Sashe 44
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maida ƙofar Baqeer yayi kawai ya juya kekenshi tare da jinginar dashi a jikin ƙofar, kunnenshi sosai ya kasa a waje yana son sanin me suke tattaunawa. Dada ce tasa dariya tace “Ahh yau naga babban, haka kawai an turkeni can a lungun ɗaki ana neman rufeni da raina.”
Zeey ce ta buɗe baki cike da mamakin kalamanta tace “Dada ni dai ba ni bace kin san wanene.”
Harararta tayi tace “Amma ai kina kallo ana neman rufeni baki taro ni ba.”
Dariya Zeey tayi don tana son zolaya takaicinta ɗaya gidansu komai da gaske ake ɗaukan shi tace “Ke dai Allah Dada har da neman magana, ni ina bakin ƙofa ina ni ina shiga ciki kinkimo ki?”
“To ai da baki kinkimoni ba na kinkimo kaina, ke ni ba wannan ba wai kin tabbatar babu komai tsakaninki da Baqeeru?”
Ido ta zaro da sauri tace “Babu komai kamar ya?”
“A’a to naga ne kuna wasan kallon-kallo nan don kar a ganni a tsofe a ɗauka ban san komai ba.”
Mikewa Zeey tayi da sauri tace “Kinga Dada ki rabani da wannan zancen, ni kinga ma wucewa ta.”
Riƙo hannunta tayi tana miƙewa suka fito waje tana sake godiyar fruits data kawo musu Zeey ce tace “Dada kar kice wa Ya Baqeer nice na kawo in ba so kike yayi faɗa ba.” Dariya tayi tace “Don Allah ni dai in da hali ki cigaba da zuwa lokaci zuwa lokaci Baqeer na buƙatar wanda zai dinga faɗa mishi gaskiya, kuma na kula ke kaɗai ke iya faɗa mishi gaskiyar kai tsaye.”
Kallon Dada tayi jiki a sanyaye kafin ta ɗaga kai kawai alamar to, haka ta shiga mota idanuwanta na sake hango mata kallon da Baqeer yayi mata, ta tabbatar yaji zafin kalaman data faɗa mishi kawai don baya da niyyar kulata ne yayi shiru, amma tasan da yasan itace Zainab ɗin daya sani ta faɗa mishi magana haka babu shakka da tuni yaci mutuncinta.
Har ta isa unguwarsu zuciyarta na saƙawa da kwancewa, akan layinsu da zata shiga motar Bello ita kuma tazo fita, kallo ɗaya tayi mishi ta ganeshi ga Asiya nan zaune a gefen mota sai hira suke ana wani rirriƙe hannu cike da so da ƙauna, nan da nan takaici ya turnuƙeta, babu shakka mutanen nan basu da kunya don ranar da suka je gidan Maryam da Salim yake bata labarin wai Bello abokin Baqeer ne, ranar tayi mamaki har ta gaji ace wai abokinka shine zai ci amanarka irin haka, da saninta ta ɗan bugi gefen motarsu kaɗan wanda hakan yasa Asiya da Bello suka yi ɗan gaba kaɗan sannan suka yi baya, da sauri ya ɗago tare da riƙo gefen fuskarta yace “Sweetheart are you okay?”
Kukan shagwaɓa tasa tana nuna wuyanta wai ta buge da kujera, a fusace Bello ya fito ya nufi motar Zeey, wacce ke jiran fitowarshi dama, sun glasses tasa kafin ya ƙaraso ta ɗauki waya ta fara daddannawa.
Knocking glass ɗin motar yayi saitin inda take, Zeey ta zare glasses ɗin fuskarta kaɗan wanda ya bashi damar haɗa ido da ita sannan taja motarta tayi gaba ta barshi tsaye cike da mamaki, ganin gidan data nufa yasa ya kasa ƙarasawa don duk sun san gidan Suleiman Karaye ne wanda kaf unguwar babu wanda ya kai shi kuɗi bare yafi shi, bai san meye haɗinta da gidan ba amma yasan tunda yaga ta shiga to akwai dangantaka mai ƙarfi a tsakaninta dasu, Asiya har tutiya take yi akan layinsu ɗaya.
Dawowa mota yayi yana saka hannu a aljihu, ta kalleshi cikin sakalci tace “My heart me tace? Don na hango mace ce.”
Ya zauna yana dariya yace “Ta bada hakuri ashe bata kula bane.”
Turo baki tayi tace “Ni ya kamata kace ta bawa hakuri ai don ni ta buge, amma ƴar wacece na ganta a katuwar mota haka?”
Don kada ta rainashi yayi saurin cewa “Da alama wucewa tazo yi.”
Motar ya tada yana ɗan murmushi, ita ma murmushin tayi don restaurant zai kaisu cin abinci tace Habi tazo suje wai bata zuwa gayyar mayaudara.
*****
Gida ta shiga tana ɗan kaɗa key ɗin hannunta ko banza ta ɗan huce takaici don da ta fito sunyi magana lallai da sai taci zarafinshi.
Ɗakin Nabeela ta shiga taga ba ta nan, fitowa tayi ta nufi bangaren Mummy, nan ma bata nan, hakan yasa ta nufi kitchen, ma’aikatan gidan ne ke girki tana kallon banbar cikinsu tace “Iyani ina Mummy?”
Murmushi tayi tace “Tana nan a ciki don bata leƙo mu ba.”
Cike da mamaki ta sake komawa ciki tana mamakin inda take, don gidan tsit babu alamun mutum, ɗakinta ta nufa ga mamakinta Mummy ce kwance akan gadonta da alama bacci take yi, kai ta girgiza tare da sakin murmushi, tana mamakin yadda Mummy ke ji da ita, shi yasa a koda yaushe take tabbatar da ita ɗin ƴar gata ce, don sau da dama Mummy nace mata haihuwarta ce ta ceci rayuwarta wanda zuwa yanzu ta tabbatar da hakan, alwala tayi sannan tayi sallah haka nan take jin nutsuwa na sake ratsa zuciyarta, tazo kusa da Mummy ta kwanta itama nan bacci ya ɗauketa don kwanakin nan sam bata samun bacci mai daɗi.
Cikin barcinta ne ta fara mafarkin Baqeer wai ga mahaifinshi nan yana neman turashi daga saman dutse, zabura tayi ta miƙe zaune tana addu’a, nan da nan Mummy ta tashi ta rungumeta tace “Menene?”
Kai Zeey ta girgiza tana mamakin abinda ke damunta, anya kanta ƙalau kuwa? Anya baza taje ganin likita ba kuwa? Don wannan abinda take yi tabbas ba na masu cikakkiyar hankali bane.
*****
A hankali Baqeer ke buɗe ido yana rufewa yanzu kam ya tabbatar kalaman yarinyar nan yake son ji, ya tabbatar ba ƙaramin tasiri kalamanta ke yi a zuciyarshi ba, hakan yasa ya gurgura kekenshi ya zubawa kaɗan daga cikin takardunshi da Umma ta bada aka kawo mishi ido, ajiyar zuciya yayi tare da rike pencil a hanunshi yana kallon takardar sai dai ya kasa ɗora pencil ɗin akai bare har ya gwada yin zanen, to shi yanzu ya zai yi? In ma yayi zanen waye zai siya? Ina zai nemo mutanen da zasu gani su siya? Bayan wayarshi dake ɗauke da duk wasu muhimman abubuwa nashi an sace? Sannan Baba dake tallafa mishi akan harkokin shi shima yayi watsi dashi? Wannan dalilin ne yasa ya ajiye takardun sannan ya maida idanuwanshi ya rufe kafin ya buɗe, yanzu haka zaka cigaba da rayuwa? In Allah yaja kwanakinka fa? Haka zaka zauna komai sai an miƙo maka ba zaka tashi da ƙafafunka ka nema ba?
Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ya sauke haɗe da ƙara ɗaukar pencil ɗin don ya gwada yin zanen sai dai kuma ina ya kasa don ƙwaƙwalwar shi ce yaji ta zama blank kamar bai taɓa sanin yadda ake riƙe pencil ba, hannunshi kuma ya hau rawa yaji tamkar an ɗauki wani abu mai nauyi an ɗora akan hannun har ma ya kasa riƙe pencil ɗin ya sake shi ya faɗi a ƙasa. Wani irin ihu ya saki yana ƙara haɗe da riƙe kan shi da hannu bibbiyu. A sukwane Dada ta faɗo ɗakin tana cewa "kai Baqeeru lafiyarka ƙalau kuwa?" Ja tayi ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin yadda yayi watsi da takardun zanen nashi duk yabi pensiran ya kakkarya.
"Yau ni nake ganin abinda ya girmi kakata Saude, su kuma takardun da kayi watsi dasu laifin me suka yi maka? Anya kuwa Baqeeru shikenan haka zaka cigaba da rayuwa ba zaka sanyawa ranka haƙuri da dangana ba ka karɓi ƙaddararka da haƙuri da ikhlasi? Kai kenan kullum cikin ƙunci da baƙin rai ka ƙuntata rayuwarka ka ƙuntata rayuwar makusantan ka yau gashi har takardun ma baka ƙyalesu ba. Haba wannan wacce irin rayuwa ce, shikenan shi bawa Allah ba zai jarabce shi ba sai yace don me? Har ina murna ka fara samuwa kwana biyu shine kake nema ka koma ruwa, idan ka kassara rayuwarka a tunaninka ubanka yana da asara ne, uwarka da ƴan uwanka su zaka yiwa don kuwa ubanka yana da wasu ƴaƴan a yanzu ma ai ka gani yadda yayi watsi da kai ya koreka daga gidanshi bayan a lokacin da kake da lafiya yafi kowa cin moriyarka, to tun wuri ma idan zaka yiwa kanka faɗa ka ɗauki rayuwa a yadda tazo maka kasan cewa rayuwarka kai kaɗai zata amfana gara kayi.”
Sunkuyawa tayi ta tattare kayan daya watsar ta killace su a gefe tana cigaba da yiwa Baqeer faɗa, shi dai yayi bakam kamar bai san tana yi ba sai dai duk abinda take cewa yana saurarenta yana kuma gaskata duk abinda ta faɗa sai dai ya kasa daina jin ciwon yadda rayuwa tayi dashi, ya kasa yardar wa ranshi cewa shine rayuwa ta mayar dashi haka, yau shi Baqeer da yake ji da lafiya da ƙuruciya ne a kanannaɗe a keken guragu ya zama musaki, gurgu wanda ba zai ƙara amfanuwa da ƙafafunshi ba. Ko yayi ƙoƙarin cire abun daga ranshi sai wani dalilin yasa shi tunowa sai yaji gaba ɗaya rayuwar ta fita daga ranshi, ƙuncin zuciyar da yake fama dashi ya daɗu, sai yaji baya son ganin kowa kaɗaici kawai yake buƙata. Hannu yasa ya ɗauke hawayen daya gangaro daga idanunshi ya biyo kuncin shi, shikenan shi yanzu haka zai cigaba da rayuwa baya da wata mamora, zanen daya ɗauki dukkanin burikanshi na rayuwa ya ɗora akai na neman ya gagareshi yi. Gangarawa yayi ya rufe ƙofar ɗakin sannan ya koma kan katifarshi ya kwanta yana jin ina ma Allah zai ɗauki rayuwarshi da yaji daɗi ya rabu da dukkanin wasu ƙalubalen rayuwa da abinda ke cikinta.