa ajiki kafin nan ta juya ta dauki Dan cup ta debi mai yawa ta xuba tin daga tsakar kanshi xuwa jikinshi

Sosai ta mulke sabulun ta mai sanyin qamshi na pure pormenganete ajikin soso, saida yay kumfa sosai sannan ta fara goga mashi a jikinshi tana wanke sa tsaf baida aikinyi sai sauke mata ajiyan xuciya,Tun yana kulle idanunshi harya xo ya bude yana kallonta,wani irin sabon yanayi ya dingaji a jikinshi da zuciyarsa sai yaji kamar an canshi ne ba shi din ba.

Sanda ta gama tsaftace shi tsaf sannan ta kawo masa katoton white towel ta umarce shi da cewa yayi tsarki makansa kafin ta dawo,wafiyya tana barin wajen ya farajin kamar bazai iyaba dan sosai yaji dadin wankan datayi masan,ji yay ma kamar bai tabayin wanka ba saiyau,da dan uban kasala ya tsantsane ruwan ya cire boxers dinshi da pant dinshi ya jibga su a wajen,ya wanke gabansa da ruwan dumi ya dauraye ya fito,towel dinda ta aje mai ya dauka yana dorawa akan kungunshi yaji daga bayanshi kamar ana knocking sai kuma yaga jim kadan an bude kofar ta shigo,kallo daya sukai ma juna basuce ma juna uffan ba sanda ta bashi brush ya goge bakinsa, nanma bata qyaleshi ba yanayi ne tana tayashi dan bata gane yadda yakeyin abu yana mata kamar kominshi abnormal

Yana gama alwala sukayi waje suka fito cikin dakin,yaga wai harta gyara gado already ta shimfide masa sallaya ga wani sabon gogaggen jallabiya ligh brown data feshe shi da turare ta aje masa shi akan gado,zama yayi abakin gadon aransa yana tunanin afkuwar komi,wato mahdi da matar sa zaira sunsan inda maman shi take tuntuni sukayi masa shiru ko?wanann wani irin mugunta ne?he was lost deeply in tot ya kasa gane kan lamarin gaba daya,duk abun da wafiyya take mashi ba ji yakeyi ba,harta gama goge ruwan jikinshi da towel ta shafa ma fatar jikinsa mai bai dena tunani ba sanda ta umarce shi daya saka kayansa ya biya sallolin dake kansa,bai mata musu ba ya amshe jallabiyar ya rike,ta mike tsaye ta bude wadrob ganinta yay da wasu pack din calvin klein irin guntayen short din nan masu kama da boxers sabbi kar kar a leda ta mika masa tace mashi ya xaba ya saka yanzun nan zata dawo,haka ya rinka bin bayanta da kallo har ta fice,da kyar ma ya mike ya saka daya daga cikin wandonan datayi masa das das kamar nashi saiya saka jallabiyar akai Wajen maida sauran kayan yaga yadda wardrobe dintan yake cike da kayan maza ya duba yaga duk kuma size dinshi ne da balain mamakin ganin hakan ya bar wajen ya koma kan sallaya ya tada salla shikenan kuma ya sa aransa cewa tuntuni maman shi ta san inda yake ta kyaleshi...

Sallan kawai yakeyi anma abunda ya cike mai kwakwalr sa kenan,have thy been playing him?
Aganin sa wannan wasa yayi masa tsauri,he spend all his life thinking abt his mum ta yaya zasu boye mashi ita bayan sun san tana raye,da kyar ya gama biyan sallon shi na jiya yana zaman hutuwa sai ga zaira ta bude kofar ta shigo wani irin kallon dayayi mata sanda taji gabanta ya bada sautin rass mai qarfi,dauke kai tayi kamar bata san ya idar da sallan ba ta aje cups din dake hannunta zata juya wani tsawa ya daka mata"Ke!!!...zo nan.
Zaira ta juyo ta kalle shi a tsorace ganin yadda ya hade ransa tamm,sai taki sam ta karaso wajensan ta ja ta tsaya abunta mikewa taga kamar zaiyi saita dan matso cikin marairacewa tace champ gani bata karasa ba taji ya fincikota ta fado cikinshi bazata saida ta mugun firgita,da nauin muguntar shi ya matse ta ajikinshi sosai"whats d meaning of these lies ure lying to me?
Kinsan mama na tana nan araye anan tuntuni ko?wato kin hada baki da mahdi dan baku da imani kuna playing dina huhn?U knew her how comes u dint tell me?tun yaushe kika san mamana?ita ta turoki wajena ko?ki bude baki kimin magana ko ranki ya baci yanxun nan,zaira ta fashe masa da kuka sosai ta fara bashi hakuri jin yadda yake maganan da bacin rai kamar ma duka zaiyi mata,ni fa babu abunda nasani..muryanta na rawa ya fito,ni ban hada baki da kowa ba,nima ai bansani ba,sake matse mata hannu yay ya girgiza mata kai da jajayen idanun shi alaman karta yadda tayi masa karya,bakin ta na rawa ta fara bashi labari tace ai mr mahdi ne ya gaya mata ya same maman shi,sai daga baya ta gane ashe maman ta ne asalin maman shi...wani hararata yayi"dalla tafi can bayan kin yaudare ni..cikin kukan tace ni fa ban yaudare ka ba,i swear to u har mukayi aure bansan haka abun yake ba
I came to find out later later shine nace mashi in muka dawo ni xan zo dakai nashwan yana jin haka ya saketa ya dafe kanshi, baice komai ba xaira taja jikinta daga nashi ta koma gefensa ta rike hannun tan daya matse tanata kuka,bude kofar akai saiga wafiyya ta shigo da tray din abinci ganin su ahakan yasa ta tsaya tana kallon su aranta tana ta mamaki,ganin nashwan bai dago kanshi ba ta maida maganan kan zaira tana cewa.."my princess lpya kuwa?zaira batace uffan ba ta tashi tana shesheka tayi waje bata kulata ba,aje abincin tayi agefen shi shima tana lura dashi kamar kukan yakeyi,"all this while sai yau ne za'a ce mashi maman zaira asalin maman sa ne?how cruel is dis world daya kasa fahimtar dashi hakan tuntuni, jin saukar hannun ta akan kafadunshi yasashi dagowar dole,suna hade idanun sa ya kau dakansa gefe ya hade rai..

,"dan shiru tayi kafin can cikin sanyin murya tace harka idar da sallan to zo kaci abinci?ya girgixa kai
Alaman a'a,ta umarce shi akan da ya tashi ya karasa sallan nan ma bai mata musu ba yay sallan tana ta kallon shi taga duk ba ahayyacin sa yake ba,yana idarwa ta zauna daf dashi tana bubbude wamers da alaman zata bashi abincin abaki,gashi kusan duk abunda yake sha'awar ci yaga ta dafa cike cokalin tayi da hadadden chicken caseroles wandayaji mashed patatoes zata kai masa baki ya ma abincin kallo daya ya kau dakan sa gefe ya bata ransa
Chapter 161 · 0% Book details