Sashe 132
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Da sauri Salim ya taho ya riƙe keken Baqeer da yake ta saurin turawa saboda yana son barin unguwar, kallon Salim yayi wanda shi kanshi kallon shi yake cike da dauriya yace “Baqeer ina zaka kake wannan saurin?” Kallonshi yayi cike da mamaki da takaici, sai a lokacin ya kalli Zainab dake tsaye a inda ya barta, kanshi ya kauda da sauri sannan ya cigaba da tura keken, Salim ne ya kalli ledar dake hannunshi wanda ake ta murna za’a bawa Zainab, shafa bayan kanshi yayi yana tunanin abun yi. Wurin Zainab ya koma dake tsaye kawai tana share ƙwalla, ledar ya miƙa mata, amsa tayi tana kallonshi, muryarta na rawa tace “Salim please ka kula dashi.” Kai ya ɗaga sannan yace “Ki koma ciki In Sha Allahu babu abinda zai faru.” Ta ɗaga kai alamar to sannan tace “Nagode,” tayi maganar tana juyawa, sai daya ga ta shige gida sannan yabi bayan Baqeer lokacin har ya kai ƙarshen layin, adaidaita ya tarar musu suka bar layin suna fatan babu wanda ya ganshi. Shi dai Baqeer tunda ya zauna bai ce komai ba, zuciyarshi ce kawai take tafasa, shi yasa ashe ko da wasa bata so tayi maganar data shafeta, hannayenshi ya dunƙule zuciyarshi na wani irin zafi, how? Taya zata mishi haka? Sai data bari ya gama mutuwa akan sonta? Shi a kanta zai iya rufe ido yace sai ita to amma me? Mahaifinta ya sani ko duniya za’a haɗu a bashi baki ba zai bashi aurenta ba, shi bai damu da yardar Badaru ba sai dai shi yasan da ƙafarshi ma mahaifinta ba yarda zai yi ba bare babu, kanshi kawai ya kawar yana kallon titi shi kuma haka ƙaddararshi take? Daga wannan sai wannan? Yanzu da yake sa ran komai yana tafiya daidai ashe yanzun ma wani abun zai ƙara ɓullo wa? Har suka isa gida babu wanda yayi magana, shi dai Baqeer kawai ya wuce ɗaki Dada tana jiyosu ta fito tana tambayar jikin Zainab, sai Salim ne ya tsaya ya bata amsa don Baqeer ɗakin shi kawai ya shiga ya kulle, jikin ƙofar kawai ya jinginar da kujerar shi ta wheelchair yana maida numfashi, komai ne yake sake dawo mishi kamar a yanzu ake yinsu, tashin hankalin da aka sakasu shida iyayenshi a dalilin ta ne yake sake dawo mishi, amma ya aka yii bai ganeta ba? A iya saninshi tana da ƙiba to yanzu ta zama siririya duk sai kamanninta suka canza, idanunshi ya runtse sai dai fuskarta ce tana mishi magana ɗazu kawai ke dawo mai. Wayarshi ce ta fara ƙara ɗagota yayi ya zubawa wayar ido wanda sunanta ne ke jikin allon wayar, ido ya rufe ya sake buɗewa yana kallo har ta katse, bata sake jira ba ta ƙara kira ji yayi zuciyarshi ta kasa jurewa, duk da yasan ba abu ne mai yiwuwa ba amma a ƙalla ya sanar da ita abinda ke ranshi, wayar ya ɗaga ya karata a kunnenshi sai dai ya kasa magana, ita ma a bangarenta da alama ta kasa magana don ajiyar zuciya kawai suka sauke a tare, ƙasan lebenta ta ciza da har yanzu bata jin daɗi tace “Ya Baqeer!” Ido ya runtse gam don kiran data yi mishi har tsikar jikinshi sai da yaji ta tashi, yawun bakinshi ya haɗiya yace “Why?” Wasu hawaye ne suka gangaro saman kuncinta tace “I’m really sorry wallahi da farko ba wai ɓoye maka nayi a sanina ba, lokacin da muka yi ta haɗuwa da farko coincidence ne don ban ganeka ba sai sanda naje wurin Umma naga ashe kaine, at that time I feel so bad na ganin abinda ya sameka.”
Wani murmushin takaici yayi yace “Kenan duk abinda ke faruwa ƙarya ne? Taya zaki bari sai da na gama kamuwa da sonki nake ji bazan iya rayuwa babu ke ba sai naji kece wacce ni nasan ko za ayi me mahaifinki ba zai taɓa amince wa ba.”
Ji tayi komai na jikinta ya tsaya ta sauke wata ajiyar zuciya tace “Ya Baqeer me kace?”
Sam abinda ke ranshi ya faɗa wanda hakan yasa bai gane me take son ya maimaita ba, Zee ta daure tace “Ya Baqeer please me kace? I’m sure kunnena jiyo mini yayi zancen soyayya.”
Cike da takaici yace “Who cares Zainab? Ko kin manta ƙatuwar katangar dake tsakaninmu? Da so da rashinsa yanzu…..”
Katseshi tayi da sauri da cewa “I care, sannan for me that’s all that matters, duk duniya babu wanda ya isa ya rabani da kai, kalmar so kawai nake jira naji daga bakinka kuma naji ba damuwa ta bane ko ma me zai faru.” Yasan halinta ba abinda baza ta iya aiwatarwa ba sai dai shi a dalilin so ba zai taɓa saka yan uwanshi cikin matsala ba, especially Umma hakan yasa yace “Mun gama magana, bye.” Ba tare da ya bari ta ƙara magana ba ya kashe wayar ma gaba ɗaya, yasan waye Alhaji Sulaiman ya kuma san akan ƴar lelen ƴar shi babu abinda ba zai aikata ba, shi kuma duk da yasan yana mugun sonta yana ji in har bai aureta ba ya haƙura da aure kenan, amma fa ba zai salwantar da rayuwar ƴan uwanshi saboda ita ba. Takaici ne ya kamashi kawai ya cillar da wayar kan gado yasa hannu biyu yana dafa kanshi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi.
Zee kuwa hawayenta ta share don tabbas babu mai rabata da Baqeer, ɗakin Mummy ta nufa lokacin tana zaune tana duba wasu takardu wanda da alama masu amfani ne, Zee na shigowa ta ɗan maidasu gefe kallo ɗaya tayi mata tasan akwai matsala, hakan yasa ta ware mata hannu ita kuma ta ƙara so ta shiga jikinta, duk kuwa da haushin Mummyn da take ji a yanzu neman me lallashinta take yi, kuka kawai ta saka tace “Mummy ki yiwa Daddy magana ni wallahi da wanda nake so sannan aurenshi nake son yi yanzu.”
Mummy cike da mamaki ta ɗagota tace “Shine wanda kike bani labari?” Kai ta ɗaga tana sake goge ƙwalla tana cewa “Shi Mummy bana ji zan iya rayuwa babu shi, don Allah ku barni na aureshi ni a yanzu ma a shirye nake.”
Dafata Mummy tayi tace “Shifa? Yace yana sonki?” Kai ta ɗaga cike da alfahari da hakan tace “Eh Mummy don haka ki sanar da Daddy.” Kai ta ɗaga sannan ta shafi fuskarta tana goge mata hawaye tace “Zazzabi kike yi ne? Naji jikinki da zafi.” Hannu tasa ta riƙe hannun Mummy tace “Ba shine a gabana ba Mummy ni dai ki mishi magana.”
Shiru Mummy tayi kafin tace “Ko ma menene kiyi ina bayanki, abinda kike so as always nima shi nake so, sannan ko ya yake ina bayanki, kawai dai ina tsoron magana ne kin san har yanzu bai sauko da abinda ke faruwa ba.” Kallonta Zee tayi sai yanzu ma ta tuno da ashe itama fushi take yi da Mummyn tsabar ta matsu yasa tama manta. Neman miƙewa tayi da sauri Mummy ta riƙota tace “Zainab please ban da ke, ki tuna shaƙuwar dake tsakanin mu, nasan nayi muku laifi akan Nabila amma a matsayinki na mace ya kamata ki tausaya mini ki fahimceni.” Kallonta Zee tayi tace “Zamu yi magana daga baya, don maganata akan su Ummi ne,” tana kaiwa nan ta fito, ɗaki ta wuce tayi sallar la’asar sannan ta kwanta, tun ruwan tea babu abinda ta sha don bama ta jin shan komai balle taci wani abun, ledar da Salim ya kawo mata kaya ta bude tana kallon kayan da Baqeer ya ɗinka mata ta tabbatar yasha wuya kafin ya haɗa ɗinkin. Kuka ne kawai taji ya ƙwace mata don da alama abinda zuciyarta ke son yi kenan, ta zubar da ƙwallar har ta gaji, kuka take yi sosai tana rungume da material ɗin.