← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 168

Sashe 52

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

******
Bello ne ya kalli Babanshi yace “Baba maganar Asiya, kaga dai ance za’a sake kiranmu Abuja akan aikin da muka yi sannan tunda ni banci na ɗaya ba sun ce zamu je a bamu wasu ayyukan da zamu yi wanda za’a dinga tura musu suna siyarwa a ƙasar su ana dawo mana da kuɗin kafin lokacin tafiyarmu ƙaro karatun yayi, shi yasa nake ganin ba sana’ar data fi wannan a yanzu, don Allah aje gidansu Asiya ayi maganar aure.”
Wani mugun kallo Baban yayi mishi yace “Wai ni kam Bello kanka ɗaya dai ko? Ina ce kai da kanka ka sanar dani Baqeer shine saurayin Asiya kwanakin baya da na ganku a ƙofar gidan kace kai rakiya kayi?”
Bayan kanshi ya shafa yace “Eh shine amma yanzu sun rabu ai.”
“Kai bana son shirme don Allah, kai da hankalinka yarinyar da ta rabu da saurayinta saboda ƙaddara ta afka mishi ita kake son aure? To ahir ɗinka ko ba don haka bama bazan bari ka auri budurwar abokinka ba, sannan Badaru kana gani yadda yake tijara tun bayan faruwar abun nan baza ka zo ka sake jaza min case dashi ba.” Yana kaiwa nan ya fita ranshi a ɓace, Goggo mahaifiyarshi ce ta kalleshi tace “Bello don Allah kada kaci amanar Baqeer yaron nan ya taimakemu a rayuwa kada kayi abinda alhakinshi zai sa komai da kake taƙama dashi ya tafi.” Ita ma tana kaiwa nan ta wuce, miƙewa yayi yace “Gobe wurin Baffa zan je ai dai kuna jin maganar shi dukanku idan ya sakaku baku isa kuce a'a ba.”

******
Dada ce ta harari Baqeer tace “Haka kawai zaka tada mini hankali.”
“Dada nifa ba yaro bane, sannan kin san dai babu inda zanje kema, kawai abubuwa ne suka yi yawa a kaina na fita don na samu nutsuwa, kiyi haƙuri idan na tayar miki da hankali.”
“Wayar tawa ce babu kati babu yadda zanyi na kira ka bare naji kana ina, gashi babu kuɗi  a hannuna a ƙarshe sai wurin Talatu na shiga na ari dari nasa aka siyo mini katin na kiraka.”
Kallon tausayi yayi mata tabbas ba zai cigaba da zama haka ba. Kallon almajirin yayi wanda bai ma san mai zai bashi ba na godiya, Dada ce ta ɗauko fruits ɗin nan lemon da ayaba ta bawa yaron tana yi mishi godiya, shima godiya yayi ya amsa ya juya ya fita.

*****
Baba yau a fusace ya kwana washegari ma ko abinci bai ci ba ya ɗauki motarshi ya fita, jikin Abu ne duk yayi sanyi ta fito tsakar gida tana daka garin maganin mata tana yi ranta na ɓaci, Kamalu ne ya shigo yace “Hajiya ya bani makullin mota zan ɗan je yawo.”
“Kaima dai kasan Babanka ya fita da ita, baka ga bata ƙofar gida ba?”
Bashir ne ya fito da alama makaranta zai je, Kamalu yace “Kai Bashir bani kuɗin hannunka.”
Kallon mamaki yayi mishi ya kalli ɗari biyu  da Jamila ta bashi yace “Ai kam kayi hakuri amma bazan baka ba gaskiya babu dalilin da zai sa na baka kuɗin da zanyi amfani dasu na tafi makaranta.”
“Kai don gidanku ni kake yiwa magana a haka?”
A ƙufule Bashir yace “Kayi haƙuri amma bazan bada ba.”

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer🦼
#RayuwadaKaddara
#Hawayena
#Samudarashi
#UmmuAsgar
#Ayushermuhd

*BAQEER*🦼
     *NA*

*UMM ASGHAR*
Da
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA BIYU*

{32}

Cakuma ya kaiwa wuyan rigarshi ya shake shi yana cewa "Dan uwarka ba zaka bayar ba fa kace? Ni kake faɗawa ba zaka bayar ba don ka raina ni ko kuwa don kana ganin kayi tsawon ƙafa ka kere ni a tsawo? Idan da wancan nakasashen ne yace ka bashi kuɗin hannunka zaka faɗa mishi haka ne?" Da ƙyar ya iya ɓanɓare hannayen Kamalu daga wuyanshi domin kuwa ba ƙaramin shaƙa yayi mishi ba. A sakarce ya kalleshi yace "An hana ka ɗin sai dai kayi duk abinda zaka yi amma ba zan ɗauki kuɗina da zan tafi makaranta ba na baka alhalin ba wani abu zaka yi dasu ba watakila ma sigari zaka saya, kuma da kake cewa da Yaya Baqeer ne bashi zan yi ai shi Yaya Baqeer sai dai a ƙi shi don wani abu amma dai ba don halin shi ba don kuwa kowa a gidan nan ya sani abun hannunshi bai rufe mishi ido ba kuma babu ruwanshi da bambancin da Baba yake nunawa idan ya tashi alherin shi gaba daya yaran gidan nan yake hadawa yayi wa kowa shine har kake haɗa kanka dashi bayan kai baka taɓa iya morawa mutum da ko sisi sai dai ma kai ayi maka.”

Ai kamar ya tunzura Kamalu ya kuwa hayayyaƙo mishi yana ƙoƙarin kai mishi duka yana cewa "Ni kake faɗawa wannan maganar don uban uwarka?" Cikin hanzari Jamila ta fito daga ɗakinta tana cewa "Rashin mutuncin naka har ya kai ka zagi ubana Kamalu? Akan ya hanaka kuɗin shi kake yi mana wannan ɗiban albarkar?" A fusace yace "Shi baki ji abinda ya faɗa mini ba sai ni don na rama zaki taso ki shigar mishi.” Ƙwafa tayi tace "To uban uwarka Abu ka zaga ba dai ubana ba ato.” Abu naji an haɗa da ubanta ta taso da tata masifar itama alhali da tana zaune a gefe tana kallon rashin mutuncin da Kamalun yake yi bata hanashi ba.

"A'a fa Jamila wallahi banda tsikarin uwar miji da taɓarya, saboda me zaki sako da ubana ko kin ji na saka musu baki tunda suka fara abinsu da zaki sako dani?”

"Au ashe babu daɗi, ba'a gabanki ɗanki ya zagi nawa uban ba kin hanashi ne? Ko kin yi mishi faɗa, to wallahi ba ubana ya zaga ba sai dai naki, haka kurum don yana ji da tijara sai ya huce akan yarona ko kuwa sai kada yaje makaranta tunda ɗan gwal wanda bai san daɗin ilimi ba ya buƙaci ya bashi kuɗin?” A take faɗa ya kaure a tsakaninsu har suna nema su kaiwa juna duka, sai Umma ce ta fito daga ɗakinta ta rabasu jin hayaniyar tayi yawa, da ƙyar suka haƙura kowacce ta koma ɗakinta suna faman zage-zage. Komawa Bashir yayi ɗakin Jamila yana bata haƙuri kafin ya fito ya tafi makarantar ranshi duk babu daɗi.

*****

Yau ta tashi cikin farin ciki ganin tun jiya suke daɗi da maigidan nata. Sandwiches tayi musu sai ta dafa milk tea ta zuba a flask, a gefe ga farfesun kayan cikin rago da ta dafa tun jiya da dare yau kawai ɗumamawa tayi. Kwalliya tayi cikin wata riga da tabi jikinta ta lafe duk wasu curves na jikinta suka bayyana, rigar iya kacinta gwiwarta sannan siririn hannu gareta guda ɗaya ɗaya hannun babu komai don haka ko bra bata saka ba. Tunda ta fito yake binta da kallo domin kuwa shigar da tayi ta tafi dashi ba kaɗan ba, a ƙarshe ma kasa haƙuri yayi ya janyota ya zaunar da ita akan cinyarshi yana sunsunar sassanyan ƙamshin turaruka da tayi amfani dasu. Haka suka ci abincin a cikin nishaɗi yana saka mata a baki itama tana bashi, ɗagowar nan da zata yi kawai taga Baffa(surukinta) tsaye a kansu. Wata irin zabura tayi sai kuma ta koma ta cukuikuye a jikin Baban Aareef kamar mai ƙoƙarin komawa cikin shi. Shi kanshi sai da yaji babu daɗi da yadda Baffan yayi musu tsaye aka yana bin su da wani irin kallo. Murya a cunkushe yace "Baffa barka da asuba," har wannan lokacin Maryam na naɗe a jikinshi baƙin cikin duniya ya lulluɓeta saboda ganin da uban mijin nata yayi mata da shigar da ko nata uban bai kyautu ya ganta da ita ba.

A ɗage ya amsa mishi "Barka kadai, kana nan mace ta sanya ka a gaba tana zuba maka karuwanci kai kuma sai faman yage baki kake yi kamar wani sakarai ina ta kiranka a waya kaƙi ɗagawa?” Murya a shaƙe yace "kayi haƙuri Baffa, amma don Allah ka fita daga waje sai na fito na sameka" ranshi idan yayi dubu ya ɓaci don ko shi yau abinda Baffan yayi ya ɓata mishi rai. Sai da ya watsa mata wani mugun kallo da bata ma san yana yi ba don ta ɓoye fuskarta akan ƙirjin mijinta bama ta son ta ɗago bare taci karo da fuskarshi sannan ya fita. Sai da ya tabbatar Baffan ya fita sannan ya ɗagata daga jikinshi yace "Ina zuwa please, bari naje naji me Baffa yake so.”

Ko kulashi bata yi ba don haushi ganin kamar ma bai damu da yanayin da Baffan yazo ya samesu ba. Yana fita ta fashe da wani irin kukan baƙin ciki tana jin takaicin yadda uban mijinta baya kunyar faɗo musu ɗaki ko tunanin yanayin da zai iya riskarsu a ciki baya yi gashi kuma Baban Aareef baya kallon hakan a matsayin wani abun damuwa idan tayi magana ma har saɓani suke samu akan hakan. Har ya dawo ciki bata daina kukan ba, duk sai taji farin cikin da take ciki ya gushe takaici da baƙin ciki duk sun mamaye mata zuciya. Tsayawa yayi yana kallonta ganin tana kuka sai kuma ya taɓe baki yace "Shi kuma kukan da kike yi na menene? Ko kuwa dai jin daɗi?” Ko ɗaga kai bata yi ta kalleshi ba ta cigaba da kukanta shima sai yayi kamar bai fahimci dalilin kukanta ba yace "to ni zan fita nasan dai babu wata matsala tunda komai da za'a buƙata akwai, idan lokacin tashin Aareef yayi sai kije ki ɗauko shi" ya miƙa mata kuɗin napep.
Chapter 52 · 0% Book details