← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 168

Sashe 65

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

******
Yau Maryam tun safe ta tashi ta fara shiri, babu shakka yau duk yadda zata yi sai ta lallaɓa Baban Areef ya barta taje duba Ya Baqeer, cike da salonta ta shirya tun yana kan gado ta kwanta ta shige jikinshi, a hankali ta gangara ta fara yi mishi wasu salon wasanni da suka janye hankalinshi gaba ɗaya, wani irin nishi kawai yake saukewa yana gurnani, wani irin salo ta shiga yi mishi daya rikitashi nan da nan ya fita daga hayyacinshi, nan suka shiga nunawa juna ƙauna. Tare suka yi wanka ya rungumeta yana sumbatarta.
Saman fuskarshi ta shafa tace “Bae please inje wurin Dada?”
Kai ya ɗaga mata yace “Kije zan sanar da Baffa kawai dai ki dawo daidai lokacin ɗauko Areef daga school.”
Sumbatarshi ta sake yi tace “Haka zan je bazan riƙe musu komai ba?”
“Fitowa yayi ya ɗauki wallet ɗin shi ya miƙa mata dubu biyar yace “Ki saya musu wani abu, nima zan samu lokaci naje na gaishe su.”
Murmushi tayi sannan suka shirya suka fito, breakfast ta haɗa suka zauna dukansu akan dining table, bayan sun gama ya shiga gaida Baffa nan yake ce mishi yana son kuɗi da zai riƙe a hannun shi, ganin babu kuɗi ya shigo gidan sai ya fito yazo wurin Maryam ya kalleta yace “Kuɗin da na baki ko zaki bani na bawa Baffa ke sai na tura miki ta account?”
Mamaki ne ya rufeta tace “Ko shi zaka turawa ta account ɗin ni kaga wurin masu fruit ba kowa ke amfani da POS ba.”
“Bani please ai dubu uku ma yake so Baffa yace kema dubu biyu ta isheki.”
Kamar zata yi magana ta fasa don tasan komai ta faɗa komawa zai yi ya sanarwa Baffan amma in banda haka dubu me zata yi mata, haka ta ciro ta  bada ita kuma ta riƙe dubu biyun, zuciyarta duk babu dadi haka ta ajiye Areef a makaranta sannan ta wuce gidan Dada bayan tasa yi kayan marmari ƴan kaɗan don ba zai yiwu taje musu gida hannu na dukan cinya babu wani ɗan alheri ba.

+*******
“Lale-lale maraba da Maryamu Daso, yau kece a gidanmu da safen nan?”
Maryam ta gaisheta tare da ajiye ledojin hannunta tace “Dada ni kam har yanzu ana yin tsame?”
“Ana yi mana a gidan Talatu ko dai Areef zai yi kanwa ne?”
Murmushin yaƙe tayi don ita kanta cikin take so ta samu amma har yanzu shiru, nan ta bawa wata yarinya data shigo wurin Dada 200 ta siyo mata, suka shiga ciki.
Ƙofar ɗakin Baqeer ta ƙwanƙwasa, ya buɗe yana kallonta, wani sanyi ne taji ya ratsata ganin nutsuwa a tattare da Baqeer tabbas bata taɓa zaton zata zo ta ganshi haka ba ta ɗauka in tazo zata ga ya rame sai gashi ta ganshi kamar da harma yafi da samun nutsuwa a fuskarshi.
Haka suka fito falo suna hira da Dada shi kuma yana daga gefe sai jefi-jefi yake saka musu baki, anan aka kawo tsamen suna ci ana cigaba da hira.
Shi dai duk hirarsu ba itace damuwarshi ba so yake ya tambayeta game da kawarta Zainab, wacece ita? A ina suka haɗu? To amma ta ya zai fara tambaya? Dada ce ya kamata tayi maganar amma yaga sam bata da alamar yin hakan sai wani zancen ma da suke yi wanda shi duk ba shine a gabanshi ba.
Ya tambayeta ne?
Ko kuwa dai yayi shiru?
To in zai tambaya yace me? Menene haɗinshi da ita da ya damu da sai yaji ita wacece?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
    *Da*
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
            *DA*
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN

{40}

Har Maryam ta mike zata tafi Baqeer bai iya tambayarta komai ba game da Zainab. Haka suka fito Dada ta rakota sai da zata shiga mota Dada tace "Maryam nikam ki mana godiya gun kawarki."
Da mamaki Maryam ta kalli Dada tana ƙoƙarin bata amsa waya ya shigo cikin wayarta hakan yasa ta ɗaga tare da ɗagawa Dada hannu. Nan ta shiga mota ta bar gun.
******
Ranar da Zainab taje ta karɓi ɗinkinta  ita da kanta tayi mamakin yadda style ɗin ya fita fiye ma da yadda tayi zato gashi kuma sosai ya dace da atampar da telan ya zaɓa mata, sai zuzuta haɗuwar kayan take yi tana jin daɗi. "Ai Hajiya idan kinga yawan mutanen da suka ce nayi musu irin ɗinkin nan wallahi zaki yi mamaki bare ma dana ɗora a shafin mu na IG da facebook baki ga yawan likes da comments ɗin da muka samu ba, sai dai haƙuri kawai nayi ta bawa mutane nace mai kayan tace bata son ganin irin style ɗinta a jikin kowa." Wata dariyar farin ciki ta saki tana jin daɗin yabon da kayan nata da ya samu, tana kuma daɗa jinjinawa Baqeer don shi ya fito da zanen style ɗin fiye ma da yadda ta kwatanta mishi, tana wannan tunanin ne taji telan ya ƙara cewa "Da zaki daure sai ki haɗani da wanda yayi miki wannan zanen Hajiya don naga ya iya tsara style ɗin ɗnkuna masu kyau dan kuwa nasan ba ƙaramin ciniki zamu samu ba." Kallonshi tayi tana jinjina abinda yace cikin ranta, tabbas idan Baqeer zai yarda yana daga zaune ya samu sana'ar yi tunda dama bai san wani abu ba bayan harkar zane watakila daga zanen kayan sai kaga ya koma wa harkar paintings ɗin shi cikin ƙanƙanin lokaci don haka ta cewa telan "Zan yi mishi maganar muji me zai ce amma fa kasan zaka yi mishi biya me kyau ne idan ya amince ko?"
Ai tuni ya fara washe haƙora yana murna yace "Haba Hajiya me zai hana kuwa na biyashi idan har irin waɗannan styles ɗin yake zanawa da ba ko ina za'a iya ganin su ba, ai ko ace wasu sun kwafemu sun yi irin su to a wurin mu dai za'a fara gani kinga kuwa ko wannan ai riba ce a karan kanta bare kuma nasan zasu ƙara janyo mana customers."
"Haka ne" tace tana mayar da kayan cikin ledar su. "To muyi maganar price tun yanzu yadda idan naje zan faɗa mishi, nawa zaka na biya akan kowane sketch?"

Tsayuwar shi ya gyara yace "Eh to ina ganin zan dinga biyanshi kaso ɗaya cikin huɗu na abinda na samu."Wani irin kallo tayi mishi "You're not serious at all, to zaka biya shi akan kowanne ɗinki ko kuwa a guda ɗaya? Kenan idan kayi ɗinki akan dubu ashirin dubu biyar ne nashi, bari kaga tafiyata don naga alamar ba da gaske kake yi ba, ka dai san ba kai kaɗai bane telana zan iya neman wani telan muyi ciniki ba sai na tsaya kana raina mini wayo ba,” ta suri ledarta ta nufi ƙofar fita daga shagon. Da sauri ya dakatar da ita yana cewa "Haba Hajiya kada muyi haka dake mana, duka abun ai bana zafi bane, kawai tsayawa zaki yi mu daddale akan nawa zan dinga biya kinga idan na biya shi shikenan ni style ɗin ya zama nawa."
Murmushi ta saki tace "To yanzu naji magana amma ina jin barin maganar price ɗinnan zamu yi har sai naje mun tattauna dashi don kasan fa harkar paintings yake yi zai fi kyau ma ya yanke kuɗin da kanshi don shi yasan a yadda yake sayar da kayanshi."
"Amma Hajjaju style ɗin ɗinki daban painting daban ba zai yiwu ayi musu kuɗi iri ɗaya ba,” yace mata don baya so aje a tsuga mishi kuɗi da yawa tunda yasan paintings suna da tsada sosai." Harararshi tayi tace "Duk ba zane bane kuma ƙwaƙwalwa ke ƙirƙirarsu to don me kuɗin su zai bambanta? Kai dai kada ka samu damuwa I assure you sketches ɗin da zai yi maka har matan gwamnoni sai sun nemeka don ka zama telansu, ai dai ka gani wannan kaɗai daka ɗinka mini yadda mutane suka yaba dashi."
"Haka ne kuma Hajjaju, to sai na jiki dai kenan ko?" Tace "In Sha Allahu, kada ka samu damuwa."
Chapter 65 · 0% Book details