Sashe 99
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Mummy dake tsaye jikin ƙofar toilet tana jiyo wayar da Nabila ta yiwa Zainab, banda ƙoƙarin buɗe ƙofar babu abinda take yi ranta a matuƙar ɓace take cewa “Wallahi Nabila in baki fito ba jikinki ne zai faɗa miki.” Tana daga ciki tace “Mummy bafa zan fito ba sai Zainab ta dawo babu abinda zaki ce mini har sai ta dawo gidan nan koma menene kiyi a gabanta, in ke kince a’a ita ai tasan da aure tsakanina da yayanta.”
Mamaki ya sake rufe Mummy, ɓacin ran dake fuskarta kuwa ba zai misaltu ba, ganin da gaske ba zata buɗe banɗakin ba yasa ta fita daga ɗakin kanta na wani irin sarawa, ɓangaren Kabir tayi don sam yanzu ya daina zaman gida, yanzun ma baya nan, anan falon ta zauna ta ɗauki waya ta kirashi, yana ɗauka tace “Kana ina?”
Ina nan ƙasan layi akwai wani gidan abokina ina can.” “Ka dawo yanzun nan,” tana kaiwa nan ta kashe wayar tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta dafa saman kanta da take ji yana wani irin zafi kamar wuta, yanzu ita ya zata yi? Ta ina zata fara ɓullo wa abinda ke faruwa? Kalaman Nabila ne ke dawo mata, bayan ta sake mata magana akan ganin likita tace ba zata ba, har zata fita daga ɗakin ta sake kallonta tace “Nabila na roƙeki da Allah karki janyo mini abun kunya, don Allah kar kiyi abinda zai sa farin cikin gidana ya lalace, shi yasa tun farko naƙi sakar miki fuska ni nasanki fiye da yadda kika san kanki nasan wannan ladabin da kike yi a gidan nan wanda har kowa yake ganin baki da wani mugun hali ni nasan pretending ne, sai dai ban taɓa nuna miki na sani ba, fatana don Allah ki koma wurin Inna ki samu miji kiyi aure don Allah.”
Nabila taji tasa dariya da mamaki take kallonta tsoro ita kanta ya bayyana a fuskarta, tana kallon Mummy tace “Kinga rashin faɗarki bai daɗa miki da komai ba, yanzu burinki ya cika? Wacce baki yarda da ita ba ta tabbatar miki da mugun halin ta?”
Yanayin Mummy ne ya canza tace “Me kike nufi?”
Ƙafaɗa ta ɗaga mata tace “Idan Kabir ya dawo ki tambayeshi ni ba zanyi komai ba sai Zainab tazo, zan gani in zaki iya korata bayan abinda ya aikata.” A tsorace Mummy take takowa tace “Tashi mu wuce gida wurin Inna….” Kafin ta ƙaraso shine ta shige toilet da wayarta, tana shiga tasa key daga nan shine ta kira Zeey. Ji take yi zuciyarta na wani irin zafi wanda ta tabbatar da za’a gwada jininta a lokacin tabbas da zai kai hawa 200/130 ga wani uban ciwon kai dake damunta, duk laifin Inna ne don ta dade tana nusar da ita zaman Nabila gabanta shine sam bata son yawan zaman nan da take saboda Kabir don tun tuni ta fahimci son Kabir take yi. Ya zata yi in da gaske take cikin ne kuma na Kabir ɗin ne? Ƙwaƙwalwar ta sam ta kasa yin wani dogon nazari don abubuwan da zasu faru a kan cikin nan Allah ne yasan yawansu, Daddy wanda ko da wasa baya son image ɗinshi ya ɓaci taya zai fuskanci abun nan? Ga Zainab wacce tasan ko me zai faru ba zata bari ace za’a tauye hakkin Nabila ba duk kuwa da yayanta ne mai laifi don haka take a kuma kan maganarta Daddy ya kaita ƙasar waje karatu saboda ya gaji da wannan halin nata.
Kabir ne ya shigo tana nan a zaune, kallonshi tayi sai kawai taji hawaye sun zubo mata, nan da nan hankalinshi ya tashi yace “Mummy menene? Ƴan Ɗambatta sun zo ne?”
Wasu hawayen ta sake yi tace “Ba gwara suzo kullum ba da abinda kake neman jawo mana Kabir meya shiga tsakaninka da Nabila?”
Gabanshi ne ya8i mugun faduwa hankalinshi yayi wani irin tashi, jikinshi na rawa yace “Mummy wallahi nima ban sani ba.”
Wani abu ta haɗiya kamar zatasa kuka tace “Kabir ka janyo mana yanzu ban san yadda zamu yi da senate ba.”
Da sauri yasa gwiwowinshi a ƙasa ya riƙe ƙafarta yace “Mummy ki taimakeni a zubar wallahi ni bansan komai game da abinda take cewa ba, ni wallahi ban tuna komai ba, Mummy in Dady yaji ni nasan kasheni zai yi.”
Kallonshi tayi tace “Ta riga ta faɗawa Zainab.”
Idanu ya zaro yace “Kafin magana ta kai kunnen Daddy dkn Allah Mummy ki sakata a gaba muje a zubar ni wallahi ban san nayi ba.”
“Tana ciki ka gwada yi mata magana.” Cikin sauri ya mufi ɗakin Nabilan ya ƙwanƙwasa tare da sanar da ita shine, da kamar ba zata buɗe ba sai kuma ta buɗe don bata son ɓacin ranshi, kallonta yayi yace “Nabila na roƙeki da Allah muje a zubar dashi, na ɗauka ke kanki baki tabbatar da ciki bane da?”
Itama kallonshi tayi tare da riƙe cikinta tace “Na tabbatar ɗazu da safe, sai dai bazan iya zubar da ƙwan ka ba, ko da kuwa zan rasa raina.” Tayi saurin rungumeshi kam tana cewa “Don Allah Kabir kar ka biyewa Mummy, da aure tsakanina da kai kada ka bari zancenta ya rabamu, ita tana ji kamar ta haifeku ne sai dai mu sa a ran mu ƙila ma rabon auren mu da zuri’armu ne yasa tazo a matsayin kishiyar mahaifiyarku.” Janye jikinshi yayi yace “A wurun mu ita ce mahaifiyarmu kuma babu wanda zai nuna mata mu ba nata bane, bazan iya auren kanwar mahaifiyata ba na sanar dake a baya yanzu zan ƙara sanar dake, ko ba don Mummy ba babu soyayyarki a raina.”
Idanuwanta ne suka yi ja da sauri ta nufi gaban madubi ta fara zubar da kayayyaki ƙasa tana fasa su turare, cikin kuka take cewa “Haka kace? Haka kace? To lallai zaka tsinci gawata don bazan iya rayuwa babu kai ba kuma babu wacce ta isa tayi rayuwa da kai ina kallo sai dai duk mu taru mu rasa.”
Hannunta ya matso ya finciko ya matseta sosai ta yadda zata nutsu taji me yake cewa yace “Enough! Just listen to me, kin san kina sona kika sanar da Mummy kina da cikina? Kika sanar da Zainab? Haka ake so?”
Cikin dauriya tace “Naga kai bazaka maida hankali wurin ƙwato ni ba shi yasa ni na furta don na raya soyayyar mu.”
Wata dariyar takaici yayi yace “Wallahi in har kika sanar da Zainab nine mai cikin wallahi magana bazan sake yi miki ba balle akai ga Shirmen zancen da kike yi na aure, na dai faɗa miki.” Yana kaiwa nan ya fito tare da wucewa ɗakin shi.
Yana fita ko minti biyar bai yi ba Zee ta buɗe ƙofar ɗakin Nabila tana haki da alama gudu tayi wajen shigowa ciki, kallonta tayi a zaune a ƙasa ga kayan kwalliya nan duk an zubar a ƙasa, wasu kwalaben turaren ma sun fashe da sauri ta ƙarasa ciki ta rungumeta, nan Nabila ta saki wani kuka, bayanta Zeey ta shiga shafawa hankali a tashe, da ƙyar ta samu ta daina kukan tace “Faɗa mini meke faruwa? Me naji kina cewa kamar wai ciki ne dake?”
Kallonta tayi sai tayi murmushi tace “Ciki na ke min ciwo ji nake yi kamar bazan rayu ba.”
Kallon zargi ta tsareta dashi wanda hakan ya sata cewa “Allah da gaske nake yi wai ke da me kika ɗauka.”
Ajiyar zuciya Zeey ta sauke ta zauna a ƙasan tana cewa “Har hankalins ya kwanta dama na gama sanin in dai har kamar ke aka ce ciki gareki to tabbas wanda yayi cikin fyaɗe yayi miki don ko kusa da namiji ba kya zama bare har ta kai ki ga riƙe hannunshi to taya kenan zaki yi ciki, a hanya nasa a raina in dai shine to fyaɗe aka yi miki ko magani aka sa miki aka yi ba’a hayyacinki ba.”
Ƙeyarta ta talle tace “Lallai na kusa daina barinki kallon dramas ɗin nan da kike yi wato har kin tafi wani senario ɗin ma na daban? To ni ta ina zanyi ciki ke kin san ba maza nake kulawa ba.”
Yanayin Zeey ne ya canza ta sake bin ɗakin da kallo sannan ta tsare Nabila da ido sosai cikin kakkausar magana tace “No Aunty Nabila ɗazu ba haka kika ce mini ba, ce mini kika yi Zeey na shiga uku ciki ne dani kuma cikin…….” Sai wayar ta yanke. Nan da nan gaban Nabila ya shiga faɗuwa, kallon Zeey tayi wacce yanayinta ya canza sosai tace “Haka kika ce am 100% sure.” Yanayin Nabila ne ya canza gabanta ya shiga faduwa, kallonta sosai Zeey take yi itama yanayinta ne yake canzawa, meke faruwa? Aunty Nabila? How?
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA ƊAYA*
{61}