← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 168

Sashe 50

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Anan Alhaji Suleiman Ƙaraye ke jin abinda ya faru da Baqeer ɗin, sai yayi ta mamaki yana jinjina lallai kam dole  Badaru ya ƙara gigicewa tunda ɗan da yake ji dashi ya zama nakasashe. Haka dai taro ya tashi kowa ya tafi da abinda Mallam Badaru yayi a bakin shi sun kuma tabbatarwa da Alhaji Suleiman Ƙaraye da zasu taimaka mishi wajen yaɗa kyakkyawar manufarshi a wajen sauran mutanen unguwa don irin shi dama suke buƙata da tsayawa takarar siyasa waɗanda suka san su suka san buƙatunsu da zasu yi musu aiki tuƙuru wajen magance musu matsalolin su ba waɗanda ba'a ganinsu ba sai lokacin campaign yayi. Haka suka yi sallama yana jin daɗin yadda taron ya kasance don yana hangowa kanshi nasara a zaɓen da za'a gabatar duk da ma Badaru yaso ya watsa mishi taro amma da yake kowa yasan halin shi sai abun bai zama wata babbar matsala ba. Yana shiga gida yake faɗawa Mummy yadda taron ya kasance har ma da ƴar hatsaniyar da Mallam Badaru yaso tayarwa anan nema yake faɗa mata abinda ya samu Baqeer. A take ta nuna bata san zancen ba duk kuwa da ita ta taimakawa Kabir wajen ɓoye laifin shi a wajen mahaifin nashi, tasan tabbas in har ya sani tofa akwai matsala sai cewa tayi "Garin yaya kuwa?" Yace "Wallahi ban sani ba sai dai ban sani ba ko hatsarin da yazo yace yaron yayi kwanaki ne sanadi wanda har yace Kabir ne ya buge ɗan nashi."

Sai ta taɓe baki tace "To waya sani ne kam, shi da ba'a rabashi da neman rigima, ai tun lokacin na faɗa maka sharri ne kawai yake so ya ƙullawa Kabir don ya samu abinda zai riƙe yace kayi mishi kaga in yayi haka ai ya zubar maka da mutuncin da yasan mutane na ganinka dashi."

"Haka ne kuma fa, to Allah ya kyauta mishi ya ganar dashi hassada dai ba abu bace me kyau."

"Ameen dai distinguished, In Sha Allah kujerar nan tamu ce tunda muka samu manyan unguwa a hannun mu." Wani murmushin jin daɗi ya saki yana hango kanshi akan kurerar senator don ji yake yi kamar ma har yaci ya gama sai dai a jira lokacin zaɓe kawai.

*****

Tunda aka fitar dashi daga gidan maigadi ya mayar da gate ya rufe yake faman zazzaga masifa har mutane na tsayawa suna kallonshi sai dai babu wanda y tambayeshi dalilin faɗan shi domin kuwa kowa yasan hali Mallam Badaru mafaɗacin mutum ne, ba'a taɓo shi ba ma ya aka ƙare dashi bare an takaleshi. Sai da yaga dai an mayar dashi kamar mahaukacin shi kaɗai yake faɗan shi babu abokin tayi sannan fa ya kama hanyar gidan shi yana cigaba da zazzaga masifa, har ya isa gidanshi bai yi shiru ba sai da ya ganshi a tsakar gidanshi ko sallama bai yi ba tsabar bala'in dake cin zuciyarshi. Da yake Jamila tasan tsiyar data shuka mishi ko leƙowa tsakar gidan bata yi ba bare kuma Fatima da dama yanzu ba wani shiga sabgar shi take yi ba ganin shima ya tattara al'amarinta ya watsar don ko ranar girkinta idan bai ga dama ba ɗakin Abu yake shigewa ko kuma ya gaiyaceta nashi ɗakin, Jamila ce dai da aka san ba zata yarda a danne mata hakki ba basa yi mata wannan kama karyar amma yadda Abu ta sameshi a hannu sai abinda tace yanzu ake yi a gidan.

Abu na fitowa yace mata "Ina biredi na dana bayar aka shigo mini dashi ɗazu?"

"Biredi kuma? Gaskiya ba'a bani ba sai dai ko idan Jamila aka bawa. Amma waye ka bawa ya shigo dashi don ni dai ina ɗaki ban ji shigowar kowa ba".

Ai tuni ya ƙara harzuƙa jin wai Abu bata san an shigo da biredi ba. "To wa aka bawa biredin nawa bayan ke nace a kawowa?"

"Gaskiya Mallam ban sani ba don ni dai babu wanda ya kawo mini biredi".
"Jamila. Jamila!" Ya hau ƙwala mata kira ita kuwa tana jin shi tayi luf kamar ba ita yake yiwa wannan kiran mafarautan ba, sai da taji ya nufo ɗakinta yana cigaba da ƙwala mata kira sannan ta fito tana cewa "Mallam lafiya, irin wannan kira haka kamar naci bashi ban biya ba". Hannu ya miƙa mata yace "bani nan". Yi tayi kamar bata san akan me yake magana ba tace "me zan baka?" Cikin tsawa yace "Kinga Jamila kada ki kawo mini rainin hankalin da kika saba, shiga ki ɗauko mini biredi na dana bayar a shigo mini dashi."

Tsuke fuska tayi itama tace "Kuma ɗan aiken ni yace maka ya kawowa biredin naka? Ko kuwa dai tijarar taka ta fama zaka sauke a kaina, to wallahi sam ba zata saɓuba tun wuri gara ka nemi inda aka kai maka biredinka amma ba wajena ba, yo in banda neman fitina ma irin taka da kayanka kake bani da zaka zo wurina neman abunka ko kuwa ni kaɗai ce a gidan da don ka rasa abunka zaka tsallake kowa ka taho wajena nema? Me yasa baka tambayi Fatima ba yanzu haka ma ita aka bawa tana ji kana tuhumar mu tayi shiru a ɗaki." Ai kamar kada ta ambaci sunan Umma sai ya mayar da akalar kiran nashi a kanta, ita kuwa baiwar Allah tana zaune akan sallaya tana lazumi tunda ta idar da sallar isha'i bata tashi ba, duk hayaniyar da suke yi tana jiyo su sai dai ko kaɗan bata ji zata saka musu baki ba shi yasa har sai da ya dangana da ɗakinta sannan ta ɗaga kai tana kallonshi. "A ina kika ajiye mini biredin don wulaƙanci kina ji ina nema ba zaki fito ki bani ba?" Yana yi yana bincike ɗakin yana neman inda ta ajiye mishi biredin. Bata tanka mishi ba har ya gama bincike ɗakin tsaf bai ga inda ta ajiye biredin ba don haka ya zuba mata ido yana jin wani sabon ɓacin rai na taso mishi yace "ba dai har kin cinye biredin ba?"

Sai sannan ta amsa mishi cikin tausasawa da "Wai wane biredi ne kake nema haka? Ni babu wanda ya bani biredin ka hasali ma tunda nayi alwalar sallar magriba ban ƙara fita tsakar gidan ba har yanzu sai dai ka tambayi su Abu ko Jamila." A harzuƙe yace "Basu na fara tambaya ba suka ce ba'a basu ba idan ba ke aka bawa ba to ina biredin yayi?" Ƙara tausasa muryarta tayi tace "Wallahi Mallam ba'a bani biredin ka ba, ni yaushe  rabon da wani abu naka ma ya shigo hannuna" ta ƙare maganar idanunta na ciccikowa da ƙwalla. Fita yayi yana bala'i wallahi duk inda biredin shi yake sai an fito mishi dashi, ita dai Abu sai rantsuwa take yi akan ita ba'a bata wani biredi ba shi kuma yace ai ita yace almajirin ya kawowa to don me yanzu zata ce bata san maganar ba. Jamila dai na daga gefe tana dariya a zuciyarta tana cewa "Ai yau ko kafi ƙuda naci sai dai ka haƙura da biredin nan don bazan bayar ba, Allah ne ya ƙwato mana haƙƙinmu da kake dannewa, ke kuma makira algunguma ko banza dai nayi miki sanadin ɓacin rai fiye ma da yadda kika yi ta sakani a kwanakin nan" daga baya ma sai tayi shigewarta ɗaki tana rausaya jikinta irin na duniya tayi mata daɗi ɗinnan.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
        *Da*
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*🦼
     *NA*
*UMM ASGHAR*
Da
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ƊAYA*

{31}

Badaru haka ya kwanta ranshi duk a jagule ji yake yi zuciyarshi nayi mishi zafi kwanan nan, har rasa irin masifar shi yake yi, to shi yanzu ba mutuncin kowa yake gani ba tunda burinshi ya lalace jin zafin kowa da haushin kowa yake, duk yanda Abu taso taja ra'ayinshi bata samu fuska ba, da yake sun san kwanan nan bala'i yake ji tun bayan abinda ya samu Baqeer yasa itama bata nace ba ta kwanta tana ƴan mitocinta wanda suka tsaya iya zuciyarta. Dole gobe a cikin jarinta ta bada a siyo mishi kwai da bread yanda zata ƙara kamashi kafin ya canza mata ita ma.
Chapter 50 · 0% Book details