← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 168

Sashe 9

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Assalamu Alaikum*
*Hajiyata kinada labarin kayan Egypt da muke kawowa kuwa to in baki saniba matso kusa kiji Ainam stockpile mun kawo muku kaya na gani na fada na gayu wainda sai wance da wance ake gani dasu ba kano made bane kunsan a koda yaushe burinmu mu kawo muku unique abu.Available ne ba jira zakiyi akawo ba muna bada sari muna kuma aikawa koina,duk abinda kike bukata hajiyata ki latsoni kawai* *wa.me/2348146766440*
*Ko baki siyaba yanzu kiyi saving number ta murika ganin status din juna*
*Nagode*

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, garin yaya ya faɗi?" Tayi maganar tana mai durƙushewa a gabanshi, hannu tasa tana ƙoƙarin juyo dashi don ta fuska ya kife sai dai ta kasa saboda jikin girma gashi kuma ƙarfi ba ɗaya ba. Ɗagowa tayi ta kalli Salim tace "ko zaka fita ka nemo masu taimaka mana a ɗagashi don zai yi wuya mu iya tashin shi daga ni sai kai kawai?" Yana fita ya samu wasu bayin Allah ya roƙesu da su taimaka zasu ɗaga mara lafiya ne ya faɗi. Haka Umma tayi ta musu godiya tana share hawayen tausayin Baqeer da yadda lokaci guda Allah ya juya halittarshi ya tashi daga mai lafiya zuwa nakasashe. Sai a sannan Salim yasan ƙaddarar data afkawa Baqeer ɗin, zama yayi shima yana share hawayen saboda tsananin tausayin Baqeer ɗin daya kamashi. Wai yau Baqeer ne a kwance a haka, mutum mai ji da lafiya da ƙarfi shine ƙaddara ta juyar da rayuwarshi haka.

Haka suka cigaba da zama jugum-jugum babu mai iya magana daga shi har Umman Baqeer ɗin bare kuma shi Baqeer da tunda ƙaddarar nan ta afka mishi ya daina iya magana idan har ba ta zama dole ba, komai aka yi nashi idanu ne saboda shi kaɗai yasan irin ƙuncin da yake ji tattare da zuciyarshi.

*****

A gidansu Baqeer kuwa Jamila ce ta fito tsakar gida tana ta surfa ruwan bala'i akan Umma ta fice tun rana ta bar gidan bata dawo ta ɗora sanwar dare ba gashi har rana na neman faɗuwa dama kuma ba wani abincin kirki ta dafa musu da rana ba saboda tana sauri ta fice ta tafi asibiti wajen ɗan da aka fifita fiye da kowanne ɗa a cikin gidan. Abu tana daga gefe tana yi mata famfo murya ƙasa-ƙasa dama kuma zai yi wuya kaji ana irin wannan faɗan da Abu, ta dai fi kauri wajen haɗa husumar ta koma gefe tana zuga amma ba dai kaji muryarta ba don ga wanda bai san halinta bama ba zai ce da sakun hannunta cikin faɗan da Jamilar take yi ba, dama kuma mafi yawanci ingiza mai kantu ruwa take yi mata, tare zasu kitsa abunsu amma sai ta koma gefe tayi shiru abunta tamkar ba da ita ake yi ba koma ta kama wata sabgar ta daban ita kuma Jamila har yau ta kasa gane halin Abu bare ta daina ɗaukar zugarta.

Fitowar Baban daga ɗaki bai sa Jamila ta sassauta murya daga faɗan da take yi ba don a cewarta ta gaji da rainin wayon da Umman Baqeer ɗin take yi musu, tun wuri gara ya ɗauki mataki don baza su yarda ta dinga fakewa da jinya tana ficewa tana barinsu da yunwa ba alhalin su ranakun girkinsu ba haka suke yi ba, ko kuwa dai baƙin ciki ne don tasan sune masu ƙananun ƴaƴa a gidan. Haka dai tayi ta faɗa tana sakin maganganu marasa daɗi akan Ummar Baqeer ɗin. Ai kuwa ya cika yayi fam don dama mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki don daga Fatimar har ɗan nata haushinsu yake ji, gani yake yi kamar shirinsu ne yasa aka ce mishi Baqeer ɗin ya zama gurgu alhalin ya mance ita ɗin uwa ce babu ta yadda za'a yi taso ɗanta da nakasa ko miye dalili kuwa.

A fusace ya danna kiran number Umman, tana ɗagawa ko amsa sallamar da tayi mishi bai yi ba ya hau cewa "Da kika tafi kika yi zamanki wani kika ajiye da zai yi miki girkin, ko kuwa shikenan don danki baya da lafiya mutanen gida ba zasu ci abinci ba?"
Murya a sanyaye duk kuwa da ranta ya ɓaci da hargagin da yake ta kira yana yi mata tun ɗazu tace "A'a Mallam zan dawo mana sai dai fa har yanzu babu kowa a wurinshi, haka zan taho na barshi shi kaɗai alhalin babu mai kula dashi bayan kuma kasan komai sai anyi mishi tunda ba iya tashi zai yi ba".

"To sai miye idan ba zai iya tashi ba, haka zai dawwama ba zai koyi yiwa kanshi hidima ba kenan tunda gaki uwar son ƴaƴa kin saki hidimar komai da kowa kin kama tashi, wallahi idan magariba ta rufa baki dawo ba Fatima ranki ne zai yi mummunan ɓaci idan kika yi wasa ma sai na hanaki zuwa asibitin gaba ɗaya naga ta tsiya" daga haka ya kashe wayarshi sai faman fitar da huci yake yi. "Zuwa zan yi asibitin nasa a sallameshi, gara yazo ya fara shirin tafiya wajen gasar nan don wallahi bazan yarda daɗaɗɗen burina ya tashi a banza ba, rashin ƙafa ai ba rashin hannu bane bare ace ba zai iya zane ba" yayi maganar cikin ranshi haɗe da yin ƙwafa don sosai yake jin ciwon nakashewar Baqeer ɗin, a ganinshi mai lafiya ma yaya ya ƙare a irin waɗannan wuraren bare kuma gurgu.

Acan asibiti kuwa a sanyaye Umma ta sauke wayar daga kunnenta tana tunanin yadda za'a yi ta tafi ta bar Baqeer a cikin wannan halin bayan babu wani a wurinshi da zai zauna ya kula da shi, Bashir ɗin dake zama yana jinyarshi ita tunda tazo ma bata ganshi ba. Gefen hijabinta tasa ta ɗauke hawayen daya sulmiyo daga cikin idanunta don bata son yin kuka a gaban Baqeer sai dai abun nema yake yi yafi ƙarfinta, ga dukkan alamu ubanshi nema yake yi ya cire hannu daga al'amuranshi babu tausayi ba tausasawa kamar ba ɗan shi mafi soyuwa a wurinshi ba, ashe duk mutanen duniya halinsu ɗaya sai kana da amfanin da zaka yi musu suke yi da kai daga inda ka rasa wannan damar sai su juya maka baya.

Ɗagowa tayi ta kalli Salim dake tare dasu tun ɗazu tace "don Allah kana nan naje gida na dawo, kaga yanayin larurarshi ai ba a barshi shi kaɗai ba"

"To Umma, sai dai kuma da kin haƙura da dawowar tunda magriba ta kawo jiki dare ne zai yi jinyar namiji kuwa sai namiji, In Sha Allah zan kula dashi".

"To kuma ayi haka daga zuwa dubiya sai ka ɓuge da zaman jinya, idan kana da wani uzurin fa kaga ai zaman ya zama takura a wurinka" cikin ranta tana jin babu daɗi don bata so ta takura mishi da abinda bai zame mishi dole ba.

"Babu wata takura Umma, ni da Baqeer ai abu ɗaya ne, nasan ko nine kwance a wurin nan sai inda ƙarfinshi ya ƙare wajen kulawa dani to don me yasa ni bazan yi mishi hakan ba, kiyi tafiyarki Umma In Sha Allah zan kula dashi kamar kina wajen in yaso goben kya dawo".

Wani daɗi ne ya lulluɓeta ganin Allah ya rufa mata asiri ya kawo mai tallafa mata ya tayata jinyar Baqeer abinda tasan ita ba zata iya ba sai dai ƙarfin hali tunda ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba ga kuma girma daya fara cimmata abubuwan da take iya yi a da yanzu nema suke yi sufi ƙarfinta. Tashi tayi ta matsa gaban gadon na Baqeer da ya samu bacci saboda allurai da magungunan da ake bashi masu sakashi yawan bacci ta dafa kanshi tana karanto mishi addu'o'in neman waraka tana tofa mishi, sai da ta gama sannan ta juyo ta kalli Salim tace "Ga amanar ɗan uwanka nan na bari a hannunka Salim don Allah ka kular mini dashi ka kuma yi haƙuri dashi saboda yanayin larurarshi yanzu dole sai ana yi mishi uzuri. Allah yayi muku albarka". Cikin sanyin jiki ta juya ta fice daga ɗakin tana ji kamar idan ta tafi wani abu ne zai samu Baqeer ɗin.
A hankali Baqeer dake kwance ya buɗe idanunshi da suka kaɗa suka yi jaa, wasu zafafan hawaye ne suka taru a cikin idanun a kwance kawai yake yayi kamar mai bacci amma idanunshi biyu dan baya ji ma bacci zai iya ɗaukan shi a halin da yake ciki yanzu, a hankali ya ƙara maida idanunshi ya rufe yana sake duba abubuwan dake faruwa dashi wanda ko a mafarki bai taɓa tunaninsu ba.
Kalaman Salim ne suka katse mishi tunani da yaji yana cewa “Hello Asiya? Kin samu ganin Baqeer ɗin kuwa?”
Shiru yayi dan ya saurari me Asiyan zata ce sai dai bai ji komai ba sai muryar Salim daya sake cewa “Asiya? Hello? Hello?” Sai kuma yace “Hala ba network ne dan bata ji.”
Baqeer ya sake maida ido ya lumshe yana hango idanun Asiya a ɗazu ya tabbatar ta shiga cikin damuwa dan shi kaɗai yasan yadda take kaunarshi, ya ƙannenshi zasu yi in suka ji abinda ya sameshi? Wannan tunanin ne yasa ya dan damtse idanunshi yana addu’a a cikin ranshi.

******
Chapter 9 · 0% Book details