Sashe 34
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*******
Baba tun daga waje yana packing Bashir ya taho da sauri ya sanar dashi Baqeer baya gidan, kai tsaye ɗakin su Baqeer ɗin ya nufa ya buɗe ƙofar ya shiga, ganin baya nan yasa ya kara shiga ciki yana bin ɗakin da kallo, babu komai na Baqeer agun sai kayan zanenshi, wanda hakan ya sake tunzuroshi ya jijiga kai tare da yin ƙwafa, ya fito ya nufi ciki, mai makon ya shiga ɗakin Fatima sai ya nufi ɗakin Abu duk da kuwa kwanan na Fatima ne, tana jinshi sanda ya shiga ta kauda kai dan ita yanzu ba wannan bane a gabanta, tunanin yanda zata samo kuɗi ta aikawa Baqeer takeyi, dan yana bukatar komawa asibiti, ta sani Baqeer nada kuɗi sai dai kaf kuɗin shi a hannun mahaifinshi suke, wanda yake ajiyewar kuma duk ya musu hidima dashi ita da kanenshi, idanunta ne suka sauka akan injin taliyar nan ba ɓata lokaci ta ƙira wata kawarta mai saida kayayyaki ta sanar da ita zata saida injin taliyarta amma tana san kuɗi hannu, dubu biyar tace zata siya haka Umma tace to tunda tasan ba yanda zatai.
Jamila kam an shaka an shaka lalai Abu banu munafuka irinta, maganin data bata ta ɗauko rai a ɓace ta sa a bin hanzu zargi ma take kila ma asiri ta bata na rabata da Mallan ita kuma ta dinga cusawa.
*****
A bangaren Baqeer kuwa, tunda ya shiga ɗaki yake jin komai na duniya ya sake fita a kanshi, Dada ta shigo tai ta magana bai iya ko furta kalma ɗaya ba, daga baya ma ta fara tunanin kamar baima san me take cewa bane, haka ta ajiye abinci ta fito, tagumi kawai tai tana mamakin yanda rayuwa ta juyawa Baqeer baya, yaran da ganinshi kaɗai ke sata farin ciki yau shine haka? Tun yana saurayi ya mata alkawari shi zai kaita Hajj ashe haka Allah ya shiryawa rayuwarsa?
Tana gani ya turo keken ya nufi bandakinsu dake waje, yanzu kam bai nemi taimakon kuwa ba haka ya dage ya matsa jikin toilet seat yai fitsari yai tsarki sannan yai alwala ya sake tura keken ya koma ɗakin, baisan kallanta dan ya tabbatar zuciyarta a karye take saboda shi, sallah yai daga zaune bayan ya gama ya fara rokar Allah yai gaggawar datse rayuwarshi ko ya samu sassaucin raɗaɗɗin da yake damunsa, bai ko kalli abincin ba balle yaci sai ruwa kawai dayasha. Yana zaune yana juyo Dada da yara a waje suna ƴar hira wanda ya tabbatar shigowa sukai, yau wayar ma airplane ya sakata kawai ya kunna karatun Qur'ani.
*****
Wajen azahar aka aikowa Fatima da kuɗi ita kuma ta bada injin taliyar a boye dan kar asan meke faruwa.
Sunyi waya da Dada ta sanar da ita halin da Baqeer yake ciki, Umma abin duniya ya sake taruwa ya mata yawa tana juyo Abu na shewa wai yau da gaza zatai girki, Jamila ce ta fito tana mata kallan sama da ƙasa tace "To kiyi da agwagwa ma mana meya damemu."
Abu ta dan wurga mata wani kallo tace "Ke kawata kar muyi haka dake ai ke cinya ma zakici."
Takaici ya kama Jamila tace "Hala a ɗakin da kuka shige ciki ranar kwanan Fatima baku tuna da hakkin wata kuke ci ba?"
"Ke bansan iskanci har yaushe kika fara maganar hakki? Kedai na kula da bala'i yau kika tashi ni zuciyata tas take yau shiyasa bana san husuma da kowa."
Tsaki Jamila tai ta wuce ciki ranta a matukar ɓace, Abu ta taɓe baki tace "Wannan kuma damuwarki ne."
Fatima kai kawai ta girgiza dan ita duk wannan abun ba shine a gabanta ba, addu'a kawai take Allah ya kawo wanda zata aikawa da kudin nan.
********
Zeey ce tsaye jikin shagon da Nabeela ke siyayya, takaici tsayuwar duk ya isheta ta kalleta tace "Kinga na kula baki shirya gama siyayyar nan ba, in kin gama ki kira driver ya maida ke gida zan ɗan je wani guri na dawo."
Mamaki ne fal ya rufe Nabeela tace "Ina zaki?"
Card ɗinta na atm ta mika mata tace "Gashi sai na dawo."
Bata jira amsarta ba ta juya da sauri ta shiga mota tai gaba, gidansu Baqeer tai parking shiru tai a cikin motar tana tunanin inta shiga tace me ya kawota?
Dabara ce ta faɗo mata akan zataje tace ai number jiya batai saving ba ashe, har zata fito sai kuma ta sake komawa ta zauna tana maida ajiyar zuciya kafin ta sake daurewa ta fito, da sauri ta shiga dan bataso Baqeer dake soron gidan ya hangota.
Abu na ta fige kaza sanda ta shigo ko kallo bata isheta ba balle tai mata magana.
"Nikam ke wacece wai? Dan jiya ma naga fitarki daga gidan nan."
Zeey kamar batasan da ita takewa magana ba tai sallama ƙofar ɗakin Umma, wata hamdallah Umma tai ganin Zainab, bayan sun gaisa ta amshi number Maryam ne Umma ta mika mata kudin tare da rokon taba Salim ya taimaka yakai Baqeer asibiti.
Da mamaki tace "Baya gidan ne?" Jin Umma na cewa dama ta rasa wanda zaije inda Baqeer yake.
"Yana gidan Dada a Mariri."
Cike da mamaki take kallan Umma sai dai bazata iya tambayarta komai ba, nan Umma ta bata number Salim kamar tace Umma tabar 5000 ɗin zata bada amma tasan halinta tabbas ta faɗa yanzu za'a juyo faɗan ta, a cikin mota ta zauna tai shiru tana kallan kuɗin ko dai ta kara musu ne ba tare da sun sani ba? Amma in Umma taji kuma tace ba ita bace ba fa? Shafar fuskarta tai kafin ta ƙira Salim a waya ta sanar dashi sako ne Umma ta bada zata bashi.
Nan yace gashinan zuwa, taɗan gangara cikin layin tai parking sannan ya fito.
Kamalu dake ta sauri a babur ɗinsa zasuje kallan kwallio ɗakin wani abokinsu, kamar a mafarki yaga Roshni ɗinsa ta fito ta tsaya kusa da Salim, baiyi auni ba yaji yabar kan titi saura kadan ya kifo daga kan mashin ɗin, da sauri ya tsaya yana waiwayensu, ganin murmushi yai a fuskar Roshni nan fa kishi ya turnuko shi lallai Salim dama ya tsaneshi ya aka yi ma yasan Roshni ɗin shi?
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*
*PAID BOOK*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA ƊAYA*
{21}
Cike da sauri Kamalu ya fara ƙoƙarin tsallaka titi ganin Salim na neman shiga motar, ganin da gaske babur ɗin babu dama yayi kwana dashi yasa ya jingineshi a titi ya tsallaka da gudu yana neman zuwa inda suke.
Zeey ce ta kalli Salim bayan ta mika mishi 10k wanda ta ƙara 5k akai tare da fatan kada Allah yasa Umma ta gane, ta kalleshi tace "Gidan Maryam ɗin kusa ne?"
Ya sauke wayar da suka gama da ita akan kai Baqeer asibiti, sannan yace "Eh ba nisa sosai zan hau mashin naje na amshi motar na kai shi sai na maida mata motar gida." Kai ta jinjina kafin tace "Muje nayi dropping ɗinka tunda in ka tafi da motorcycle ɗin ma dole ka ajiye."
Daɗi ne ya kamashi don dama ba wani man kirki gareshi a ciki ba hakan yasa ya shiga gaban mota ita ma ta shiga, ta kunna mota suka fara tafiya.
Kamalu sai haki yake yi wurin gudu sai dai kafin yazo yana gani suka yi gaba, iska ya nausa cikin matuƙar ƙunar rai yace "Wallahi Salim sai na fasa maka baki sai kasan motar Roshni ɗi ta ka shiga shegen yaro da shishigin tsiya."
Juyawa yayi yana tafe yana zage-zage da masifa, turus yayi a gefen titi ya fara waige-waige yana neman inda ya ajiye babur ɗin shi, mamaki ne duk ya gama rufeshi ya rikice a wurin yana waige-waige sai dai babu babur babu alamarshi, hankali a tashe ya nufi wani mai saida yalo yace "Yayana don Allah kaga babur ɗina?"
Yaron ya kalleshi yace "Yaushe na zama yayanka? Sannan wani babur kake magana?"
Kamalu zufa ce ta fara keto mishi yace "A daidai nan na ajiye don Allah yi tunani kaga wani ya ɗauke?"
"Wa zai ɗauke maka babur in har key ɗin na hannunka?"
Nan ya laluba aljihunshi ashe ko key bai cire ba? Yaron ya kalleshi yace "To Allah ya kiyaye."
Gaba ɗaya Kamalu kanshi ne ya ɗauki zafi ya fara bin hanya yana neman babur sai dai babu shi babu alamarshi. Haka nan ya haƙura ya nufi gida kamar wanda aka yiwa dukan tsiya.