← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 168

Sashe 143

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(😞🥺😟)

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar Ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
*NA*

*AYUSHER MUHD*
*DA
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA TAKWAS*

{88}

Tsayawa kawai Daddy yayi yana kallon Zeey ganin yadda take ta dariya kamar wata sabin kamun hauka. Sai da tayi dariyarta ta isheta sannan ta tsagaita, wato Mummy tunda ta gane ita wacece shine zata yiwa Daddy bariki a gabanta ko, ita dariya ma ta bata ganin yadda ta haƙiƙance tana nuna damuwarta a fili. Da ace da ne da idanunta basu buɗe tasan asalin wacece Mummyn ba da tayi mamakin yadda lokaci guda ta juya magana amma yanzu ta gama ganeta sarai sai abun bai wani bata mamaki ba, tasan fiye da hakan ma zata yi in dai Mummy ce. Wani kallo yayi mata yace "Gidan uban wa zaki da kike haɗa kaya?" Turo baki Zeey tayi idanunta ƙyar babu alamun tsoro tace "Wajen uwata zan koma tunda dai ba za'a aura min wanda nake so ba ni banga amfanin zamana anan ba." Hannu Daddy ya ɗaga zai kwaɗa mata mari sai Mummy tayi saurin riƙe hannunshi tace "Haba Senate ya zaka mareta bayan kasan auta yarinya ce har yanzu ba wani sanin daidai tayi ba, don Allah kayi haƙuri abi abun nan a hankali. Ke auta bashi haƙuri kullum ina faɗa miki ki daina yin musu da mahaifinki."

Wani kallo Zeey ta watsa mata kawai ta cigaba da haɗa kayanta, a fusace Daddy yace "Ki tattare kayan nan ki mayar dasu cikin wardrobe don babu inda zaki je, kuma ki sani nasa ranar aurenki da Junaid sati huɗu masu zuwa don bazan yarda ki zubar min da mutunci da ƙimata ba.” Itama ƙara tamke fuska tayi tace "Ai na faɗa maka wallahi bazan aureshi ba sai dai nayi ta zama a haka babu aure in har ba zaka aura min Baqeer ba sai ka shirya ganina a cikin gidanka, ai tun farko na faɗa maka ni bana son Junaid bazan aureshi ba ka dage sai anyi to sai kasan yadda zaka yi dasu don ni dai bazan taɓa auren mijin da bana so ba."
Ƙara yunƙurowa yayi zai kai mata duka Mummy ta sake tare shi ta hanashi kaiwa ga Zeey ɗin. Sosai ranshi ya ɓaci duk da yasan halin Zainab bata iya yin shiru idan anyi mata abu amma bai ɗauka zata tsaya a gabanshi yana faɗa tana faɗa ba. Juyawa yayi zai bar ɗakin don idan ya tsaya zai iya lahanta ta da duka sai ji yayi tace "Kuma na faɗa maka bazan zauna a gidan nan ba don kada ma kuje kuna yawon nemana ah to."
Tsaki kawai yayi ya fice Mummy ma tabi bayanshi suka bar ɗakin. Cigaba tayi da zuba kayan a cikin akwatin, sai da ta tabbatar ta ɗauki duk wani abu da tasan zata rinka buƙata sannan taja akwatinta ta fice. A parlour suka kusa karo da Kabir. Kallonta yayi fuskarshi ɗauke da mamaki yace "Ke kuma ina zaki?" Wani irin kallo ta watsa mishi ta ratsa gefenshi ta wuce don shi kanshi haushin shi take ji, sai take ganin kamar shine sanadin wannan halin da take ciki don watakila da bai nakasta Baqeer ba da duk hakan bata faru ba. Bama zata ga ana wulaƙanta shi ba bare har tausayin shi ya ginu a zuciyarta, da kuma Badaru bai koreshi daga gidanshi ba. Watakila ma da yanzu sun yi aure shi da Asiya. Tana yin wannan tunanin taji wani abu mai nauyi ya sauko ya tokare a ƙirjinta, bugun zuciyarta ya ƙaru fiye da ƙima, numfashi ta dinga yi akai akai har ta samu bugun zuciyarta ya dawo daidai.
Tana fita a harabar gidan taga Junaid ya nufo inda take yana murmushi. Ƙara tamke fuskarta tayi ta cigaba da tafiya zuwa wajen motarta, buɗe motar tayi ta jefa akwatin a baya sannan ta rufe. Daidai lokacin Junaid ya ƙaraso inda take. "Hajiya Zeey kin yi wuyar gani." Wani kallo tayi mishi ta saki tsaki ciki-ciki don bata so yaji saboda tana ganin mutuncin shi kawai dai halin shi na naci ne bata so tunda tace bata yi ba sai ya haƙura ba amma ya dage shi a dole sai ya aureta gashi tana ganin kima da darajarsa. Cigaba yayi da cewa "Kin ji abun farin cikin da yake tunkaromu ko? Su Daddy sun saka ranar aurenmu, In Sha Allah nan da four weeks kin zama mallakina."
Yatsina fuska tayi tace "Idan ma mafarki kake yi gara ka farka don ba tun yau ba na faɗa maka ni bazan aureka ba to yau ma ina ƙara faɗa maka bazan aureka ba, idan har ban samu Muhammad wanda nake so ba sai dai na haƙura da aure don haka tun wuri ma gara kaje ka faɗawa waɗanda ke da alhakin sanya ranar auren nace bana yi su warware." Ta buɗe motarta ta shige ciki ba tare da ko kallon Junaid ta ƙara yi ba.
Kamalu daya faki idon maigadi ya samu ya shigo gidan don ya faɗawa Roshni ɗin shi ya gama haɗa lefe ta faɗi ranar da za'a kawo don so yake yi ayi komai da komai lokaci guda ba sai anyi ta kai komo ana zuwa ana dawowa ba, ganin ta fito ya fito daga bayan motar daya laɓe, yana wani gyara kwalar riga, da sauri ya koma bayan motar ya sake laɓewa ganin saurayi ya nufi Zee ɗin, har ya fara auna cin zarafin da zai mai indai yace yanasan Roshini dan kuwa kowa yasan Roshini ta Saddarth ce, sai dai kalaman Zee sun sa ya zauna dabas a ƙasa. Sakin baki yayi yana kallon Zeey da saurayin da ta gama yagawa, tabɗijam idan har zata iya kallon idanun wannan tsalelen saurayin tace bata son shi to shi kuma a wa da zai yi tsammanin zata so shi. Lallai Roshni ta wuce da saninshi, sai dai duk da haka gara ya gwada sa'arshi don bai san inda za'a dace ba. Wa ya sani ma ko shine Muhammad din? Tunda dai kowa yasan Kamal ma ana cemusu Muhammad Kamal.
Ƙarasawa yayi jikin motar yace "My Roshni!" Wani banzan kallo tayi mishi taja wani irin tsaki don sarai ta gane waye Kamalun ɗan uwan Baqeer ne, shi bai san duk haushin ƴan gidansu take ji ba saboda abinda ubansu ya yiwa Baqeer bare wannan mahaukacin da sam bata sakashi a layin masu hankali. Har zata shiga mota sai kuma ta kalleshi tace “Na ɗauka nace in neman taimako kake a bakin ƙofa zaaka tsaya ko?”
Kallan kanshi yai da irin wankan dayai na gayu ya buɗe baki zai sake magana kawai yaga ta shiga motarta tayi reverse kafin ta danna wani mahaukacin horn, a guje maigadi ya taso ya buɗe mata gate ɗin taja motarta ta fice daga gidan a guje. Kallon wurin data bari Junaid yayi ya juya ya nufi motarshi don bai ga tsaiwar me yake yi ba a wurin kuma sai jin muryar Kamalu yayi yace "Ah to tun wuri gara ka kiyayi Roshni don ba sa'ar yinka bace." Ai juyowa bai yi ya kalleshi ba ya cigaba da tafiyarshi, duk da ranshi a cunkushe yake da maganganun da Zainab ta yaɓa mishi sai da yayi dariya din ya fahimci kamar shima wancan jakin son Zeey ɗin yake yi.
Har sai daya zo kusa dashi a mota ya sake mai wani kallan takaici ya kalli kafafunsa da suka sha wani tsohon takalmi, kai ya girgiza, Kamalu ganin irin kallan daya mai yasa ya harsuko yana kumfar baki yana cewa “Dallah Malan ware ko banza wacce kake so bata sanka ni take so Muhammad Kamal ɗan gata sarkin iya soyayya.” Shidai Junaid wucewa yai kawai ya dinga jin dariya na zuwa mai, duk kuwa da bacin ran da yake ciki.

*****
Tunda ya dawo wani abu bai shiga tsakaninshi da Asiya ba duk da a matse ya diro ƙasar amma annakiyar ƙazantar data haɗa tasa yaji sam baya son kusantar ta, to ita ma bata cikin yanayin daɗin rai tunda yace mata ba zasu koma ba shi yasa bata damu da rashin nemanta da bai yi ba. Yau sai ya tashi da tsananin buƙatuwa, haka nan ya daure ya shiga ɗakin Asiya ya tarar da ita a kwance tayi shame-shame sai shaƙar bacci take yi. Hannu yasa ya toshe hancin shi warin dake busowa daga toilet na hautsina mishi ciki. Kallonta yayi yaga yadda take bacci hankalinta kwance ga alama ita wannan warin daya cika ɗakin baya damunta. Ƙarasawa yayi jikin window ya bubbuɗe don iska ta shigo ko ya samu warin ya fita. Juyawa yayi ya kalli ƙofar banɗakin sai ya ganta a hangame, runtse idonshi yayi ya janyo ƙofar ya rufe banɗakin don baya son ma idanunshi suyi mummunan ganin da zai hana mishi zaman lafiya.

Tsaki yaja yana jin takaicin shigowa ɗakin Asiya da yayi sai dai yanayin daya tsinci kanshi a ciki ne ba zai iya haƙuri dashi ba idan ba ya fitar da abinda ya taru a mararshi ba. Ƙarasawa yayi gaban gadon ya ɗan bubbuga pillown da take kwance akai, shi kanshi pillow case ɗin yayi baƙi ƙirin da dauɗa if he's not mistaken kamar tun wanda aka shimfiɗa ne da aka kawota gidan bata canja ba. Tashi tayi tana mutsitsika ido, ganin Bello tsaye a kanta yasa ta haɗe rai tace "Malan lafiya zaka tashe ni ina bacci?"
Wani irin wari ne ya buso fuskarshi data buɗe baki tayi magana, ai tuni zuciyarshi ta tashi yaji cikinshi na wani irin hautsinawa ɗan abinda yaci yana neman dawo mishi.
Chapter 143 · 0% Book details