← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 168

Sashe 153

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
*NA*

*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA HUƊU*

{94}
Sosai ya kalleshi yana mamakin abinda ya kawoshi nan sai kuma ya juya ya cigaba da aikin shi cikin ranshi dai cewa yayi "To ina ruwana tunda dai nasan ba wurina yazo ba." Kabir ya daɗe a tsaye a wurin yana tunanin ta yadda zai fara fuskantar Baqeer bayan abinda yayi mishi, haka nan ya ƙarfafi kanshi ya daure ya tura ƙofar shagon ya shiga. Tanimu na ganinshi ya taso ya tare shi da fara'arshi yana welcoming ɗin shi don babu laifi suna da kyakkyawar mu'amala da customers ɗin su. Bayan sun gaisa da Tanimun ne yace mishi wurin Baqeer yazo. Raka shi yayi wajen da Baqeer yake aikin yanka ya ɗauko mishi kujera ya ajiye kafin yaje ya kawo mishi ruwa da drink duk ya ajiye mishi sannan ya tafi ya bar su. "Assalamu alaikum," Kabir yace don duk tsawon lokacin da ya ɗauka a wurin Baqeer bai yi alamar yasan da tsayuwarshi ba. "Ameen Wa'alaikassalm," shima ya amsa mishi ba tare daya ɗago ya bar abinda yake yi ba. Ɗan shiru Kabir yayi yana jinjina ta yadda zai fara faɗin abinda ya kawo shi duk da bai ga fuska a wajen Baqeer ɗin ba sai dai kuma bai ga laifin shi ba don tun dama can su ɗin ba abokai bane ga kuma abinda yazo yayi mishi bayan ya kaɗeshi da mota sannan ya gudu ya bar wurin ko fita bai yi yaga a halin da ya saka shi ba.
Ɗan gyaran murya yayi dai kuma yace "Zuwa nayi na baka hakurin abinda nayi maka duk da dai babu abinda hakan zai canja, don Allah kayi haƙuri ka yafe min, bani da wani excuse akan abinda nayin don haka ma bazan kawo uzuri akan hakan ba. Fatana ka yafe min don Allah ba don ni ba nasan in har ba yafe mini kayi ba bazan taɓa ganin daidai a rayuwata ba." Saurarenshi kawai Baqeer yake yi yana jin ciwon abinda yayi mishi yana dawo mishi kamar a lokacin abun ya faru. Idan yace bai ji ciwon rasa ƙafafunshi da yayi ba kowa ma yasan ƙarya ne to amma idan ya duba yaga alherin da hakan ya janyo mishi a rayuwa sai ya gode Allah don ya tabbatar da hakan bata faru ba Badaru ba zai taɓa barinshi yayi pursuing dream ɗin shi na zama tailor ba, watakila da har yanzu yana can Badaru na juya rayuwarshi yadda yake so bai isa ya yankewa kanshi hukunci ba dile sai abinda yace zai ayi.

Ɗagowa yayi ya kalleshi yace "Kada ka damu abinda ya riga ya wuce babu amfanin dawowa dashi baya, Allah ya yafemu gaba ɗaya." Farin ciki ne ya cika zuciyar Kabir don bai tsammaci samun afuwa daga Baqeer ɗin da wurwuri haka ba, godiya yayi tayi mishi har sai da yace ya isa haka nan sannan ya bari. Ƙara gyara zama yayi na wasu ƴan dukkansu kuma sai suka yi shiru don babu wani sabo a tsakaninsu, sai da ya tashi zai tafi sannan yace "You didn't ask me about her, ko har ka manta da ita?" Ya ƙarashe maganar da sigar tambaya.
Da sauri Baqeer ya ɗago ya kalleshi jin ya taɓo mishi abinda ke ƙunshe cikin ranshi. Ɗan kawar da kai yayi ya basar kamar bai ji abinda Kabir ɗin yace ba. "Bai tsaya sauraren abinda zai ce ba ya sake cewa "Ta dawo fa although bata san zan zo nan, zan ce mata kana gaisheta," ya ƙarashe maganar da tsokana duk da babu wani sabo a tsakanin shi da Baqeer yana so wannan awkwardness ɗin ya rabu dasu. Ɗan murmushi kawai Baqeer yayi sai dai duk da haka bai yi magana ba sai ma ɗaukar scissors da yayi zai cigaba da yankan kayan da Kabir ya tarar dashi yana yi.

Ƙara nutsuwa Kabir yayi yace "Nagode sosai I really appreciate it, baka duba kuskurena ba ka yafe min duk da na aikata maka ba daidai ba, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi." Hannu Baqeer ya miƙa mishi suka yi musabaha sannan yace "Kada ka wani damu ya riga ya wuce kuma ni dama ban taɓa riƙe ka a raina ba." Wayarshi ya miƙa mishi yace idan baza ka damu ba ka bani number ka ma riƙa gaisauwa." Karɓa Baqeer yayi ya saka mishi number sai shi kuma yayi flashing Baqeer yaga tashi number sannan suka yi sallama ya tafi yana ayyana wani abu cikin ranshi.
Haka Kabir ya fita yana jin daɗi don sai yaji kamar an suke mishi wani gungumemen dutse daga kanshi, ashe haka hakki yake duk yabi ya dabaibaye rayuwarka ya hana ka samun cikakkiyar nutsuwa.
Yana fita Baqeer yabi bayanshi da kallo cikin ranshi yana cewa "Ai ko don Zainab dole na yafe maka tunda ka kasance ɗan uwanta." Duk da haka yayi mamakin abinda ya faru daya canjawa Kabir ɗin tunani har ya nemeshi ya nemi yafiya a wurinshi.

*****
Tunda Baqeer yazo ya ɗauke Fatima hankalin Badaru ya tashi, ya kasa gasgata abinda idanunshi suka gani wai Baqeer ne yazo gidan cikin kyakkyawar shiga ga ƙatuwar mota, kenan cigaba yayi da aikin zanen babu shi? Yanzu don rashin imani irin na ɗan yau shine da hannun nashi ya warke bai nemeshi sun cigaba da yin harkar tare ba shine don rashin amana ya tafi yake yin abun shi shi kaɗai ba tare da ya nemeshi ba, ya mance duk tarin alherin da yayi mishi ya fifita shi a cikin ƴaƴanshi amma yanzu da yayi kuɗi uwarshi kaɗai ya sani.
Wannan baƙin cikin ne yasa abu kaɗan zaka yiwa Badaru sai ya hau faɗa yana zage-zage tun ba Abu ba don yake jin haushi gana satar da Kamalu yaje yayi banda Allah ya tufa asiri Baqeer ya hana a tafi dasu watakila da har yanzu suna police station ga kuma na tayashi ɓoye kayan da yake zuwa kasuwa yana sace mishi da tayi shi yasa ko gilmawarta ya gani ya dinga surfa mata zagi kenan, to itama da yake lallaɓawa take yi shi yasa bata biye mishi sun yi rigima ba kamar yadda suka saba yi da. Daga Abun har Jamila abun duniya ya taru yayi musu yawa, sun rasa ta yadda aka yi Baqeer ya zama wani babban mutum haka daga ganin shi anga wanda yake cikin wadata da kwanciyar hankali. Ta yaya za'a ce duk wani alheri da zai samu a cikin gidan sai dai Baqeer ya samu bayan suma sun da ƴaƴan nan, anya kuwa babu wani abu da Fatima tayi don ɗanta yafi nasu ɗaukaka da kuɗi kuwa? Kai gaskiya ma haka ne don in ba hakan ba sai kace shi kaɗai ne ɗa a cikin gidan, su miye sa nasu ƴaƴan basu zama wani abu ba har yanzu sai shi da ko shekara biyu bai yi da barin gidna ba zai dawo yayi irin wannan kuɗin, to ko dai sata yake yi? Wata zuciyar ta Jamila ta kitsa mata hakan sai dai ta kasa yardar wa kanta Baqeee zai yi sata watakila dai wata sana'ar ya kama da kuɗin filin shi da Fatima ta ɗauke ta kai mishi. Har kamar ta tashi taje ɗakin Abu su tattauna don tunda abun nan ya faru basu zauna wuri ɗaya sun yi maganar ba ga kuma tijarar da Mallam yake yi musu kullum tasa kowaccen su ta kama kanta ta tsaya a iya ɗakinta kawai.
Chapter 153 · 0% Book details