← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 168

Sashe 161

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai yaji ranshi ya ɓaci sai dai yayi shiru bai katse shi ba har ya gama magana, cikin ɗaurewar fuska yace "Ni bazan iya cewa Baffa ya daina shigowa cikin gidan nan ba don dani da abinda na mallaka duka mallakin shi ne baya da wani iyaka da duk abinda na mallaka ba kuma zan iya canja mishi gida ba bayan nasan ba wani da zai kula dashi gareshi ba tunda mahaifiyarmu ta rasu ba kuma wata matar gareshi ba."
Rai a ɓace Baqeer ya mayar mishi da "Bashiv da iyaka da komai naka face Maryam don kuwa ba a garin gaɓa-gaɓa muke ba mu musulmai ne ba kara zube muke rayuwa ba, idan har ba zaka dakatar da mahaifinka daga shigo mata ɗaki ba to lallai kuwa zan tafi da ita gida don bazan barta ta cigaba da zama da kai bata da sakewa a cikin gidanta ba tana fargabar kowane hali take ciki za'a iya shigo mata. Ke Maryam ɗauko mayafinki mu tafi don ba zaki cigaba da zama a gidan nan ba."

Da sauri Auwal ya tare shi ganin har Maryam ta miƙe zata tafi ɗaukar mayafin kamar yadda Baqeer yayi mata umarni. "Kayi haƙuri Ya Baqeer don Allah kada ka tafi da ita yanzu dai me kake so ayi nayi alƙawarin yi maka in har zaka bar mini Maryam." Kallon kada ka raina mini hankali Baqeer yayi mishi yace "zaɓi ai yana wurinka tunda na faɗa maka su, inma dai ka canja mata muhalli ko ka hana mahaifinka shigo mata wuri dai kuma batun sana'a daka hana lallai idan har baza tayi aiki ba dole ka barta ta nemi na kanta saboda halin rayuwa ba'a san me gaba zata haifar ba bayan haka kuma ita ma tana da iyaye tana da ƴanuwan da zata so tayi musu hidima da guminta ba sai ta jira abinda ka bata ba."

Haka nan ya amince da duk abinda Baqeer yace ba don yana so ba sai don yasan ba kowacce mace bace zata ɗauki abinda Maryam ɗin ke ɗauka ba. Zama da Baffa ne bata so to zai gyara mishi tsohon gidansu ya koma idan yaso sai ya nemi wata matar yayi aure, su dama tun bayan rasuwar mahaifiyarsu ai auren suka so yayi shine yaƙi shine kuma dalilin da yasa ya dawo dashi nan saboda acan ɗin babu kowa ko wajen abinci babu mai bashi amma yanzu ya zama dole ya koma ko ba zai yarda yayi auren ba idan yaso sai su nemi wanda zai dinga zama dashi suna biyanshi abinci kuma ko daga nan ko gidajen ƴan uwanshi sai a dinga girkawa ana kai mishi.
Haka Baqeer yayi musu sallama ya tafi bayan ya cika Maryam da kyautar kuɗaɗe ya kuma ce tayi tunanin sana'ar da take son yi shi zai bata jari ba sai ta tambayi Baban Aareef ba.

*****
Bashir na fita daga gidan ya dannawa number Umma ƙira, abinda ba zai iya tuna ranar da yayi hakan ba don fa iyayen su sun koya musu rashin ganin girmanta tun suna yara shi yasa kusan dukkansu yaran gidan suka rainata don ma ba shiga shirginsu take yi ba shi yasa duk abinsu basa iya yi a gabanta. Bayan ta ɗauka ne ya gaisheta sai kuma yace "Umma dama gaininki nake son yi don Allah." Duk da tayi mamakin jin wai Bashir ke son ganinta hakan bai hanata cewa tana gidan Dada yaje can ya sameta ba, kwatancen gidan tayi mishi don ba taɓa zuwa yayi ba. A wurin ya tari adaidaita ya faɗa mishi inda zai kai shi cike da fatan dacewa da abinda zai je nema. A ƙofar gidan Dada mai adaidaitan ya ajiye shi kamar yadda Umma tayi mishi kwatance don dama gidan ba wani wahalar ganewa ne dashi ba. A ƙofar gidan ya tsaya ya kira Umma a waya yace mata gashi ya ƙaraso sai tace mishi ya shigo kawai. Suna zaune a tsakar gida ita da mai aikin Dada suna haɗa abincin rana don tunda Umma ta dawo gidan ta karɓi aikin girkin sai dai mai aikin ta tayata da ƴan wasu abubuwan. Zama yayi akan tabarmar da Umma ta shimfiɗa mishi ya shiga gaisheta cike da girmamawa abinda da sam basa yi mata. Da fara'arta ta amsa tana tambayarshi lafiyar mutanen gidan yace mata duk suna nan ƙalau Jamila ma tace a gaisheta. Murmushi tayi tace tana amsawa jin wai yau Jamila ce ke aiko mata da saƙon gaisuwa.

Ɗan shiru yayi yana juya ta yadda zai fara faɗa mata abinda ya kawo shi sai da taga baya da alamun zai ce wani abu sannan tace "Wacce magana ce kace zamu yi? Kada kaji komai ka buɗe bakinka ka faɗa mini ni uwa ce a wurinka."
Ɗan gyara zamanshi yayi yace"Dama Umma cewa yayi don Allah ko zaki yiwa Ya Baqeer magana ya bani aiki a shagon shi tunda na gama makaranta aiki ya gagara samu bare aiki a ƙasar nan da ya zama na masu hanya sai kuma mai tsananin rabo."
"Haka ne,"Umma tace. "Baqeer ɗin baya nan yana shago amma In Sha Allah idan ya dawo zan faɗa mishi nasan ba zai rasa wajen da zai ajiye ka ba." Godiya yayi ta yiwa Umma don yasan tabbas Baqeer zai bashi aikin don baya taɓa tsallake umarnin Umma.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
       *Da*
*Umm Asghar*

*BAQEER*
*NA*

*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA TARA*

{99}

Baqeer na komawa gida wanka kawai yayi ya shirya cikin wani tsadadden men lace kalar sky blue da ya yiwa special ɗinkin shi da wa kanshi kaɗai yake yin designs ɗin. Dark blue ɗin hula ya saka sai baƙaƙen takalma ƙirar kamfanin baertozzi da ya saka. Turarukanshi ya fesa da ba'a iya tantance sunayensu saboda ba guda ɗaya yake amfani dashi ba a lokaci guda, ya kan fesa a ƙalla turare uku zuwa biyar don haka ba'a taɓa iya tantance wane kalar turare yake amfani dashi. Yana fitowa Dada ta sa ka guɗa tana tsokanarshi tace "Iye wannan wankan dai daga gani zance zaka," shi dai murmushi kawai yayi. Ta cigaba da cewa "to idan kaje kace ina gaisheta da kyau da kyau, na kuma gode da kayan marmari." Bai iya amsawa Dada ba ganin Umma zaune a wurin, ita kuwa Umma sai daɗi take ji don tasan macen ƙwarai ce kawai abinda Baqeer ɗin ya rasa a yanzu, fatanta da burinta bai wuce na ganin aurenshi da zuri'arshi ba sannan tunda taga sun koma tare alama ce ta Dady ya sauko kenan. Sallama yayi musu ya fita inda Tanimu yake jiranshi don ya faɗa mishi dama kada yayi nisa zasu sake fita bayan magriba. Buɗe mishi motar yayi ya shiga ya zauna sannan ya zagaya ya shiga mazaunin direba yaja su suka bar wurin. Sai da suka hau titi sannan yake tambayar inda suka nufa, "Unguwarsu Salim zamu je don nasan yanzu yana can yana jiranmu, ban ɗauka zamu daɗe sosai a gidan Maryam ba sai gashi mun kai kusan magriba acan."
Suna shiga unguwar ƙiran Salim na shigowa wayarshi, yana ɗauka Salim ɗin yace "haba Baqeer taya zaka sani na zauna ina faman jiranka amma har yanzu baka ƙaraso ba." Ɗan tsaki Baqeer ɗin yayi yace "To Malan gamu nan mun shigo cikin unguwar, a ina zamu sameka?"
"Ina majalisar su Audu, please kuyi sauri don ina da wurin zuwa nima tun kafin kuma kace wani abu ba zance zani ba."
"Kaji da gulmarka,da ɗin ta dai unguwarsu ɗaya." Baqeer yace ya kashe wayar bai jira jin me Salim ɗin zai sake faɗa ba. A majalisar su Audu suka tsaya, sai da Baqeer ya gaisa da ƴan zaman majalisar da suka kasnace tsofffin abokanshi sannan Salim ya buɗe gaban motar ya shiga Tanimu yaja motar suka bar wurin. Basu tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan su Zeey, horn ya danna maigadi ya taso ya buɗe gate don dama Zeey ta sanar dashi zuwansu tace kada yayi nisa su zo suna ta yin horn babu mai buɗe musu ƙofa don shima akwai ɗan banzan yawo idan yaso tun ma ba yanzu da Daddy yake kwance baya da lafiya ba.
A harabar gidan Tanimu yayi parking motar, basu fito ba sai da Baqeer ya ƙira Zeey a waya ya sanar mata da isowarsu. Ƙara gyara fuskarta tayi sannan ta fita wajen Daddy da yake zaune a parlourn shi da Kabir, a shirye yake tsaf zuwan su Baqeer kawai yake jira don tun bayan da suka rabu ɗazu tana dawowa gida ta sanarwa Daddyn cewa zai zo ya gaishe shi shi yasa ana yin sllar magriba ya shirya ya fito parlourn ya zauna yana jiran zuwan nasu. Faɗa mishi tayi su Baqeer ɗin sun iso, Kabir ne ya tashi ya fita don ya shigo dasu ita kuma ta tura Daddyn zuwa sitting room ɗin shi inda yake amsar baƙin shi. Bata jira shigowarsu ba ta koma ciki don ta haɗo musu kayan motsa bakin data tanadar musu.
Chapter 161 · 0% Book details