← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 168

Sashe 27

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Kamalu ne ya diro daga kan gadonshi cike da jin daɗin wayar da aka yi mishi cigiyar Zeey daya bada aka ce an gano gidansu, ba zai iya jira ya watsa ruwa ba hakan yasa ya shiga fesa body spray sai daya kusa ƙarar da shi ya cillar anan tsakar ɗakin sannan ya zura wando da riga yana yi yana taka rawa, kallon Baqeer yayi dake zaune yana karatun Qur’ani yace “In an kawo abincina a ajiye mini zance zani.”
Ko kallonshi Baqeer bai yi ba balle yasa ran zai amsa mishi, a kufule ya naushi iska da ƙafa saitin inda Baqeer yake yace “Gurgu kawai.”
Fitowa yayi bai kula da motar dake gefen gidan ba ya hau babur ɗinshi yayi gaba.

*****
Abu a tsakar gida sai girki take tana zabga nishadi din tabbas jiya Malam ya tsunduma a tarkonta jinta take yi kamar wata yarinya ƴar shekara ashirin da biyar, yo dama ina zata yarda ace wai don ta girma shikenan baza ta ɗana sakalci ba? Jiya ta tabbatar da kalmar da ake cewa maza basa girma.
Jamila sai kallonta take yi tana binta da harara don yau sai 12 na rana Malam ya fito daga ɗakin Abu wanda kuma baya yi musu hakan ko a lokacin da Fatima take ƴar gaban goshinshi, ta tabbatar wani makircin ta sake yi ta barta a gefe.
Fatima ce ta fito daga ɗaki ganin Salim har rana babu shi babu labarinshi, ta tabbatar Baqeer na neman taimako don da asuba da ƙyar ta lallaɓa su Bashir suka taimaka mishi yaje banɗaki, Abu ta kalla tace “Abu dan Allah ko zaki yiwa Kamalu magana ya taimakawa……”
“Aye yare aye nayi yara ye iya aye yare munga idon wasu yara ye iye, wasu gasu can ba ƙafa yara ye iye, sai bi suke a taimaka yara ye iya to in kunsan da haka? Yara ye iye meya sa baku yi biyayya ba tun farko?” Waƙar da Abu take yi ne yasa Fatima kasa ƙarasa maganar da take yi, Jamila ta sheƙe da dariya suka tafa tace “Kai Abu yaushe kika zama mara kirki haka?”
Fatima ta share ƙwallarta ta zura hijab ta leƙo waje, Zeey dake tsaye bakin mota tana saƙar shiga da warwarewa akan ta koma gida ta hangota, kallo ɗaya tayi mata ta tuna Umman nan ce dai mai ƙaunarta, murmushi ta saki tana jin sanyi a ranta, da sauri ta fara takowa wurin daidai nan wani yaron almajiri yazo wucewa Umma tana cewa “Dan Allah bawan Allah ka taimaka ka dubo mini Salim a gidan can. Ko kuma in akwai almajirin daya fika girma ka kirashi kace zamu biya ya taimaka mana.”
Yaron na juyawa idanunta ya kai kan Zeey, sam bata ganeta ba hakan yasa ta nemi juyawa da sauri Zeey tace “Umman mu?”
Da mamaki ta kalleta, nan idanuwanta suka fara mata alamun kallon sani, Zeey ce ta rungumeta tace “Nice Zainab fa? Zainabun ki.”
Da mamaki ta ɗan zareta tace “Zainab? Kece?”
Kai ta ɗaga tare da sake rungume Umma, cike da jin dadi suka shiga cikin gidan, Jamila ce ta watsawa Zeey kallo ganin shigar dake jikinta tace “Ha’a ba dai ita ce wacce Baqeer ke zancen zai aura ba? Ta shigo mana ganɗarɗar haka?”
Umma tace “Ba ita bace wannan….”
Hannun Umma ta riƙe da sauri tare da girgiza mata kai alamar a’a, Umma tasan dalili hakan yasa tace “ƙawar Maryam ce.”
“Oh na ɗauka ai budurwarshi kika ɗauko don ta taimaka mishi.”
Kalaman ta sun konawa Umma rai sai dai bata da damar amsawa. Abu dake zuba maganin mata a jarkoki tace “Wai ma kin dubashi ko? Kin san zai iya gangarawa ba tare da an sani ba tunda ba kafafun guduwa.”
Gaban Umma ne ya faɗi wanda yasa tayi hanyar ɗakin da sauri tana tafe tana addu’a.
Bin bayanta Zeey tayi don da alama ba lafiya ba, bata tsaya maida ƙofar ba ta tura ɗakin da sauri zuciyarta cike da tsoro.
Baqeer ta samu a zaune ya rufe idanunsa gam hannunshi na hagu ya cukwikuye takardar zane da ita, ƙasan ɗakin duk pencils ne a zube an watsar.
Da sauri Umma ta ƙarasa ta riƙo shi tace “Baqeer menene? Meya faru?”
Zeey jin Umma ta ambaci sunan Baqeer yasa ta nemi juyawa da sauri, idanuwanta ne suka hango mata keken guragun dake gefen katifar shi, gabanta ne yayi wani irin faduwa nan da nan jikinta ya fara rawa, kalaman Umma ne suka sake rikitata “Baqeer kayi hakuri ban san ina Salim yake ba, na aika dai yanzu a kira shi zai zo ya taimaka maka, wannan bala’in da muka shiga Allah ya fitar damu Baqeer rashin ƙafar nan taka na daga mini hankali, sai yaushe zanga ka dawo Baqeer mai yawan fara’a?
Zee bata san sanda tayi karo da bango ba, Baqeer? Umma ce ta waigo ta kalleta tace “Zainab kin tsorata ko? Ƙaddara ce ta afka mishi.”
Zeey tana kallonshi tana girgiza kai, Baqeer? Baqeer data sani wanda kwarjininshi yasa take tsananin shakkarshi? Wanda kusan kullum sai ya sakata kuka ba tare da ya damu ba? Wanda akan baƙar maganar da yake yi mata har zazzabi take yi? Wanda a dalilinshi abotarta da Maryam ta yanke? Ina Baqeer ɗin data sani da har zai bari mace ta wulaƙantashi? A nemi illatashi a titi? Meke faruwa? Ƙwaƙwalwar ta sam ta kasa gasgata abinda ke faruwa cikin wata murya tace “Umma meya faru haka?”
Muryarta daya ji ne yasa shi buɗe idanunshi da suke rufe gam a hankali ya saukesu a kanta, wacece wannan dake bibiyarshi? Yanzu kuma har gida? Ya aka yi ma tasan Ummanshi?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer
#Shalele
#Zeey
# RayuwadaKaddara
#Hawayena
#UMMASGHAR
#AYUSHERMUHD

*BAQEER*
     *NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI*

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199
07068558096

{17}
Taku biyu tayi baya, tsabar rudanin data shiga yasa ta fice daga cikin gidan a gaggauce ba tare data tsaya jiran fitowar Umma ba, jikinta gaba ɗaya rawa yake yi ta rasa takamaimai abu ɗaya da zata kama. Haka nan dai taja jikinta da yayi wani irin sanyi ta ƙarasa wajen data ajiye motarta ta buɗe ta shiga ciki ta zauna, ta daɗe zaune a cikin motar da ƙyar ta iya saka makulli ta tashi motar ta bar wurin, har ta ƙarasa gida zuciyarta nata kai kawo akan abinda ta gani yanzun nan, kasa fita tayi daga cikin motar sai ma kifa kanta da tayi a jikin stearing wheel tana tunanin to me ya faru dashi haka? Ita dai tasan lafiyayyen mutum ne mai ji da ƙarfi to garin yaya ya zama gurgun da sai an turashi akan wheel chair? Kai Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, abun duniya ya dameta duk ƙoƙarin da take yi na kawar da tunanin shi daga ranta ganin tun da can babu wani shiri a tsakaninsu bare damuwar halin da yake ciki ta dameta ta kasa sai ma ƙara kutse da tunaninshi yake yi cikin zuciyarta.

Tsaki tayi cikin ranta tana cewa "to wai ni miye ma damuwata ne da daga ganin mutum zan bi na rasa sukuni?" Tunanin hakan yasa ta ficewa daga cikin motar ta shiga gida sai dai duk da hakan ta kasa yakice ganin da ta yiwa Baqeer akan keken guragu a zaune daga ranta. Da murna Mummy ta tareta ganin yau ɗaya dai Zeey taji maganarta ta dawo gida da wuri don tun fitarta take zullumin kada Daddy ya dawo bai tarar da ita ba bayan ya hanata fita ko ina, tasan da ba ƙaramin ɓacin rai hakan zai janyo mata ba sai kuma ta taimaketa ta dawo kafin Daddyn. Akan doguwar kujera ta zube ta kwanta ba tare da ko takalman ƙafarta ta cire ba, kallon tsaf Mummy tayi mata ta lura kamar da akwai abinda ke damunta sai dai ba tayi magana ba sai ma tayin abinci da tayi mata ganin har ta fita bata yi lunch ba.
Chapter 27 · 0% Book details