Sashe 95
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
*****
Sai da Badaru yayi kwana biyu yana jinyar jikinshi kafin ya warware, Jamila ce tayi fama da jinyar a gefe guda kuma tana ƙara yi mishi famfo tana nuna kamar duk gidan babu wanda ya damu dashi idan ba ita da ƴaƴanta ba. Yana samun kanshi ya tada tijara ko Kamalu ya fito mishi da takardun filinshi ko su fice su bar mishi gida daga shi har Abu data take ɗaure mishi yana yi mishi sata, sai dai fa daga nesa yake duk wata tijara tashi ko kusa da Abu bai je ba bare Kamalu don yana tairon kada ya taɓa ita kanta Abun Kamalu yayi mishi ƙamshin mutuwa don yaga alamar babu imani a tattare dashi tunda har zai iya saka hannu yana neman lahanta shi in banda Allah ya kiyaye. Yana daga ƙofar ɗakinshi yace "Kinga Abu tun muna shaida juna ki faɗawa ɗanki ya fito mini da takardun fili na idan ba haka ba alƙali ne zai rabani daku don wallahi bazan yarda na ɗauki asara ba, haka kurum don rashin tausayi tun yana yi mini ɗauki ɗaiɗaya a shago har ya fara biyo ƴan kadarorina yana kaɗarwa, to bazan lamunta ba tunda dai bada uban kowa na haɗa na nemi kuɗina ba ah to."
"Ba dai ubana kake neman ka zaga ba dai ko Mallam?" Tayi maganar cikin ɗaga murya don Kamaku yana ɗakinshi a kwance tana fatan ya jiyota ko ya fito Mallam ya ganshi tunda ta lura kamar yanzu tsoron Kamalun yake ji. Kamar yasan abinda take shirya mishi ya waiwaya ya kalli hanyar soron gidan inda ɗakin na Kamalu yake, murya ƙasa-ƙasa kamar ba shine yake hayagagar nan ba yace "ke fa da neman magana kike, Kawun nawa zan zaga don baki da hankali to na zagi Kawu nace na zagi wa. Ni dai ki lallaɓa ɗanki don Allah ku fito mini da takardun nan ko na samu na ƙara jari idan ba haka ba wata rana abincin da zamu ci ma sai ya gagare mu don kullum kasuwar tawa ƙara ƙasa take yi."
Sai data murguɗa baki gefe sannan tace "Wai har yanzu kana nan akan bakanka na Kamalu ne ya ɗauke maka takardun fili? Haba Mallam to Kamalu ya sace maka takardun fili yayi me dasu? Gaskiya ka nemi ɓarawon filinka a wani wuri amma ba Kamalu ba don ni dai babu ɓarawo a ɗakina." Takaici ne yasa Badaru kasa sake cewa komai amma ba don ya haƙura ba don ya lura kamar da haɗin bakin Abu Kamalu yake yi mishi sata shi yasa bata so ana faɗa amma wallahi akan takardun filin nan tsaf zai ture zumuncinsu a gefe ya shigar da ƙararsu har ita Abun a wajen alƙali har sai sun fito mishi da takardun shi don kuwa dai ba yarda zai yi ba.
Duk abinda suke yi Umma na daga ɗakinta tana jin su, da har zata faɗawa Badaru gaskiya ita ta ɗaukarwa Baqeer takardun filinshi ta kai mishi kuma har ya sayar yayi amfanin da zai yi da kuɗin don ya daina ƙalawa mutane sata sai dai ta rabu dashi don ba yanzu take son yasan ita ta ɗauka ta bawa Baqeer ba don a yadda ya manta yana da ɗa mai wannan sunan ba taso ya tuna dashi har sai a gaba zuwa lokacin da zai yi dana sanin da baza tayi mishi amfani ba. Tashi tayi ta karo ƙofar ɗakinta ta rufe don bama taso ta dinga jin tashin muryarsu daga nan inda take, zama tayi ta ɗauki radio ɗinta ta kunna tana sauraren shirye-shiryen da ake gabatarwa a lokacin.
*****
Tun ɗazu take dakon dawowarshi har kusan ƙarfe sha ɗay da rabi na dare sannan taji ƙarar buɗe gate, sai taji tsayuwar mitarshi har ma da fitarshi daga cikin motar ya rufe sannan ta tashi cikin sanɗa ta fita ta samu wuri daidai ƙofar ɗakin shi ta inda ba zai ganeta ba saboda duhu gashi fitilun wajen duk a kashe suke. Ta gabanta ya wuce sai dai sam bai lura da ita ba har yasa makulli ya buɗe ƙofar ɗakinshi ya shige da sauri kamar mai gudun kada wani ya ganshi sai dai abinda bai sani ba shine wacce yake gujewa na biye da shi a baya, ya turo ƙofar zai rufe tayi sauri tasa hannu ta tare, gabanshi ne ya faɗi daya ganta a daidai wannan lokacin. Sakar mata ƙofar yayi kawai ya koma cikin ɗakin don har ya gaji da yawan yin jayayya da ita tunda yayi-yayi da ita ta fahimci babu wani alfanu a cikun taraiyarshi da ita ta kasa ganewa. Uffan bai ce mata ba ya ɗebi kayan baccin shi ya shige banɗaki ya rufe ƙofar haɗe da saka mata key don yasan a yadda Nabila ta mayar da kanta ƙadan da aikinta ne yaga ta shigo mishi banɗaki alhalin tasan wanka yake yi. A cikin banɗakin yayi wanka ya shirya sannan ya buɗe ya fito, bai yi mamaki ba da yaga har wannan lokacin Nabila na zaune a cikin ɗakinshi bata da alamun tashi ta fita. Sai da ya gama dukkan wasu al'adun ahi na kwanciya sannan yazo ya zauna a bakin gadon yace "Ya aka yi?" Yana ɗage mata gira da sigar tambaya. Kallinshi tayi taga yadda yake kawar da kai baya so ko ido su haɗa saboda yadda ta takura rayuwarshi tace "tun safe nake jiran dawowarka saboda ina da wata muhimmiyar magana da nake so muyi har kiranka nayi a waya don naji lokacin da zaka dawo amma baka ɗauka ba."