← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 168

Sashe 157

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
[2/6, 08:44] Ayusher: *BAQEER*
*NA*

*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA SHIDA*

{96}
A jikin motarta suka tsaya Baqeer nata kallonta, gaba ɗaya sai yaga ta canja mishi, ga wata irin nutsuwa da take da ita yanzun. Wani irin farin ciki ne yake ratsa zuciyarshi, yau dai gashi ga abar son shi a zahiri ba'a irin mafarkan da yake yawan yi ba sai idan ya farka yaga ashe mafarki yake yi. Ƙasaitaccen murmushi ya sakar mata yace "Kin dawo daga tafiyar kenan?" Itama murmushin ta sakar mishi kwatankwacin wanda yayi mata, haka nan take jin kunyar shi yau. Cikin wata irin murya tace "Umm na dawo, ya aka yi kasan bana nan?" Tace tana kallon fuskarshi sai dai ta kasa haɗa idanunta da nashi.
"Matsoraciya ce ke ai ban sani ba." Yar hararar tsokana tamai tace "Allah a'a, sannan indai ansan bana nan kenan nemana akaje ba'a sameni ba?"
Kai ya ɗan kauda yana murmushi mai sanyi yana cewa "Hmm maybe, kila naje bakya nan ance kinyi tafiya, maybe kila na ƙira wayar bata shiga ba."
Da mamaki ta juyo tana kallon shi jin wai yayi ta zuwa yana nemanta, ita ai ta ɗauka ya rabu da ita kenan tun daga abinda Daddy yayi mishi ashe dai bai manta da ita Aaaba, sai taji wasu hawaye na neman cika idonta, ɗaga idonta sama tayi tana ƙoƙarin mayar dasu ciki don bata son tayi kuka a gabanshi. Sai da ta samu hawayen suka koma sannan tace "Ɗambatta na tafi wurin Ummi, wayata kuma na canja number ne."
"Saboda ni kika canja number?" Yayi mata tambayar muryarshi tana ɗan rawa don yaji babu daɗi da yaji wai ta canja number ne, kenan don kada ya kira ya sameta a waya shi yasa ta canja layi. Da sauri tace "No ba haka bane Ya Baqeer nayi ne saboda hakan zai fi mana sauƙi wajen mantawa da juna don nasan mawuyacin abu ne iyayen mu su bari muyi aure a wancan lokacin sai dai hakan da nayi bai rage komai na daga yadda nake jinka a cikin zuciyata ba sai ma kewa da tunaninka da basu taɓa barina na huta ba."
Wani daɗi yaji da jin yadda take jaddada soyayyarta a gareshi, kallonta yayi sai yaga kamar ta gaji da tsayuwar don haka yace ko zaki shiga daga cikin motar ki zauna naga kamar kin gaji," kallonshi tayi sai ta girgiza kai alamun a'a don bata son abinda zai shiga tsakaninsu a yau ɗinnan. Shiru suka yi kamar ba zasu sake magana ba sai kuma yace "Da kikaje can kin manta dani?" Waigowa tai ta kalleshi, idanuwansu suka haɗu da juna, idanunta na kanshi yace "Ba haka bane?" Kai ta girgiza haryanzu idanunsa na kanta, ya dan waiga kaɗan gefe yace "In nace ban taɓa son wata mace kamar yadda nake jin son ki a raina ba zaki yadda?" Wani abu ne taji ya sauka daga saman kanta har kafafunta, idanuwanta ta zuba mai wanda suke tara kwalla, hannunsa yasa cikin aljihu yana cewa "Maganganun Daddy basu ban tsoro ba sai ma ƙara min ƙarfin gwiwa da suka yi wajen son ganin na mallake ki, tafiyar da kika yi ce abinda yayi min cikas don ni ban ɗauki rashin jituwarsu da Baba abinda zai hanani aurenki ba zan aureki with or without his consent, bana jiran ya bani izinin aurenki don bashi zai zauna min dake ba, Daddy ne dama matsalar shima kuma na shirya ɗaukar duk wani ɓatanci da zai fito daga wurinshi idan har zai haƙura ya bani aurenki."

Wani murmushin farin ciki ne ya suɓuce daga bakinta, cikin yanayi na jin kunya ta goge kwallarta tace "Shima Daddy ba matsala bane don a yanzu ya amince na kawo wanda nake so zai aura min ni kuma kasan kai ne..." sai tai shiru tana ta rufe fuskarta saboda kunyar yadda ta iya tsayawa a gabanshi tana fallasa mishi asirin zuciyarta.
Ya kalleta yace "Faɗa min nine me?"
Kai ta girgiza tace "Kaima kansani."
Shima kai ya girgiza yace "Bansan komai ba, a faɗa min ko daga haɗuwa na fara rubuta bashin da aka fara bina."
Kallanshi tai tace "Zaɓina, kai nake so da kai nake da burin kasancewa har ƙarshen rayuwata." Dariya yayi kunyarta na ɗaya daga cikin abubuwan dake burgeshi da ita, duk da Zainab take sakaltacciya tana da kunya sosai abinda yake ƙara mishi jin sonta don ya kasance yana son mace mai kunya, kuma yanasan mace wacce zata faɗi abinda ke ranta shiyasa santa yai kane-kane a ranshi.

"Yanzu dai an bani go ahead naje naga Daddy kenan?" A kunyace ta ɗaga mishi kai alamar amsawa, "In Sha Allah zamu je, sai kuma a bani number da aka canja saboda ni," ya ƙarashe maganar da tsokana. Dariya tayi ta miƙa hqnnu ta karɓi wayar da yake miƙo mata, number ta daddana ta miƙa mishi yayi saving, sai da ya fara kiranta don taga tashi number sannan yayi saving number da *Sweetums*.
Kallanshi tai tace "Allah ka canza," tai maganar cike da shagwaba, kallan daya mata ne yasa tai saurin cewa
"Ya Baqeer ina Dada?" kewar Dada na daga abun da yafi damunta a zamanta a Ɗambatta, sai sannan tasan ashe ba ƙaramin sabo tayi da Dada ba.
"Tana nan lafiya ƙalau, kullum sai tayi maganarki."
"Allah sarki Dada sosai nayi kewarta wallahi, don Allah kace ina gaisheta." Ɗaga mata kai yayi alamun amsawa.
Kamar kada su rabu haka suke ji sai dai kuwa hakan ya zame musu dole don magriba ta kawo kai, kallon agogon hannunshi yayi sai sabbab ya tuna ashe fa fitowa yayi da niyyar zuwa gidan Maryam suyi magana da mijinta sai dai yanzu lokaci ya ƙure ba zai yiwu yaje musu gida da fare ba sai dai kuma gobe. Haka suka yi dallama da Zeey ta shiga motarta yana kallonta har sai data bar wurin sannan shima ya shiga tashi motar Tanimu yaja shi suka koma gida, daga shi har ita sun manta da wasu mutane da suka zo gani tunda suka haɗu da junansu shikenan suka manta da komai.

*****
Da farin ciki Zeey ta koma gida, tana yin parking lot Kabir ya fito daga cikin gidan zai tafi masallaci sallar magriba, sai sannan ta tuna ashe fa shi ya tura ta taje ta karɓo mishi saƙo ita shaf ta ma manta da abinda ya fitar da ita ganin Baqeer da tayi yasa ta mance da komai. Fitowa tayi daga motar shima yana ganinta ya nufo wurinta da sauri yace "To ya?" Harararshi tayi tace"Ka duba wayarka ka gani sau nawa na ƙira ka, kawai ka tura ni wuri baka bani number ba don haka kada kaga laifina da ban karɓo maka saƙon ka ba." Ɗan sosa kanshi yayi yace "Share wannan batun don Allah, kun dai haɗu ai ko?"
Chapter 157 · 0% Book details