Sashe 118
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Nabila kam ta dinga buɗe makogaro tana kuka saboda Zeey taji sai dai ganin tayi kusan awa biyu tana kukan ba tare da tazo ba yasa ta daina don ji tayi har muryarta na neman dusashewa, haka ta kwashe kayanta ta dinga leƙawa sai dai gidan babu kowa kamar anyi mutuwa, su kansu masu aiki da alama sun fahimci akwai abinda ke faruwa a gidan don suma aikin gidan a hankali suke yi, ɗakin Kabir taje sai dai ta jishi a kulle haka taja akwatin ta fita idanuwanta duk sun yi ƙanƙanta. Motarta ta shiga ta bar gidan tana jin komai yayi mata zafi, takaicin abinda ta aikata ya isheta. Gida ta wuce kai tsaye, tayi parking sannan ta janyo manyan akwatinanta guda biyu tayi ciki, tana tafe kamar zata faɗi saboda wata irin yunwa da take ji, don kaf ɗin su tun breakfast babu wanda ya ƙara cin abinci.
A zaune taga Inna tayi shiru da alama tunani take yi, har ta shiga da akwatinan bata tanka mata ba, ganin haka yasa ta dawo tace “Inna.” Kallonta tayi cike da ɓacin rai kafin tace “Yanzu hankalinki ya kwanta? Kin ruguza farin cikin mahaifiyarki?”
Zama tayi a ƙasa kusa da Inna tana maida ƙwallarta tace “To ni menene nawa Inna? Ta tsaneni ba tare da nayi mata laifin komai ba, ko abinci take ci idan nazo wuri haƙura take yi sannan daga baya naji wai bama Yayata bace mahaifiyata ce? Sannan ni da nake ƴarta bata damu dani ba sai su Zainab? Kina ganin yadda take yi musu bata iya ɓoye son da take yi musu.”
Cikin faɗa Inna tace “Wannan dalilin bai kai kiyi abinda kika aikata ba, tunda Halima ta kira ni a kan cikin ƙaryane, ke kin san rayuwar data shiga a baya saboda cikin ki? Kin san yadda tasha wahala? Ko kuwa kin san abubuwan da tayi saboda ta canza tabon dake jikinta saboda nan gaba ke kar kisha irin wahalar data sha?” Nabila ɗagowa tayi sai taji kuka ya ƙwace mata tace “Inna na tuba, don Allah ku yafe min, kishin su Zainab ne da son Kabir ya sani aikata hakan.” Inna ba tace mata komai ba ta miƙe tayi ɗaki, nan ta ƙara durƙushewa tana rera wani kukan na tsananin dana sani.
****
Zeey kam bayan sallar Isha’i tana kwance kan sallaya bacci yayi gaba da ita, bata farka ba sai asuba, haka ta tashi tayi sallah sannan ta zauna akan gado tana tunani, fitowa tayi ganin gari ya fara ɗan haske ta nufi ɗakin Daddy, sai dai da alama ma baya gidan, jikinta ne yayi sanyi hakan yasa ta juya, muryar Mummy taji tace “Auta bai dawo ba, da alama a guest house ɗinshi ya kwana.” Bata tanka wa Mummy ba kawai ta koma ɗaki har ta zauna ta tuna gift ɗin da Baqeer ya bata hakan yasa ta fito taje motarta ta ɗauko ta koma ɗaki, anan kan sofa ta zauna ta buɗe jakar, idanuwanta ne suka sauka kan fabric ɗin nan, ta fara janyoshi ta wareshi, nan da nan tayi wani murmushin jin daɗi, abayar tayi mata kyau har bata san yadda zata kwatanta ba, a fili ta furta “My Baqeer.” Ta ɗan rungume abayar, turaren ta ciro ta ajiye shi akan dressing mirror sannan ta ajiye abayar a bakin gado, agoggo ta kalla karfe takwas na safe gani take lokacin ma kamar baya sauri sam, saƙo ne ya shigo wayarta hakan yasa ta janyo wayar sai taga daga Baqeer ne, wani murmushi ta saki a fili tace “ɗan halak!”
_Sending you good thoughts and hoping you believe in yourself just as much as I believe in you. Morning_
Sakon ta ƙurawa ido tana jin wani irin kewar Baqeer na shigar ta, dole zata bayyana mishi ƙaunar da take yi mishi don a wannan lokacin tana ji gwara tayi aure ta bar gidan don ganin Mummy ya fara mata wahala. Maimakon tayi mishi reply sai ta kwanta ta ɗaura wayar a saitin ƙirjinta ta rungume tana tunanin Baqeer a haka wani ɗan karamin bacci yayi awon gaba da ita.
****
Baqeer kuwa bayan ya tura mata ne ya sake karantawa, goshinshi ya ɗan riƙe yace “Ko dai saƙon bai kamata bane?” Sai kuma ya girgiza kai yace “Abinda ke raina ne sannan I think it’s time to let her know abinda nake ji a kanta, in har bata yi gwara na haƙura kafin na ruguza abinda ke tsakaninta dasu Dada.” Da wannan shawarar ya cigaba da exercise dinshi, gwada sauke ƙafar yayi yana ɗan neman yin amfani da ita ya tsaya tsaye, sai dai yaji ya kasa, ya sake nan ma ya kasa, dabara ce tazo mishi ya saukesu sannan ya riƙe head board na gadon ya ɗan sa ƙarfi gadon ya zame mishi kariya ya riƙe, yana tsayuwa ko second biyar bai yi ba ya faɗa kan gadon, samun kanshi yayi da dariya yace “Baqeeru da sauranka.” Wayarshi ya sake janyowa Zee har yanzu bata yi reply ba, IG ya shiga ya sake posting na wasu flyers da yasa aka musu na adverts sannan yai shiru yana tunanin wani yankan ɗinkin maza daya fara, wani unique designs ne wanda bai taɓa ganin anyi ba, ya tabbatar in aka gama ɗinkin nan zasu samu mutane In Sha Allahu. Sai wajen goma Tanimu yazo suka je makaranta suna dawowa ya leƙa shagonsu suka sake gyarawa su biyu sannan ya ƙarasa yankan da yake yi, yanayi yana nunawa Tanimu yadda zai yi ɗinkin, basu gama ba sai karfe sha biyu, wani murmushi ya saki ganin ɗinkin ya fita sosai yadda ya tsarashi, Tanimu kam sai dariya yake yi bakinshi yaƙi rufuwa.
Baqeer yayi murmushi yace “Muna needing styles kamar biyar kafin mu buɗe shago, na mata muna da su kawai ɗinkawa zamu yi sannan ina so na sayi wasu manyan electric sewing machine idan aka samu kuɗi, ina ganin daga nan zamu iya buɗe shagon.” Tanimu yace “Allah ya ƙara daukaka ka, zuciyarka mai kyau ce shi yasa Allah ba zai barka haka ba.”
Fitowa suka yi suka shiga adaidaita suka yi hanyar gida, suna parking ya hau kan kekenshi sai ga motar Zeey tayo kwanar, bai san sanda ya saki murmushi ba, ya kalli Tanimu yace “Ka wuce gida ni zan ƙarasa, juyawa yayi shi kuma ya tsaya har sai da ta kashe motar, kafafuwanta ta zuro idanuwanta na kanshi shima haka, kafin ta fito ta maida kofar ta rufe.
Kasa ɗauke ido yayi daga kanta ganin abayar daya saya mata ce ta saka, bai ƙara ganin kyan abayar ba sai yanzu da ta saka, tayi kyau har ya rasa me zai ce.
Ido ta ɗan lumshe tana murmushi kafin ta fara takowa inda yake, sai data zo kusa dashi tace “Na sani nayi kyau kar mutanen waje su gane ka kasa ɗauke ido daga kallona.”
Tana kaiwa nan tayi ciki, a bakin ƙofa ta ɗan tsaya sannan ta waigo sannan tayi mishi murmushi tayi mai ƙaramin gwalo, sumar kanshi ya shafa yana jin wani yanayi wanda ba zai iya fassarawa ba, fuskarshi ya shafa sannan ya sake murmushi yabi bayanta.
Dada ce take cewa “Zainabu na! Lale lale kai ina zaki haka kika sha kyau? Ba dai wurin saurayinki zaki ba?” Ta gefen ido ta kalli inda Baqeer ke tahowa tace “Ya riga ya ganni Dada yana gama ganina nazo kema ki ganni.”
Nan da nan yanayin fuskarshi ya canza, ya tamke fuska sosai da kayanshi daya bata zata je Junaid ya ganta? Dada ce tace “Shiga falo ki zauna bari na ƙarasa abu.”
“Dada kema ki dinga hutawa don Allah, ni kam na kai shekarunki bani ba girki.” Dariya tayi tace “To ai gwara na motsa jikina bana son zaman haka nan, sannan yawanci kinga abinda nake fa ba mai wahala bane.” Zeey ta nufi inda take har zata ce zata tayata ta tuna babu abinda fa ta iya hakan yasa tayi saurin yin kwana tayi falo, Baqeer ranshi a ɓace ya gungura yayi ciki yana kuncini, yana jin Dada na cewa “Wannan kai dai wallahi baka ji daɗi ba, matarka akwai aiki a gabanta.” Bai tanka mata ba ya shiga, Zeey ce ta kalleshi ya ɗauka tana ciki sai ya ganta daga gefen ƙofa kaɗan tace “A dinga sakin fuska dai Ya Baqeer.”
Kallonta yayi duk da yana jin haushinta sai yaga kamar har ƴar ƙaramar rama tayi, jiki a sanyaye yace “Are you okay now?”
Nan da nan yanayinta ya canza, ta girgiza kai alamar a’a tace “I’m not.”
Wani irin sanyi jikinshi yayi maimakon yayi ɗaki kamar yadda yayi niyya sai ya nufi cikin falo ya ja burki ya nuna mata kan kujera dake gefenshi kaɗan ya buga kaɗan alamar tazo ta zauna.
Ƙarasawa tayi ta zauna ya kalleta yace “Meke faruwa?”
Kallonshi tayi zuciyarta na zafi tace “Komai ma ya faru, komai da nake tunanin shine gaskiya ya koma ƙarya, yanzu ban san dame zan yarda ba.”
“Kin yiwa yayanki magana akan mahaifiyarku?”
Kallonshi tayi tace “Itan ce ba neman mu take yi ba.”
“Kunji dalili daga wurinta? Ko ku kun taɓa nemanta?” Idanuwan ta ne suka sake yin raurau alamun son yin kuka tace “Ni naso zuwa wurin danginta amma abinda suke yiwa Mummy yasa naji bana so.”
Maimakon ya bata amsa sai ya kafeta da ido, kai ta sunkuyar da sauri cike da shagwaɓa tace “Me nayi kuma?”
Shi kawai mamaki yake yadda sam basu da mai basu shawara yace “Ki samu time kije da kanki kiji me yasa ita bata nemanku, a matsayinta na mahaifiyarku.”
Kallon juna suka yi……
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*