Sashe 78
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sassafe ta shirya yau gidan Dada zata je ta yini, da ƙyar Mallam Badaru ya barta ma taje don da cewa yayi me zata je tayi? Sai da tace mishi "Dada ce fa nace maka zan je na gani mahifiyata ba wata can daban ba" sannan ya amince. A cikin kuɗin da Baqeer ya aiko mata ne tayi cefane tayi musu soyayyiyar miya da zata jima bata lalace ba, sauran abinda ya rage kuma ta saya musu kayan shayi dasu sabulun wanka dana wanki sai omon wanke-wanke, dama ta saba yiwa Dada irin wannan sayayyar miyar ta kai mata duk lokacin da zata je ta duba ta don ma ba kasafai Badaru ya cika barinta taje ba sai kuma ya sameta ba mai yawan son tashin hankali bace don haka take haƙuri duk da ba daɗin hakan take ji ba ace suna gari ɗaya da mahaifiyarta amma sai ta ɗauki wani tsawon lokaci kafin taje ta gaisheta. Sai data duba jakarta ta tabbatar takardar filin na nan a inda ta ajiyeta kafin ta ɗauki ledar kayanta ta fice. Sallama tayi wa su Abu da Jamila wanda ke ta gulma ganin gana soyayyar miya, da sun san Baqeer ke bata kuɗi yanzu kuwa sun tabbatar kuɗin kujerunta tasa a gaba take miya, ita dai ta fita tana jin ɗokin son sake saka tilon ɗanta a idanunta bayan wani lokaci da suka ɗauka ba suga juna ba sai dai suyi magana ta waya abinda bai taɓa faruwa ba kenan a tarihin rayuwarsu tun daga haihuwarshi har zuwa girmanshi sai fa yanzu da tijarar Mallam Badaru ta raba su. Ƴar tafiya kaɗan tayi ta samu adaidata sahun daya ɗauketa har ƙofar gidan Dada. Da sallama ta shiga gidan fuskarta ƙunshe da fara'a ta tsantsar farin cikin daya kasa ɓoyuwa. Daga cikin ɗaki Dada tace "Muryar wa nake ji kamar ta Fatima?"
"Nice Dada" ta amsa tana nufar ƙofar ɗakin.
Cikin barci yaji kamar muryar Ummanshi suna gaisawa da Dada, ai kuwa zumbur yayi ya miƙe zaune yana jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarshi. Wheelchair ɗin shi ya janyo ya daddafa ya hau kai ya zauna yana garata, wai kuma sai da yaje baƙin ƙofar ɗakinshi sai yaji ba zai iya fita ba, haka nan yaji tausayin kansu shi da Umman ya kamashi, yasan wannan tsawon lokacin da suka ɗauka a mabanbanta wuri ba ƙaramin dauriya da haƙuri tayi ba. Kasa fita yayi ya tsaya daga nan yana jin sautin muryar Umman da yayi kewa iya kewa. Ita kuwa Umma suna gaisawa da Dada hankalinta na wajen ɗanta kara da kawaici ne kawai yasa ta kasa tambayar inda yake sai kallon ƙofa take yi a kaikaice tana zuba idon ganin ta inda zai ɓullo.
"Yana ɗaki watakila bacci yake yi tunda kika ga bai fito ba" Dada tace mata don tana lura da yadda take satar kallon hanya tasan Baqeer idanunta ke kwaɗayin gani. Kunya ce ta kama Umma ta sunkuyar da kanta ƙasa ganin Dada har ta fahimci ɗokin son ganin Baqeer da take yi. Sai ta kasa cewa komai sai da Dada tace "Ki shiga ki ganshi mana ai ya samu sauƙi fiye da lokacin da ya dawo nan, ko daga walwalar da ya samu ma bare da yarinyar nan Zainabu ta haɗashi da likitan ƙashi yana zuwa can asibitinsu yana dubashi.”
Kallon Dada Umma tayi tace "Zainab ɗin na yawan zuwa nan ne?" Tace "Ai bata kwana biyu bata zo ba yarinyar kirki mai yawan barkwanci da sanin darajar mutane, da badan ita ba Baqeer da har yanzu banajin zai dawo daidai.”
Jinjina kai Umma tayi har yanzu ta kasa daina mamakin jin wai Zainab ce take yawan kawo musu ziyara har ma da taimakon da ta yiwa Baqeer bayan tasan ƴar tsamar dake tsakaninsu wanda abu har iyaye ya haɗa, wanda tashin hankalin da akai a shekarun baya, sai dai ganin yanzu sun girma kila shi yasa suka zubar da duk wasu abubuwa na yarinta. Tashi tayi ta shiga ɗakin nashi sai ta ganshi daga bakin ƙofa, haka nan taji wani irin rauni ya saukar mata kawai sai ta fara hawaye, tana son Baqeer a cikin ƴaƴanta tana kuma tausaya mishi saboda dattijon yaro ne da bai ɗauki rayuwa da girma ba, mai mayar da damuwar wasu tashi shi yasa ya zame musu bango abun jinginarsu daga ita har ƴan uwanshi, ya ɗauki dukkanin wasu damuwoyin su ya mayar dasu nashi, bai taɓa bari sun yi kukan rashin wani abu ba bakin gwargwado yana kyautata musu. Tsugunnawa tayi a gabanshi ta riƙo hannayenshi a cikin nata tace "Ya jikin naka?" Ɗaga mata kanshi yayi alamun amsawa don haka nan yaji bakinshi yayi mishi nauyi ya kasa furta ko kalma ɗaya. Cikin rawar murya tace "Ina can ina ta fama da kewarka kai kana nan kana cigaba da rayuwarka cikin kwanciyar hankali.” Hannu yasa ya share mata hawayen dake ta faman zuba daga idanunta sun kasa tsayawa tunda ta ganshi. "Nima ina cikin kewarki Umma nayi kukan rashinki a kusa dani sau babu adadi, sai dai nasan in na cigaba da zama cikin damuwa sai kin fini damuwa.” Tausayinshi ne ya ƙara kamata ta ɗan yi murmushi na ban tausayi. Zama tayi suna hirar sai tambayarta lafiyarta yake yi tana ce mishi tana nan ƙalau sai dai ya kasa yarda don sai yaga gaba ɗaya ta canja mishi, sai yaga kamar walwalarta ta ragu shi idan ba idon shi nema ke faɗa mishi ƙarya ba da sai yace har ramewa yaga tayi. Sun jima a ɗakin kafin ta turashi su koma wajen Dada da bata katse musu hira ba ta ƙyalesu su ga na sosai don tasan sun yi kewar juna.
Yau yini suka yi cikin farin ciki da annashuwa bare da Umma ta dafa musu shinkafa suka ci da miyar data kawo musu sai Baqeer yaji kamar lokutan baya da suke tare a gidansu da sam baya iya cin girkin kowa idan ba na Ummanshi ba shi yasa ko ba ita bace da girki kullum ne sai ta girka mishi nashi abincin daban don a cewarshi su Abu basu iya girki ba baya iya sakewa yaci abinci ya ƙoshi idan su suka dafa.
Takan daɗe bata je taga Dada ba amma duk ranar da taje bata barin gidan sai tayi mata kwalema ta share kowane lungu da saƙo na gidan ta goge na gogewa ta wanke na wankewa, kyakkyawan gyara take yi mata irin wanda za'a kwana biyu gidan bai haɗa datti ba. Sai data gama duka waɗannan aikace-aikacen don har wankin kayan sakawar Dada sai da tayi sannan ta fito da takardar filin ta miƙawa Baqeer. Karɓa yayi yace "Takardar miye wannan ɗin Umma?"
"Kai dai ka buɗe ka gani mana" tace mishi. Sai da ya buɗe sai yaga takardar filinshi ce dake wajen Baba. Ɗan yamutsa fuska yayi yana kallonta yace "Ki mayar mishi da ita Umma don bana buƙata.” Kallonshi take yi itama ta kuwa ɓata rai tace "Bazan mayar mishi ba domin kuwa fili dai naka ne sunanka ne a rubuce a jikin takardar ba nashi ba, sannan da kuɗin ka aka saya bashi ya saya maka ba to na miye kana da buƙatar kuɗin don ka gina rayuwarka sai kace baza kayi amfani da kadararka ba bayan amfanin ajiye kadarar kenan.”Juyawa tayi ta kalli Dada sai tace "Takardar filin shi ce daya saya na kawo mishi a saka a kasuwa idan Allah yasa aka dace da samun masu saye ba sai yayi amfani da kuɗin ya biya kuɗin makarantar koyon ɗinkin da yake son shiga ba ga sayen keken ɗinkin tunda yace dole sai dai yayi amfani da mai aiki da wuta wanda baya buƙatar sai ya takura ƙafafunshi wajen taka keken da dai sauran ƴan matsaltsalun daka suka mishi.” Dada tace "Haka ne,” tana jijjiga kai "Ai daɗin sayen kadarar a ajiye kenan dama.”
Yana jin su sai dai ya kasa yin musu dasu duk kuwa da yadda baya son karɓar filin, shi duk wani abu daya danganci Baba ma ba son shi yake yi ba shi yasa bai yi wani farin ciki da ganin takardar filin nashi ba dashi a mance ma ya manta yana da wani fili don tun lokacin da aka saya takardun na wurin Baba ba kuma su ƙara yin maganar fiin dashi ba. Dada ya miƙawa takardar filin yace ta ajiye a wurinta don shi ko ganinta ma baya son yi, haka Umma ta ƙara gyara gidan tasa turaren wuta. Sai can da yamma sannan tayi musu sallama zata tafi, sai yaji sam baya son rabuwa da ita da da hali da ya bita sai dai yasan a yanzu zaman gidan baba yafi ƙarfinshi tunda dai shi da kanshi ya kore shi yace ya bar mishi gidanshi saboda ƙaddarar rayuwa ta afko mishi, abinda yafi yi mishi ciwo kenan a duk abinda ya sameshi yadda Baba ya juya mishi baya tamkar bai taɓa sanin shi ba kawai saboda ya gama yi mishi amfani, har da wannan yasa ya ƙuduri aniyar in har ya cigaba da rayuwa da izinin Allah sai Baba yaga yadda Allah zai yi dashi, akanshi zai san cewa nakasa ba kasawa bace, sai yayi alfahari da abinda zai zama don ba zai taɓa zama komai sai anyi mishi ba alhalin Allah ya barshi da ranshi da lafiyar da zai iya tashi ya nemi na kanshi.
Har bakin titi ya rakata sai da ya tare mata adaidata sahu ta shiga har ma ya biya kuɗin a cikin sauran kuɗaɗen zanen shi da suka yi ragowa sannan suka yi sallama, bai bar wurin ba sai da adaidaitan tayi mishi nisa ya daina ganinta sannan ya sauke ajiyar zuciya ya koma gida yana jin kewar Umman ta sake kamashi, fatanshi dai Allah yayi mishi arziƙin da zai ɗauke Umma ya mayar da ita kusa dashi don yana da burin rabata da zaman gidansu wanda bata tsintar komai a ciki sai kayan ɓacin rai.