← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 168

Sashe 121

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*****
Baqeer yau yana da appointment hakan yasa ya shirya da safe Tanimu yazo suka je, ga mamakinshi office ɗin Junaid aka kaisu, sunfi minti goma suna jira kafin yazo, nan yace Baqeer ya biyoshi, haka Baqeer ya gungura kekenshi suka nufi ciki, Junaid ya zauna yana sa Baqeer yayi gwaje-gwajen abinda ya umarceshi, kafin daga bisani shima ya zo da kanshi ya duddubashi, kallon Baqeer yayi bayan sun gama, fuskarshi sam babu walwala yace "Akwai wani abu ne tsakanin ka da Zainab?" Da mamaki Baqeer ya kalleshi, sai dai haka kawai yaji ya kasa bashi amsa a ganinshi wannan tambayar ba shi ya kamata yayi wa ba, Junaid ya ɗan kauda kai yace "Of course nasan ba kai bane kenan akwai wani?" Sake kallonshi yayi duk da zuciyarshi na son sanin me yake nufi da kalamanshi sai dai haka kawai yaji ba zai iya tambaya ba, Junaid ya sauke ajiyar zuciya yace "Baqeer please naga Zainab na ganin girmanka da kula da kai kamar yayanta me zai hana ka bincikomin wanda ke hure mata kunne yake neman hanata bin umarnin iyayenta?"
Yanzu kam yanayin kallon da Baqeer yake yi mishi ya canza, kallo ne mai alamar tambaya wanda da alama Junaid ya fahimci kallon da yake mishi, ya ɗan miƙe tsaye yana sa hannu a aljihunsa yana cewa "Tana da gardama ne ban san ya zan yi ta fahimceni ba, wannan dalilin yasa nace yau a turoka wurina,” ya ƙarasa maganar jiki a sanyaye, yana ƙoƙarin matsawa daga wurin yaji ance “Babu komai a tsakaninku kenan ko me?” Da mamaki ya waigo suka yi wa juna kallon kallo shi da Baqeer, kallon da su biyun kaɗai suka san ma’anarshi sai dai gaba ɗaya Junaid ji yayi ya kasa bada amsa, sai kauda kai da yayi wanda hakan yasa Baqeer ya tabbatar da amsar da yake son sani, a hankali ya saki siririn murmushi wanda da alama bai san sanda ya fito daga ƙasan zuciyarshi ba. Ba tare da yace komai ba ya fara tura kekenshi zuwa ƙofar fita, ina ma Zee tana nan ya ruga ya sanar da ita ƙaunar da yake yi mata? Dariya ma kalmar Junaid ta bashi wato ya binciko kanshi kenan ko me? Don ya tabbatar in har Zeey ba Junaid take kulawa ba to tabbas akwai sonshi a ranta kamar yadda yake sonta, ya daɗe yana ganin sonshi a ƙwayar idanuwanta sai dai in ya tuna soyayyarsu da Junaid sai yayi tunanin tausayi ne, wani tausayi ne ake tambayar matsayi? Abinda yaji zuciyarshi ta tambayeshi kenan, wani murmushi ya karayi ji yake yi tun yanzu ya ƙosa ma ta dawo ya fallasa mata abinda ke ranshi don wannan maganar dole sai gashi gata. Kamar ya kirata a waya sai ya fasa tunowa da yayi tana hanya, nan suka wuce shago, sun kammala ɗinki na biyu suka sake jera kayyakin da Salim ya kawo musu, suna yi yana ɗan sakin murmushi wanda yasa Salim kasa jurewa yace “Wai hala Zainab tazo yau?” Da mamaki ya kalli Salim yace “Me kake nufi?” Cigaba yayi da aikin yana cewa “To Malam Baqeer ai in dai aka ganka kana murmushi kwanan nan to tabbas akan Zeey ne.” Nan da nan ya tamke fuska yace “Me kake nufi?”
Dariya Salim yasa yace “Ah to ku za’a tambaya ai ba wani ba,” yayi maganar cike da zolaya.

******
Mumy kam bata tashi ba sai karfe sha biyu don dama sai wajen goma ta sake kwanciya, ganin bargo a jikinta yasa tayi saurin miƙewa tana tunanin Senate ne ya shigo tana bacci, sai dai tana shiga ɗakin shi ta tabbatar ba shi bane, jiki a sanyaye ta juyo ta nufi ɗakin Zee don babu shakka in dai ba shi bane to Zainab ce, shiga tayi sai dai babu alamar Zainab a ɗakin ga dai ɗakin nan an gyarashi tas wanda hakan yasa tasan mai aiki ce tayi, fitowa tayi ta nufi kitchen tana kiran Karima wacce tasan sun jitu da Zainab. Da sauri ta fito ashe itama wurin Mummyn zata je ta kai mata breakfast tunda taga ta farka ta shigo don ta tattara kayan abincin, Mummy ta kalleta tace “Ina Zainab?” Kai tsaye tace “Ta fita Mummy tun ɗazu.” Idanun Mummy na kanta tace “Ina?” Kai ta girgiza wanda hakan yasa Mummy juyawa don tasan dama ba zata san inda take ba, Kabir ta hango sanye da jeans da long sleeve shirt da key a hannunshi yana ɗan kaɗa su yadda ya saba, tayi saurin cewa “Kabir baka yi breakfast ba zaka fita.” Waigowa yayi ya kalleta don shi bai masan me zai ce mata ba, neman juyawa yake yi tace “In har Zainab bata fahimceni ba kai dai bana ji ya kamata ka ƙi fahimtata, Kabir ka manta abubuwa nawa na ɓoye sirrinka? Sai ni don na ɓoye nawa sirrin ƙwaya ɗaya shi kenan sai ka kasa yafe mini?” Cak ya tsaya sai kuma ya waigo, nan da nan jikinshi yayi sanyi, ganin haka yasa ta tako inda yake tace “Kai bai kamata kayi mini haka ba, Kabir ka sani bazan iya furta kalmar bane shi yasa na ɓoye bawai don inaso ba, nasan nayi laifi amma sai ku duba zaman amanar da muka yi ko?”
Murya cikin sanyi yace “Mummy na sani sannan zan huce ki bani kwana biyu don Allah, nasan dama Nabila ba da izininki tayi abubuwan nan ba.” Kai ta jinjina alamar fahimta kafin tace “Zeey fa? Na duba bata nan.”
Tsaki yayi yace “Dambatta taje.” Wayar Mummy dake hannunta ce taji tayi mata nauyin ɗauka wanda sai jinta suka yi a ƙasa, hannu yasa ya ɗauko ya miƙa mata sannan ya kalleta yace “Mummy?” Murmushin yaƙe tayi tace “Daddynku ya barta?” Ɗan wani motsi yayi da bakinshi yafin yace “It seems so, don ta tambayeni jiya nace ba zani ba.” Kai ta jinjina kawai ta juya tana tafiya ƙafafunta na ɗan neman kasa ɗaukan ta, ɗaki ta shiga ta kalli abincin da Karima ta ajiye, hannayenta tasa a matse-matsin cinyoyinta kamar mai jin sanyi tana matsasu, tama kasa yin tunanin komai, wayar Zee ta kira sai dai da alama babu network ko wayar a kashe take don taƙi shiga, ajiyewa tayi tare da sake matse hannayenta.
Chapter 121 · 0% Book details