← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 168

Sashe 115

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*******
Tsugunnawa Bello yayi ya haɗe hannayenshi alamun roƙo yana murza hannun yana cewa “Sir plz help me,” yayi maganar cikin roƙo, wani kallo suka yi mishi mutanen dake zaune a office ɗin, ɗayan wanda kana gani kasan bature ne, ya kalleshi yace “Am sorry but you have to go back to your country, we brought you here to sponsor you but unfortunately you couldn’t pass any test and at the end we realised everything you said was false.”
Gabanshi ne ya ƙara faduwa, sam ya manta karatunsa da passport ɗinshi suna daban-daban ya saka, su sun yi visa da sunan Muhammad Bello Bala, sai dai bayan yazo ya faɗi gwaje-gwajen da suka yi mishi suka tausaya mishi akan to ya kawo karatun degree da yace yayi in yaso su nema mishi wani aikin, sai dai yana kawowa suka ga Bello Bala Jogana, wannan dalilin yasa suka ce sato takardun yayi, duk yadda yake fahimtar dasu bai sa sun fahimceshi ba, gashi maganarsu ta turanci da sauri suke yi shi kuma ba fahimtarsu yake yi sosai ba. Wani ne ya kalleshi yace ya shirya wai ƙarshen satin nan zasu maidashi gida in kuma ya cigaba da zama zasu lalata mishi permit ɗinshi na zama wanda ko aiki bai isa ya samu ba. Haka ya fito ya shiga masaukin da aka bashi da ƙyar kanshi na wani irin sarawa saboda ɓacin rai, zama yayi a bakin gado ya zuba tagumi yana tunanin abun yi, gaba ɗaya bai yi nisa da tunani ba sai ga wayar Asiya. Wani ƙululun baƙin ciki ne ya kamashi ya ɗaga fuskarshi a tamke, ba tare da yace komai ba.
“My love baka turo mini kuɗin ba bayan mun yi magana rannan, sannan Habi ta tafi wai ta gaji so take ta koma wurin Inna, shine nake so in ka turo kuɗin zan ɗauki masu aiki biyu kafin ka zo ka ɗauke ni don sam zaman garin nan ya isheni wallahi,” ta ƙarasa maganar cikin kashe murya.
Wata irin iska ya furzar yace “Ni kam Asiya hala baki san komai ba sai kisan kuɗi ko?”
“Ba dai suma cewa zaka yi ba zaka bani ba?”
Ranshi ne ya ƙara ɓaci don dama ƙoƙarin danne ɓacin ranshi yake yi, a fusace ya kashe wayar don yana ji kamar idan ya cigaba da yi mata magana to lallai zai iya furta kalmar sallama don shi dai ta gama kai shi bango tunda yake da ita bata taɓa tambayarshi ya yake ba? Yana da kuɗin da take so ko babu, amma a iya saninta da Baqeer lokacin suna soyayya kullum ta Allah in suka yi waya da safe sai ta tura mishi text na soyayya wanda a zamanshi da ita har suka yi aure bata taɓa yi mishi text ɗin soyayya ba, sai na godiya in yayi mata wata kyautar.

******

Baqeer shiru yayi yana tunani meke faruwa da Zee? Don da alama akwai abinda aka yi mata sosai sannan menene laifinshi? Kashe wayar data yi ya tsaya mishi a rai yana ganin kamar shima ya ɓata mata rai, tambayar data yi mishi na son sanin matsayinta shi ke sake dawo mishi, ko dai ya sanar da ita yana sonta ne? Iya kaci in bata sonshi tace a’a sai dai baya son ya zama sanadiyyar rabuwar zumuncin Dada da ita sannan Maryam da ita. Shafar sumar kanshi yayi sannan ya turo kekenshi zuwa waje Dada ya kalla dake saka maggi cikin ɗan wake yace “Dada yau kuma ɗan wake kika yi?”
“Ina fa aiko mini aka yi daga maƙwabta, ga naka can kaima na ragema, yanda yayi daɗi nake ta tunani ina ma Zainabuwa zata zo.”
Murmushi yayi yana ɗaukan kwanon yana cewa “To ai sai ki aika mata ni dai ci zan yi don ya bani sha'awa.” Wani kallo tayi mishi tace “Nikam Baqeeru son Zainab kake yi ko?” Gabanshi ne ya faɗi ya maida murfin kwanon ya rufe yana cewa “Dada me kike nufi? Wani irin so ana zaune ƙalau?”
“In ba haka bane abar maganar amma ni haka kawai nake gani.” Sake buɗe kwanon yayi yana cewa “Ku dai tsofaffi da son zancen aure kuke,” yayi maganar yana kifkif da ido.

******

Mummy ce ta goge hawayenta, Inna na gefenta itama tayi shiru tana tunani, daurewa tayi tace “Aikin gama ya riga ya gama yanzu abun yi zaki yi tunani ai ke mai wayau ce sannan ba kya rasa mafita duk abinda ya shige miki duhu.
Wani kallo ta yiwa Dada cikin magana mai ɗan sauti tace “Kin san da haka shine kika biye mata kuka zo kuka janyo mana tozarci? Sannan sanda kika yi magana sam babu alamun mamaki a fuskarta dama ta sani ne ko me?” Inna ta kalleta yanayinta ya ɗan canza tace “A’a banaji gaskiya.”
Mummy ta girgiza kai tana tuno abubuwa da dama da Nabila take faɗa mata especially akan Zainab lallai ta sani kawai dai nunawa take yi kamar bata sani ba, Inna ce ta katseta da cewa “Bana ji gaskiya da ta sani da ta nuna.” Kai Mummy ta girgiza tace “Ta sani shi yasa ta ƙwallafa rai da Kabir so take yi ta tozartani.”
Wani kallo Inna ta zabga mata tace “Kada ki kuskura ki yi mata wannan  ƙazafin, zan ɗauketa mu koma gida ke kin san me zaki yi ki shawo kan komai,” tayi maganar tana miƙewa, har ta kai ƙofa Mummy tace “Shi yasa nake cewa ki dinga sawa bakinki linzami yanzu don Allah me kika ja mana?” Tayi maganar tana bin Inna da kallo. Waigowa tayi ta kalleta sai bata ce komai ba kawai ta fita ta ja ƙofar. Mummy ta share ƙwalla tana murza bayan hannunta tana cewa “Duk abinda na gina shekara da shekaru rana ɗaya mahaifiyarka ta ruguza ma shi? Da wani ido zan kallesu? Da kuma wani ido zasu kalleni?” Saman kanta kawai ta riƙe tana jin takaicin abun nan.

Daddy duk yadda yake ƙoƙarin ƙwaƙwalwarshi ta ɗauki abinda ke faruwa ya kasa, har ya tafi zai je guest house ɗinshi ya fahimci ba zai iya zama ba tare da an cire cikin nan a gabanshi ba.
Nan yace driver ya sake maidashi gida don meeting dai an gama shi tuni dama guest house zashi, suna zuwa suka ga su Inna sun fito zasu tafi, cewa yayi su tsaya a gabansu bayan sun tsaya ne ya kalli Nabila yace “Shigo!” Kallon Inna tayi a tsorace Inna ta kalleshi tace “Alhaji kayi haƙuri don Allah.”
Magana zamu yi da ita ke ki wuce gida zan ajiyeta in mun gama, haka ta shiga motar a tsorace don babu alamun wargi a fuskar Daddy balle ta bashi hakuri, gaba ta shiga kusa da driver ko sake kallon Inna bai yi ba balle ya sa a kaita gida, sai driver daya kalla yace “Muje asibitin Zahir” daga haka bai ce komai ba, gaban Nabeela ne ya faɗi ta waigo hankali a tashe zata yi mishi magana, wani mugun kallo yayi mata wanda ya sata maida kanta gaba, gabanta na wani irin faɗuwa wanda take jin kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito. Idanu kawai take ƙiƙƙiftawa akan titi, a hankali zufa ke ɗan karyo mata tana jin wani dummm bata gama fahimtar me ke faruwa da jikinta ba sai gani tayi an zo asibitin don dama ba wani nisa gareshi ba zuwa gidansu. Fitowa Daddy yayi sannan ya kalleta yace “Wuce gaba saboda bana son a ganeni kiyi gaba ina binki a baya, sannan wallahi kika kuskura kika yi wani abu ko magana da zata sa hankalin mutane yazo kan mu sai ranki ya ɓaci.” Bakinta na rawa ta ɗaga kai don tasan  bata isa tayi magana ba, haka suka wuce tana tafe ƙafafuwan ta na sake yin sanyi, nauyinsu na ƙara tafiya, kuzarinsu na ƙara raguwa.
Waya yayi mishi ya sanar dashi ya iso hakan yasa ya turo secretary ɗinshi akan ta shiga dasu, sun shiga suka sake gaisawa, Nabila na takure gefe ɗaya kamar ƙuli, bayan sun gama magana ya sanar dashi ciki gareta yana so a cire mata, ƙanwar matarshi ce sai tsautsayi ya afka mata tayi ciki, ya ɗan jinjina abun sannan ya umarceta da tazo su shiga ɗan kewayen cikin office ɗin kaɗan don yayi scanning wanda zai bashi damar sanin taimakon da zai yi mata ba tare da matsala ta afku ba.
Nabeela ta sake kallon Daddy wanda ya sake haɗe rai yace “Magana ake yi miki ko?” Ta ƙarasa wurin kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, idanunta kuwa nan da nan suks fara zubar da ƙwalla, keɓantaccen guri ne a cikin office ɗin ansa labule an kulle ta yadda na waje ba zai iya ganin meke faruwa ba, haka ta gyara zaman skirt ɗinta ta hau saman gadon da Dr ya umarceta ta hau, hawayenta ya kasa daina zuba, haka tana gani ya fara sa mata gel sannan yasa abun scanning akan cikinta, mamaki ne ya kamashi ganin duk inda ya duba a mahaifarta babu ciki babu alamunshi, da mamaki ya kalleta yace “Ya aka yi kikasan kina da ciki?”
Gaban Nabila ne ya faɗi tace “Na'am?”
“Kinyi pt ne?” Yawun bakinta ta haɗiya da ƙyar tace “Eh!”
“Kuma positive ya nuna?” A tsorace ta ɗaga kai.
Cike da mamaki ya sake yin scanning yace “Amma babu alamun ciki babu ma alamun mahaifarki ta taɓa ɗaukan ciki.”
Daddy dake zaune mamakin kalaman Dr ya kamashi a fusace ya miƙe yace “Me kake nufi?”
Dr yana scanning yana cewa “Gaskiya bata da ciki ban san ya aka yi kuka yi tunanin tana da ciki ba.”
Tsoro ne ya rufe Nabila tayi saurin durowa daga kan gadon ta zube ƙasa tace “Dr ka duba sosai wallahi ciki gareni, don Allah kada kace babu, don sai dai in zubewa yayi ban sani ba……”
A ƙufule Daddy ya yaye labulen ya kalleta yace “Kina son kice mini cikin da kika ce kina dashi minti goma sha biyar da suka wuce shine ya  zube ba tare da kin sani ba?”
Dr ne ya kalli Daddy yace “Yallabai ka kwantar da hankalinka bari muyi bincike.” Yayi maganar yana fita daga office ɗin, wani gigitaccen mari taji an ɗauketa dashi wanda yasa ta ƙarasawa ƙasa riƙe da kuncinta…….

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
Chapter 115 · 0% Book details