Sashe 141
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gidan Suleiman kuwa Ummi ta kasance mace mai mai haƙuri da sanin ya kamata. Ƴaƴa biyu ta haifa daga Kabir sai Zainab wanda tsiran shekaru biyar ne a tsakaninsu. Zainab nada shekara huɗu wasu mutane suka tare a gidan dake jikin nasu. Mace ce da ƴaƴanta biyu budurwa sai ƴar ƙaramar da bata fi sa'ar Zainab ba. Kasancewar Ummi mace mai faram-faram da jama'a da saurin sabo yasa nan da nan suka saba da maƙwabtan nata tun ma ba budurwar ba mai suna Halima. Kullum zaka sameta a gidan tana taya Ummi ƴan aikace-aikace.!Da kaɗan da kaɗan sai Ummi ta sakar mata hidimar gidan ta gaba ɗaya komai su Zainab da Kabir suke so sai tace su tafi wurin Halima, ya zamanto dai ita bata tsinana komai a cikin gidanta sai dai Halima tayi. Tun Suleiman bai lura ba har yazo ya fahimci ai Hafsatu ta sakarwa Halima duk wasu hidindimu na gidanshi, ga wani irin kauna da Haliman ke wa yaran, abinda zai baka mamaki har takai ta kawo indai yaran na san abu to fa gun Halima zasuje ba gun Ummi ba, wanda ita ko damunta bayayi gani take saukin ta ne. Alhaji Sulaiman wannan abu na bala’in birgeshi dan yana san Kabir yai karatu sai gashi zaiga Halima tasa Kabir a gaba akan yai karatu, kusan duk sanda zai shigo gidan zai ganta tana karatu da Kabir, gashi yana san Zainab wanda ya kula Halima ma tafi Ummi kula mishi da Zainab. Wane tudu wane gangare sai ga Halima da Suleiman sun fara soyayya, cikin ƙanƙanin lokaci aka yi aurensu dan a lokacin ya gama yadda Halima ce wacce yake bukata, balle in suna hira tana karfafa mai gwiwa akan siyasar sa da yanda take ganin tabbas har matsayin Governor zai iya kaiwa tana ji a jikinta, duk Ummi bata sani ba saboda sun yi abun ne a ƙudundune basu bari kowa ya sani ba sai dai batun ɗaurin aure kawai mutane suka ji daga sama.
Mai unguwa ne ya bada auren Halima don basu da kowa a garin a cewar Inna mahaifiyarta mahaifin su Halima ya rasu ƴan uwanshi suka danne gadonsu suka koreta shine ta tattaro ɗan abinda ya saura musu ta taho nan ta kama hayar gida tana sana'ar sayar da abinci a bakin kasuwa, amma a zahirin gaskiya cikin shege Halima tayi bayan har an saka mata ranar aure da wani ɗan aminin mahaifinta tace ita bata son shi, shi kuma mahaifinta yace ba zai bawa wanda ta kawo ba don bai yarda da tarbiyyarshi ba shine Halima ta tafi ɗakinshi don su gudu to basu gudun ba dai sai tsarabar ciki data koma gida dashi. Ciki na bayyana a jikinta mahaifinta yace sai ta fita ta bar mishi gida ita kuma Inna tace sai dai ya haɗa ya koresu gaba ɗaya don babu inda tilon ƴarta zata tafi ta barta, wannan ne sanadin baro ƙasarsu wato Niger suka shigo Nigeria bayan Halima ta haihu Inna ta ɗauki ƴar ta riƙe a matsayin ita ta haifeta suke kuma faɗin wancan labarin na ƙarya da suka ƙirƙira don su ɓoye sirrin daya rabosu da ƙasar su.
A lokacin da Hafsatu ta samu labarin auren cin amanar da Suleiman da Halima suka yi sosai ta ɗaga hankalinta, tashin hankali aka yi sosai a inda har Suleiman yace ta fice ta bar mishi gidanshi ya saketa don a lokacin gani yake yi baya da buƙatarta tunda komai na hidimar gidan dama Halima ce ke yi. Koda ta tashi tafiya ta haɗa kan ƴaƴanta zata tafi dasu sai Suleiman ya ƙwace su ya bawa Halima, tana kuka tana roƙon shi akan ya bar mata ko Zainab ce ita da take mace idan yaso shi ya riƙe Kabir amma ya ƙeƙasa ƙasa yaƙi a ƙarshe ma sai yayi mata korar kare yace idan ya bar mata yaran da ba iya kulawa take yi dasu ba. Abinda ya baƙanta ranta kenan tayi fushi ta tafi sai dai tasan komai daren daɗewa ƴaƴanta zasu nemeta.
Suleiman ya ɗebi yara ya bawa Halima ita kuma tasa hannu bibbiyu ta riƙe su kamar nata sai dai a haka ne ake ganin soyyayar da take yi musu anma a zahirin gaskiya yaran ba wani damuwa tayi da yaran ba kawai dai tasan idan bata yi musu riƙon kirki ba to ba lallai ta samu ubansu yadda take so ba shi yas take nuna musu soyayya take nuna musu kamar nan duniya babu mai son su kamar yadda take yi.
Alhaji Sulaiman Karaye da Alhaji Badaru suna da ƙullalliya wanda kaf unguwar an san ƴar tsamar dake tsakaninsu, duk da ba faɗa suke yi ba sai dai basa jituwa, wanda a baya a lokacin ƙuruciyarsu an shaida abokan juna ne su biyu suka san me ya haɗa su sai ɗaiɗaikun mutanen unguwa da suka san abinda ya faru a wancan lokacin don su dai matansu haka nan suka taso suka ga basa shiri sai ƴar tsama, Zainab makarantar islamiyarsu ɗaya da Maryam wanda haka kawai jininsu ya haɗu, tana ƙarama yar duma-duma ce, duk lokacin islamiya shi kuma Baqeer a lokacin ya takurawa Zee duk sanda ya ganta sai yace “Abulele! Injin taliya” ba abinda ta tsana irin ya dinga tsokanarta da sunaye barkatai, ko wasa ake yi da yake shi dama Badaru baya barinshi yayi wasa yana daga zaune yana zane zaka ji yace “Karfa kusa Abuwa don kuna sakata zata lalata muku wasa.” Duk sanda ya faɗi haka ita kuma zata sa kuka ta kai ƙararshi wurin Umma, haka Umma zata yita yi mishi faɗa akan ya daina takurawa Zainab.
Shi Kabir a lokacin sa’an Baqeer ne sai dai sam basa shiri don Badaru makarantar da aka sa Kabir nan ya kai Baqeer aka sakasu aji ɗaya, babban farin cikin Badaru shine yaga Baqeer yaci na ɗaya yayi ta yadawa Sulaiman habaici shi kuma hakan ke sa ya sake takura Kabir akan karatu, a lokacin Mummy ce matar Daddy don sun rabu da Ummy a lokacin shekarun su Kabir sha biyu ita kuma Zee shakarunsu bakwai ita da Maryam, Hadiza kuma shekararta tara.
Haka kawai Allah ya haɗa kan Zee da Maryam bini bini tana gidan, duk kukan da Baqeer ke sakata bata fushi da zuwa gidan. In har aka hanata ma fita sai ta saci hanya tazo, Alhaji Sulaiman yayi faɗa har ya gaji, Mummy tana nuna mishi ai ba komai in tayi hankali sosai zata daina.
Wani sa’in ko gidan zata shigo sai ta leƙa ta leƙo ta tabbatar Baqeer baya nan kafin ta shiga, sai dai tana shiga zata jishi ta ɗakin shi yana yi mata waka ‘Abuwale Abulele yar dumi-dumi ƴar duma-duma, ina zaki babu hanya.’ Takaici in ya kamata wani sa’in ta ɗebi ruwa a kofi ta watsa mishi ta window, haka Umma zata zo tayi rabiya, ita kuwa Abu mahaifiyar Kamalu daga taga ya fara zata ce eh dama dani kake shine kake wayancewa. Sai dai duk da haka baya dainawa, shi dai yana son ya takurawa Zee, Umma tayi fada har ta gaji, ita kam Zee tasha kuka don kusan duk sanda tazo sai ya sakata kuka hankalinshi ke kwanciya. Gashi abun na bashi dariya daga ya tsokaneta sai kuka, wani sa’in tana tafiya sai yazo bayanta kawai ya firgitata haka zata ruga a guje taje gida tana kuka, Mummy ta bata haƙuri tace ta daina zuwa, sai dai gobe da sun nemeta suka rasa sun san inda take.
Ranar da abun ya faru ranar walimar su Baqeer ne na saukar Alqur’ani a islamiya shida Kabir, bayan an raba kyaututtuka anyi karatu sai Baqeer ya fito saboda yada maganganu da Badaru ke yi a wurin, wai a dole asan Baqeer ɗanshi ne, shi kuma sam baya son abinda Badarun yake yi, yana tafe yaji alamun ana binshi a baya, waigowa yayi yaga Zainab alokacin yake ce mata Abu dumi me kike yi anan?
Kallonshi tayi tace “Nifa Allah ka daina ce mini Abu dumi ai dai Allah ne yayi ni haka.”
Dariya Baqeer yayi yace “Inyee yarinya kin girma.” Ta murguɗa mishi baki tana cewa “Oho dai, kuma ni ba binka nake yi ba abu zan siyo.”
“Me zaki siyo bayan ga shago can a can?” Ta ɗan waiga tace “Ya Kabir zan saiwa kyauta kaga kudina,” ta nuna mishi ɗari biyu sannan ta cigaba “To shi kwallo yake so kuma Daddy ya hanashi shine zan je na siyo mishi.”
Kallonta Baqeer yayi yace “Dumi kinsan inda ake saidawan ne?”
Ta taɓe baki tace “Oho koma dai ina ne zan duba.”
Tunani yayi ko dai ya tsokane ta ne? Da yake ba abokai gareshi ba yana jin daɗin tsokanar ta. Kwafa yayi a ransa yace “Dumi muje na kaiki?”
Da mamaki ta kalleshi tace “Kai din?" Yayi dariya yece “Kina wasa ne?” Haka suka dinga tafiya inta tambaya anzo Baqeer yace ba’a zo ba, shi kanshi tun yana gane hanyar har yazo baya ganewa, gashi lokacin gidaje basu yawaita ba, in ka fiya tafiya sai daji, Zee tunda taga an zo inda babu gidaje hakalinta ya tashi nan da nan ta maƙalƙale ta bayanshi, matsar da ita yayi shi kanshi ya fara jin tsoro.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce*
Da
*Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA BAKWAI*
{87}