Sashe 120
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*****
Kwanakin nan bata cikin nutsuwarta saboda ta daina samun Bello a waya ko zata kwana tana nemanshi wayarshi bata shiga, babbar damuwarta yadda kusan komai nata ya ƙare saboda dama ba wata sayayya suka yi mai yawa ba tunda dama a tsarinsu baza su daɗe a ƙasar ba shi yasa suka sayi kayan abinci na adadin kwanakin da suke saka ran zata yi anan kafin ta bishi to gashi kwanakin har sun haura ita bata bishi ba sannan kuma bai turo mata wasu kuɗaɗen da zata sayi wasu kayan buƙatun ba. Tana kwance a parlourn ta wurin yayi kaca-kaca don tun bayan barin Habi gidan bata ƙara saka tsintsiya da sunan shara ba, komai taci anan wurin take barin shi bata ɗaukewa don haka parlourn ya cika da ƙazanta. A gefe ga farantan da take cin abinci nan sun yi tsibi guda don ko su bata iya kawarwa sai dai idan tayi amfani da wani ta ɗora shi akan waɗanda ta tara, ga ledojin tarkacen kayan ciye-ciyenta nan da ribobin lemo da ruwan da take sha sun haɗa wata ƴar ƙaramar bola. Ita kanta idan aka kalleta ba za'a so sakewa ba don ga dukkanin alamu tayi kwanaki jikinta bai ga ruwa da sunan wanka ba, gaba ɗaya tayi biji-biji da ita duk ta fita daga hayyacinta.
Tana kwance tana danne-danne a waya ga alama ita wannan bolar data haɗa bata damunta don chatting take yi da sababbin ƙawayen data yi tana murmushi don sai fasa mata kai suke yi suna cewa ai sun ɗauka da suka jita shiru kwana biyu ko har ta tafi ne babu labari. Turo ƙofar yayi ya shigo parlourn bakin shi ɗauke da sallama yana rataye da jakar matafiya a kafaɗar shi sai akwatin trolley da yake ja a ɗaya hannunshi. Sallamar da yayi ce ta maƙale mishi a maƙohgaro ganin parlourn kamar ba nasu ba, fita yayi ya duba yaga tabbas gidan ne dai ya shigo don haka ya koma ciki yana ƙarewa parlourn da alamu suka nuna kamar babu mutum ɗin dake rayuwa a ciki. A kwance akan doguwar kujera ya ganota. A fusace yace "Asiya miye haka?" Yana nuna tsakar parlourn da hannu. Wai sai a sannan tasan da shigowarshi cikin gidan don hankalinta gaba ɗaya ya ɗauku ga wayar da take dannawa ko kusa bata ji motsin shigowarshi ba. Miƙewa tayi tsaye fuskarta ƙunshe da mamakin ganinshi a daidai wannan lokacin da bata yi zato ba tace "Bello! Saukar yaushe?"
Bin jikinta yayi da kallo sai yaji ranshi ya ƙara ɓaci, bsyan ƙazantar gidan har ma jikinta ba zata iya tsayawa ta gyara ba. Tsaki yayi kawai ya wuce ciki ya barta anan. Bin bayanshi tayi sai ta ganshi a tsaye yana ƙarewa ɗakin kallo. "Tafiya babu sanarwa Bello, hala kazo ka tafi dani ne. Kamar kasan dama na gaji da zaman ƙasar nan wallahi duk na matsu na bika ashe ma kai da kanka zaka zo mu tafi shi yasa bana samunka a waya."
A fusace yace"Dallah Malama yi mini shiru, a hakan zan kwasheki na fita dake ƙasar waje kina zuba wannan uwar ƙazantar, kalli jikinka saboda Allah ki duba muhallinki kamar ba gidan amarya ba komai ya fita daga hayyacinshi tsabar ƙazanta." Kallon kanta tayi ta kalli ɗakin data manta yaushe rabon da a gyara a hakan ma wai shine mai ɗan dama don ba kasafai ta cika shigowa nan ɗin ba, cewa tayi "ya kake so nayi saboda Allah bayan nace maka zan nemo mai aiki saboda aikin yayi mini yawa bazan iya ba kaƙi amincewa."
Ajiye kayan hannunshi yayi zai fita daga ɗakin tace "To yaushe zamu tafi don na fara shiri?"
Wani wulaƙantaccen kallo ya wata mata yace "Ina? Ai babu inda zamu don nima na dawo kenan," kawai ya fice ya barta a ɗakin.
Bin bayanshi Asiya tayi da kallo hankali a tashe tace "Iyyeee.......Bangane ba ba inda zamu je a ina? Ni kaga bari nazo na tattara kayanmu."
Tsaki yai kawai ya cigaba da tafiya, kallan mamaki ta bishi dashi ai ko za'a mutu sai ya fitar da ita daga kasar nan, tab ai bataga yban daya isa ya hanata ba....
Mukam mukace to ga fili ga doki🥴
*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA UKU*
{73}
Duk da Baqeer yasan zai yi missing ɗin Zee in ta tafi amma wata irin nutsuwa da jin daɗi yake ji, tabbas a matsayinta na mace tana buƙatar ta nemi mahaifiyarta sai dai in ita mahaifiyar ce ta nuna bata son zuwan nata, yau yana tashi ya tuna yau ne zata wuce, tun yanzu ya fara jin rashinta ya fara damunshi, wayarshi ya ɗauka ya tura mata text _Karfe nawa zaki wuce?_ Ba dadewa sai ga reply _11am In Sha Allah_ ajiyar zuciya yayi ya maida wayar, wani saƙon ne ya ƙara shigowa _In na dawo ina son jin amsar tambayar da nayi maka_ murmushi ne kawai ya bayyana a fuskarshi don shi kanshi amsar yake son bata, ganin bai yi reply ba yasa ta shiga wanka, tana fitowa ta shirya cikin atamfa anyi mata ɗinkin doguwar riga tasha kwalliya da stones tayi kyau sosai, bata son ɗaura ɗankwali hakan yasa tasa ƙaramin mayafi tayi rolling sannan tasa abaya buɗaɗɗiya a sama, fitowa tayi daga ɗakin, gidan yayi shiru kamar ba mutane a ciki, ita kaɗai tayi breakfast shi yasa kawai taci toast bread da tea, ji take yi komai baya yi mata daɗi a gidan, ƙofar ɗakin Mummy taje tana tafe tana tuno irin tsananin ƙaunar da Mummy take nuna mata, ta tabbatar wannan abinda take yi mata dole in taga ta shareta abun ya dameta. Hannu tasa ta murɗa ƙofar ɗakin ta tura a hankali, a duƙunƙune ta ganta tana bacci da alama sanyi take ji, bargo ta janyo ta lulluɓa mata cike da tausayin halin da suka tsinci kansu sai dai bata ji zata iya yafe mata yanzu kila dai in taje wurin Ummi ta dawo. Juyawa tayi ta fita bayan ta sanar da masu aiki akan su kai mata abinci anjima sannan in bata ci ba su sanar da Kabir. Motarta ta shiga tana ganin saƙon Daddy wai zai turo driver ya kaita da sauri tayi mishi reply akan ita da kanta take son zuwa don Allah ya barta. Tayi sa'a daya ce mata Allah ya kaita lafiya ta tabbatar ta kira shi in ta isa. Haka ta fito daga gida tana tafe tana tunanin yadda zata yi magana da mahaifiyarta don kuwa ita ko gidan da take aure bata sani ba, shekarun baya sukan je Dambatta amma tunda dangin mahaifiyarta suka fara tsangwamar Mummy sai taji sun fita daga kanta gaba ɗaya, hakan yasa ta tattarasu ta watsar dasu.
Wayarta ta kalla wanda kiran Junaid ya shigo maimakon ta ɗauka sai ta kifa wayar ta cigaba da tuƙin ta, tana tausayawa Junaid sai dai ba zata sadaukar da kanta akan abinda tasan ba zai sanyashi farin ciki ba, ita mace ce da in har ba ta son abu to fa bata iya ɓoyewa, haka zalika in tana son abu kana iya gani a fuskarta, shi yasa har yanzu take mamakin yadda Baqeer ya kasa gane son da take yi mishi, ajiyar zuciya tayi ta cigaba da tuƙi ai ya dai yi ya gama in ta dawo zasu yita ta ƙare, bazata bari suyi ta tafiyar tatata haka ba.