← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 168

Sashe 139

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kabir yana shigowa ɗaki ya shiga ya dinga zarya a cikin ɗakin, tsoro duk ya hanashi sukuni, daga cikin ɗakin yake jiyo fadan Daddy akan zuwan Badaru, hankalinshi ne ya ƙara tashi ya leko ya ɓoye a jikin ƙofa yana ji Mummy na kareshi, Daddy ranshi a ɓace ya shiga ɗaki bai daɗe ba sai gashi da key ya fito ko kula Mummy bai yi ba yayi waje, taya ƴar yafi so a rayuwarshi zata janyo mishi ɓacin rai haka? Dan ƙaunar da Daddy yake yiwa Zainab a bayyane take kawai baya son nunawa ne amma ita kanta Zee ɗin ta sani.
Yana fita Kabir ya fito kana kallon yanayin fuskarshi zaka san lallai yana cikin tashin hankali don idanuwanshi duk sun jame, bakinshi na rawa yace “Mummy yaron nan zuwa yayi maganar bugeshi da nayi ko?”
Kallonshi tayi tace “Muje ciki.” Tayi maganar tana kallon ɗakin Zee wanda taga alamun za’a buɗe, ɗakin Mummy suka yi yana shiga yace “Mummy meke faruwa? Zancen bugeshin da nayi ne?” Ajiyar zuciya tayi tana ɗan kallon ƙofa don basu rufe ba tace “Kabir ba wannan ya kawo shi ba sai dai yanzu in har aka san abinda kayi bayan abinda ya faru to lallai akwai gagarumar matsala.”
Cike da rashin fahimta yace “Ba hakan bane?”
Hannu tasa ta shafi fuskarta tace “Gaisuwar surukai yazo Zainab yake so.” Ido ya zaro hankali a tsananin tashe yace “What? Zainab? Bata da hankali ne zata ce tana son Baqeer? Gurgu ne fa? Sannan taya zata wulaƙanta mutane da yawa tace yaron nan take so?” Gaba ɗaya magana yake yi cikin ɗaga murya yana yi yana tafiya yana yarfe hannu don mamakin abun nan ya isheshi wai Zainab, Mummy ce ta kalleshi tace “A bar maganar Zee nasan shi yana sonta, yanzu me kake tunani zai faru in har tasan kai ka bugeshi, in har tasan kaine silar rasa ƙafar shi da yayi.
Ƙofar da aka ƙarasa turawa itace tasa su waiwaya su kalli wurin, Zainab wacce jin fitar Daddy yasa ta fito don ta yiwa Mummy magana akan zata je ta bawa Baqeer hakurin wulaƙancin da Daddy yayi mishi kunnuwanta suka jiye mata wannan mummunan labarin, hawaye ne kawai suke gudu a saman kuncinta don kamar wanda ake korosu haka suke zubowa, Mummy da Kabir ma hankali a tashe suka kalleta, da sauri Mummy ta nufo inda take, hannu ta ɗaga mata alamun karta ƙaraso inda take sannan ta juya da sauri daga ita sai material ɗin ɗazu sai ɗankwalin kanta, ta fizgo mayafi da wayarta, kallon drawer ɗin gefen gado tayi ta ɗauki key ta fito da sauri, Mummy ce tace “Zainab!” Ko kallonta ba tayi ba tayi waje da gudu, mota kawai ta shiga mai gadi ya buɗe ta fita daga gidan da gudu, gudu kawai take don saura kaɗan ta buge wani mai yalo dake tura baro, birki ta taka da ƙarfi ta kifa kanta a sitiyari tana maida numfashin dake fita da sauri da sauri, da ƙyar ta iya buɗe ƙofa ta fito ta bawa mai yalo haƙuri sannan ta komo mota, tana tafe kuka kawai take yi. Ina zata kai son Baqeer da tausayinshi? Taya za’ace yayanta shine ya ja mishi abinda ya faru dashi? Hawaye kawai take yi tama rasa ta ina zata fara tunanin abun yi, tausayin Baqeer ne fal cikin ranta wanda take ji ya riga ya gama bin duk wasu gaɓoɓi dake jikinta.
Bata san inda take jan mota ba don tuƙi kawai take yi, ga mamakinta sai ganin kanta tayi a ƙofar gidansu Dada, kanta kawai ta kwantar a kan kujerar ta runtse ido, to ita dama ina take dashi na wurin zuwa banda nan? Kasa fita tayi daga mota sai hawaye kawai da take yi, tafi minti sha biyar a haka sai kuma taji zuciyarta na son ganin Baqeer yanzu kam ta tabbatar babu ita babu shi don in har yasan Kabir ne ya ja mai nakasa to fa ita dashi kila har abada. Ciki ta shiga ta tsaya daga daidai ƙofar shiga tana goge fuskarta, sai dai idanuwanta kaɗai  zaka kalla kasan tasha kuka, tana shiga taji Dada na faɗa tana cewa “Mutum sai kace yaro, komai aka baka kace baza kaci ba, in har kaje gaisuwar surukai ba’a dace zuwan farko ba ai haƙuri ake yi sai a ƙara gwadawa, to ni dai ga abincinka nan in kaga dama sai ka buɗe ɗakin,” tana kaiwa nan ta ajiye kwanon a bakin ƙofa tana waigowa taga Zainab a bayanta, da sauri Zainab ta rungumeta kamar dama jira kukan da take so tayi yake kawai ta fashe da kuka. Kuka take yi wanda in kaji sai ka tausaya mata, shafa bayanta kawai Dada take yi cike da tausayin halin da suke ciki wanda ita aka barta a duhu bata san meke faruwa ba.
Tun daga ciki yake jiyo kukan wanda ya ɗaga mishi hankali, saukowa yayi daga kan gado ya hau kekenshi zuciyarshi na wani irin zafi ji yake kamar yaje ya rungumeta ya bata haƙuri, turo keken yayi cikin sauri yazo daf da jikin ƙofa hannu yasa ya buɗe ƙofar din zuciyarshi ta kasa haƙuri da abinda yake ji, da yake tana rungume da Dada fuskarta tana kallon saitin ƙofar ɗakin, cike idanuwanta suke da ƙwalla take kallon ƙofar da aka buɗe sai dai bai leƙo ba.
Dada ce jin shirunta yasa ta zareta daga jikinta tace “Ba komai In Sha Allahu zai yarda shima Baqeer ba laifi yayi ba Allah ya ƙaddaro mishi hakan,” tayi maganar tana kallon inda Zee ke kallo, ganin Baqeer ya buɗe ƙofa yasa tace “Asha na manta na bar abu a kitchen,” tayi maganar tana yin kitchen ɗinta dake waje.
Zee a hankali take takawa har jikin bangon ɗakin tsugunawa tayi ta ɗauki kwanon abincin da Dada ta ajiye, ba tare da ta miƙe ba ta ɗago suka haɗa ido, idanunshi yayi ja sai dai ita idanunta cike suke da hawaye wanda suka sauko daidai sanda ya kalleta, sharewa tayi tana murmushi tace “Mantawa nayi ban tambayeka ya ka ganni ba bayan kaji wacece ni,” tayi maganar cikin hawayen da take ta ƙoƙarin tsaidawa, yanayin maganarta kaɗai zai sa kasan lallai tana cikin babban damuwa, murmushin yaƙe yayi yace “Shi yasa ban ganeki ba Abulele.” Ta jinjina kai tana goge fuskarta tare da yin wata dariya mai cike da ban tausayi tana cewa “Me na canza?”
Shima murmushin yayi yace “Komai, sai dai da alama ba kya cin abinci ne yasa kika rame haka.” Ta ƙara yin ƴar ƙaramar dariya tana jan hanci tace “Randa na fara ganinka nima ban ganeka ba.”
Kai ya jinjina don yana ji in har yayi magana zata fahimci rawar da muryarshi keyi, ta sadda kai tace “Da wannan, da kuma girma,” tasa hannunta kan hannun kujerar guragun, kai ya sake jinjinawa yana cewa “Umm!”
Hannu biyu tasa tana maida kwallarta tare da goge ƙasan idanunta tace “Da alama bazan ƙara ganinka ba ko?”
Kai ya ɗaga mata alamar eh, ta haɗiyi wani abu mai ɗaci tace “Hmm na sani, amma kayan da aka bani an bar mun ko?” Kai ya ɗaga mata alamar eh, gaba ɗaya tausayin kansu ya isheshi. Murmushi tayi ta miƙa mishi kwanon abincin da ɗaya hannunta na dama wanda tasa kwanon a saman cinyarta, hannu ya kai ya amsa yasa a jikinshi. Kallon juna suka yi ta miƙe tsaye tana haɗiyar wani abu mai ɗaci wanda ta rasa daga ina yake ziyartar makogwaronta, da sauri ta juya baya don ji take baza ta iya riƙe hawayenta ba, Ya Kabir bai kyautawa Baqeer ba, an san da tsautsayi, ya zata yi ta sanar da Baqeer akan Kabir ne ya janyo mishi zama gurgu?
Dada dake kitchen duk jikinta yayi sanyi ita kam meke faruwa da har yayi zafi haka? Ta ɗauka kawai dai iyayenta ganin gurgu ne shi yasa suke jinkirin basu ita amma yanzu ta fara tunanin akwai abinda yafi haka.
Zee ce ta waigo suka haɗa ido da Baqeer kowannensu abinda zuciyarshi ke aika mishi daban, saƙo ne mai zafi da ƙuna wanda muhimmancin junansu da ƙaunar da suke yiwa juna ya tarwatse lokaci ɗaya.
Kasa jurewa tayi kawai ta juya da sauri ta fita, ƙofar kawai Baqeer ya maida ya rufe ya jingina da ƙofar tare da runtse ido, ta ina zai fara? Lallai babu inda soyayyarsu zata kai, laifin da ya aikata aka kulle Badaru a cell sai da yayi kwana ɗaya ana biyun aka sallameshi kaɗai ba zai bari a bashi aurenta ba.
Abubuwan da suka faru a baya ne suke dawo mishi…….Itama Zainab tana shiga mota taja tana tafe abubuwan da suka faru ke dawo mata.
Tuna Baya……

Asalin iyayen Alhaji Suleiman ƴan Ƙaraye ne sai dai zama daya dawo dasu cikin garin Kano. Mahaifinshi mai kuɗi ne don babban ɗan kasuwa ne a kasuwar kantin kwari. Shi kuwa asalinshi ɗan cikin birnin Kano ne, anan unguwar aka haifi iyayenshi da kakanninshi anan suka taso suka girma har suma suka yi nasu gidajen anan cikin unguwar, bai san wani wuri da zai kira da asalinshi ba bayan nan. A rayuwar Badaru babu abinda yake ƙauna irin karatun boko gashi Allah yayi mishi baiwa da iya zane, tun yana zane akan ƙasa ko ya samu gawayi ya zane sumuntin dakalin gidajen mutane har ya fara sayen pencir da littafi yana yin zanen akan takarda. Yaso mahaifin shi ya barshi yayi karatun boko inda zai faɗaɗa ilimin shi akan harkar zane mahaifin nashi yaƙi, babu irin roƙon da bai yi mishi ba amma sam yace ɗanshi ba zai je makarantar boko inda ake koyawa yara kafurci ba.
Chapter 139 · 0% Book details