Sashe 43
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
******
Zeey yau kwananta biyu kenan bata leƙa Baqeer ba sai dai yadda kasan mara lafiya haka take jinta, ko doguwar magana bata yi, Mumy har ɗaukan ta tayi suka je shopping amma sam taƙi dawowa daidai, suna hanyar komawa gida tace “Mummy don Allah ki barni naje gidan ƙawata akwai abinda zan amsa.”
Kamar zata hanata sai kuma ta fasa tace “Please Zainab in har da wani abun ki sanar dani na tsani ganinki haka.”
Rungumar Mummy tayi tace “Ni kaina ban san meke damuna ba Mummy shi yasa na kasa sanar dake.”
Kanta ta shafa don Daddynsu har ya gaji da tambayarta ko wani abun ke damun Zeey.
“Muje gida sai ki hau motata ki je, tunda har yanzu bai baki motarki ba, kin dai san kulawa ce tasa hakan ko?”
Kai ta girgiza tace “So yake yasan duk inda nake zuwa Mummy kema fa kin sani.”
Wani kallo tayi mata irin na son ta canza abinda ke ranta, Zeey kwantar da kanta tayi a saman kujera tace “Kema fa kin san haka ne.”
Haka suka isa gida sannan ta hau motar Mummy bayan tayi mata kashedi akan kada ta daɗe, ta tsaya ta sayi kayan marmari sannan ta isa ƙofar gidan su Dada, kanta ta maida bayan kujera tana mamakin yadda wai sam ta kasa cire Baqeer daga ranta, rayuwar da suka yi dashi a baya ta tuna hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya bayan ta tuno yadda mahaifinta sam ya hanata kallon gidansu Baqeer, ya zai ji idan yaji ita take bibiyarshi? Yaro ta samu ya shiga da ledojin cikin gida.
Dada na zaune tana tsinke zogale yaron ya shigo ta tambayeshi inji waye yace “Watace a mota a waje.” Da sauri ta miƙe tare da leƙowa nan ta hango Zeey tayi reverse tana neman wucewa, da sauri tace “Ƴar nan ina zaki?”
Karaf a kunnenta hakan yasa tayi parking tana murmushi tace “Dada sai da kika fito?”
Harara ta zabga mata tace “Ina nan ina ta addu’ar na ganki kuma zaki zo naga kin tafi baki shigo ba?”
Fitowa tayi tazo kusa da ita tana dariya tace “Gani nayi ban sanar daku zanzo ba…..”
Ai bata ƙarasa ba taja hannunta ciki tace “Ni kullum in zaki zo daɗi zanji, wannan kayan duk na menene?”
“Ke na kawowa kici kiyi ƙiba da lafiya.”
“Ni ko shi?”
Ido Zeey ta zaro tace “Ke dai, rabani da wannan zancen Dada.”
Dariya suka yi tare da shiga ciki sosai. Baqeer na zaune a ɗakin shi bai rufe ƙofar duka ba, kallon ƙofar yayi jin kamar muryar data kasa barin cikin kunnenshi, muryar da kullum ke yi mishi yawo a zuciya.
Zeey ce ta kalli ƙofar gabanta na wani irin faduwa haka kawai take jin faɗuwar gaban taƙi tafiya, idanunsu ne suka haɗu da juna nan ta ɗan lumshe ido sannan ta sake buɗewa, ta sake saukesu kanshi sannan suka wuce ciki ita da Dada.
Zama tayi har yanzu bata daina ji gabanta na faduwa ba, ta sani tausayin Baqeer ne ke damunta amma faɗuwar gaban ta menene? Shakkar shi da kike yi tun da ko kin manta? Da wannan tunani ta gama tabbatar wa hakan ne.
Baqeer na jiyosu daga ɗaki Dada na cewa “Wai da tafiya zaki yi da ban jawo ki ba?”
Zeey tayi murmushi tace “To Dada mai zan shigo nayi? Wancan karon ma Maryam ce ta aiko ni.” Ta ƙarasa maganar tana ɗan kallon ƙofar ta gefen ido.
Haka kawai yaji kalamanta sun yi mishi zafi, to da yace tazo ne? Dada ce kawai yaji ta ƙwalla mishi kira tace “Baqeer ka fito mana ku gaisa.”
Ko amsawa ma bai yi ba don ji yayi kamar Dada ta gama tozartashi wato har ta gane abinda yake tunani shi yasa take magana da karfi haka?
Miƙewa tayi tazo ta wangale ƙofar tana cewa “Kazo ku gaisa mana.”
Kai ya girgizawa Dada alamar baya son zuwa don baya son ma yin magana balle taji ta ɗauka son ganinta yake yi.
Mikewa Zeey tayi tace “Dada kin dai san ba fitowa zai yi ba ko kin manta ya gama yanke alaƙa da duniya?”
Nan da nan ran Baqeer ya kai bango, me take nufi?
Zeey ta cigaba “Ai Dada kawai ki barshi yayi ta zamanshi a ɗaki tunda har yanzu bai fahimci abinda ya dace yayi ba.”
Dada dariya tasa a gaban Baqeer tace “To ka dai ji namiji da bai san me ya dace ba kuwa ai gani nake akwai matsala ko Muhammadu?”
Fuskarshi ya tamke sosai don shi saboda tsabar baya son raini shi yasa ko wasan tsokana baya yi, Zeey da yake tasan halinshi tace “Dada ya gama azumin ne ko yasha ruwa?”
Dada ta sake kwashewa da dariya wanda hakan ya sake ƙular da Baqeer matuƙa, ya gurguro kekenshi cikin ɓacin rai ya nufi ƙofa, tana jingine a jikin ƙofar tana murmushi, cak ya tsaya yana kallonta itama kallonshi tayi wanda ta sake sakar mishi murmushi tace “Dada bari na wuce kafin na ganni a waje.” Tayi maganar idanuwanta a kanshi, a ina yasan fuskar nan? Tambayar da ta sake zuwa mishi kenan, baya son ta gane kallonta yake sosai hakan yasa ya ɗan kauda kai, zai rufe ƙofar Dada ta riƙe ƙofar tace “A’a ni kar a rufe dani a barni naje mu sha hira da ƙawata, tunda kai dai ka kulle kanka sai kasha zamanka lafiya.”
Wani murmushi tayi mishi wanda ya kasa gane wani iri ne tana kallonshi shima yana kallonta tace “Toh Dada in ma mutum zai farka ya nemi abin da zai debe mishi kewa ya farka in ba haka ba yana zaune mutanen da ya daɗe yana kula dasu zasu ƙarasa rayuwarsu cikin baƙin ciki.”
Tana kaiwa nan ta koma inda Dada ta saka musu tabarma ta zauna, Baqeer wani irin yanayi ya tsinci kanshi dashi wanda yaji yama kasa rufe ƙofar, Dada ce ta fito don tabbas tasan kalaman Zeey sun shigeshi dole ta roƙi Zeey ta dinga zuwa don ta tabbatar Baqeer na neman mai fada mishi gaskiya gwara ya san abun yi.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
#Baqeer
#Zeey
#Kamalu
#Sanyin Zuciya
#Rayuwata
*Umm Asghar Ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*🏌🏻♀️
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA*
{26}