← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 168

Sashe 164

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

Ayusher Ce
Da
Umm Asghar

*BAQEER*
*NA*

*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊARI DA ƊAYA*

{101}

Tun Mummy tana gwada ƙiran wayar Sultan tana ringing har ma ta daina ringing ɗin gaba ɗaya. Hankalin Mummy fa ya tashi ta rasa inda zata sa kanta taji daɗi, tsoron ta ɗaya kada dai ace yaron nan cutarta yayi ya karɓe mata kuɗaɗenta da dabara. Cikin kwana biyu gaba ɗaya ta futa daga hayyacinta don ko abinci bata iya sawa cikinta, a ranar da aka cika kwana biyu ne aka yi evicting ɗinta daga hotel room ɗin data kama saboda kuɗin data biya sun ƙare kuma bata da alamar cigaba da biya.
Haka nan ba don taso ba ta tattare ya nata ya nata ta bar gidan ta koma gidan Inna. Inna na ganinta tace "ke kuma daga ina?" Kawai ta fashewa Inna da kuka cewa take yi "Na shiga uku Inna, don Allah ku nemo Sultan yazo ya bani kuɗaɗena wallahi na fasa yin kasuwancin." Ita dai Inna sai kallonta take yi har tayi ya isheta sannan Inna tace "idan na fahimce ki daidai wani kika damƙawa dukiyar ya gudu da ita," kasa amsawa Inna tayi don haka Inna ta cigaba da cewa "ai daidai kenan Halima, dama wanda yaƙi ji ai baya ƙi gani ba, nan babu yadda ban yi dake akan ki koma gidanki ki kula da mijinki da larura ta sameshi ba kika toshe kunnuwanki kika ƙi ji sai yanzu da kika haɗu da mutanen duniya suka yi miki hankali ne zaki zo ki sakani a gaba kina kuka. Ai baki ga komai ba tunda kika ce ke butulu ce mai manta alheri. Duk irin yadda mutumin nan ya riƙemu amana ya ɗauke dukkan wasu nauyin mu baki duba ba kika rasa lokacin da zaki butulce mishi sai da ƙaddarar rayuwa ta afka mishi, wato yanzu ya gama yi miki amfani to bari ki ƙara gaba ki barshi."
Ita dai Mummy sai kuka take yi tana jin baƙin cikin damfararta da Sultan yayi, yanzu shikenan duk abinda take taƙama dashi take ganin ita ma yanzu ta kai wani matakin rayuwa data daɗe tana yiwa kanta fatan kaiwa ya rushe lokaci vuda kamar ba'a yi ba.
Kallon tausayi Inna take yi mata har sai data tsagaita da kukan sannan Inna tace "Sawunki a likkafa ki tashi ki koma gidanki ki nemi yafiyar mijinki don baki da wani rufin asiri face ɗakin ki, da Allah yasa ma ba sakin ki yayi ba ke kika ga dama kika baro gidan don wallahi baza ki zauna min anan ba ke ba bazawara ba ke ba sakakkiya ba nayi ta faman ɗawainiyarki alhali kina da gidan mijinki." Share hawayenta tayi tace "yanzu Inna sai na koma bayan duk abinda nayi mishi?"

Kallon tsaf Inna tayi mata sai daga duk ta rame ta lalace kamar ba ita, cike da tausayawa halin da ta jefa kanta a ciki Inna tace "Komawa kuwa ta zame miki dole kije ki nemi gafarar maigidanki don dai kin san baki kyauta mishi ba bayan duk alherin da yayi miki a rayuwa, baki da wani gata face ɗakin ki Halima haka zaki yi haƙuri ki tashi ki koma. Maza shiga ciki kiyi wanka ki gyara jikinki sai kizo ko tafi kin ji, Allah yayi miki albarka." Cikin zuciyarta ta amsa Ameen ɗin ta tashi ta shiga ɗakin Inna don tayi wanka kamar yadda ta umurceta.

Babu kunya haka Mummy ta koma gidan tasa makulli ta buɗe ɗakinta ta shige, babu wanda yace mata ci kanki sai ma hidimarsu da suke yi, to itama kunyar abinda ta aikata yasa ta kasa sakewa a cikin gidan kullum tana ƙunshe a cikin ɗaki bata iya fitowa, gaba ɗaya a ɗarare take da mutanen gidan duk da ma babu wanda yake shiga sabgarta a cikin su.

*****
Badaru da ƴan uwanshi sun je wajen Alhaji Suleiman Ƙaraye nemawa Baqeer auren Zainab, sosai Alhaji Suleiman da nashi ƴan uwan da suka zo daga Ƙaraye suka yi musu tarba da mutunci da girmamawa, abinda ya ƙara sanyayar da jikin Badaru. Cikin mutunci da mutuntawa duka gabatar da abinda ya kawo su, babu wani ja'in'ja ko ɓata lokaci aka tsayar da magana guda ɗaya har an yanke ranar auren watanni biyu masu zuwa nan gaba. Haka suka rabu ana raha ana wasa da dariya. Bayan sun fita Badaru ya ɗan dawo ya kalli Alhaji Sulaiman yace "Ya jikin naka?" Murmushi yai ya sake mika mai hannu yace "Allah ne ya haɗa mana yaran nan dan mu sassauta wa kan mu a lahira saboda wannan gabar batada amfani." Badaru ya jinjina kai nan ya bashi hakuri shima Alhaji Sulaiman ya bashi hakuri sannan ya fito.
Sosai Baqeer yayi farin ciki da jin an bashi Zeey don ma ranar da aka saka ɗin tayi mishi tsawo a cewarshi shi bai ƙi ace daga zuwa neman auren an ɗaura ba. Itama Zeey ta samu kanta cikin farin ciki don abu ne da har ta cire rai da faruwarshi sai dai da yake komai yin Allah ne sai gashi cikin sauƙi iyayen nasu sun aminta da maganar gashi har an saka rana.
Kowanne ɓangare shirin biki kawai suke yi, ga Baqeer dai gyare-gyare yake yiwa gidanshi duk da sabo ne ya siya amma akwai wuraren da yake so a canja musu fasali sai kuka painti da za'a yiwa duka gidan har part ɗin su Umma. Da kanshi ya haɗa lefenshi don a yanzu za'a iya cewa yafi su Maryam sanin manyan kaya saboda harkar ɗinki da yake yi, babu irin zanin da baya gani, ya dai ɗaukesu sun rakashi amma komai da kanshi ya zaɓa ai kuwa kaya yayi mata masu kyau da tsada sosai, bai dai yi kaya irin na ƙarya ba sai dai komai mai kyau ne da inganci. Akwatina ne set biyu kowanne mai uku da kit sai suttura guda talatin da biyar amma fa duka manya sai dangin su dogayen riguna, abaya, ƙananun kaya da sauransu.
Duk wanda yaga kayan sai da ya yaba don kaya ne aka yi su babu ƙaranta babu kuma fariya a ciki. Ita kanta Umma data ga irin kayan da Baqeer yayi sai data yaba sosai ta kuma ƙara godewa Allah daya ɗaukaka ɗanta gashi yanzu kullum ƙara samun cigaba yake yi. Ba wasu mutane da yawa ne masu kai kayan ba don Baqeer yace baya son gayyar mutanen nan don haka aka tsara a gidansu daga Abu sai Jamila ne masu zuwa sai Hadiza a cikin ƴan uwanshi sai kuma daga cikin ƴan uwan Badaru mutum biyu sai matar wan Umma, su kenan mutum shida.

A ɓangarensu Zeey ma sai shiri suke yi, kuɗaɗe masu yawa Daddy ya tura mata a account ɗinta yace suje da Ummi su sayi duk wasu sayayyar kayan kitchen don furniture wani interior decorations company ya bawa kwangilar zuwa su shirya mata gidan. Babu abinda ake saka Mummy a ciki, to ina ma suka ganta tunda ta mayar da ɗaki wajen zamanta. Ranar da za'a kawo lefen ma haka ƴan uwan Ummi dana Daddy suka cika gidan sai hidima ake yi, anan nema wata ƙanwar Ummi tayi magana akan bata ga Mummy ba shine aka ce mata tana ɗaki. Tashi tayi ta tafi ɗakin Mummyn, daga bakin ƙofa ta tsaya tayi knocking. Tasowa Mummy tayi ta buɗe jikinta a sanyaye don tunda taji hayaniya ta cika gidan ta sakawa ƙofarta key don tsoron haɗuwa take yi da ƴan uwan Ummi saboda wulaƙancin da tayi ta musu a yanzu kuwa da suka dawo cikin rayuwar su Zeey bata san abinda zasu yi mata ba shi yasa ta dannawa ƙofarta key.
Murmushi Aunty Badi ta sakar mata don ta lura da yadda take a ɗarare, kaucewa tayi ta bata hanya ta shiga cikin ɗakin. Zama tayi akan resting chair ita kuma Mummy ta zauna a bakin gadon. Gaisheta Aunty Badi tayi sai kuka tace "mun zo tun ɗazu naga ban ganki ba shine nake tambayar ina kike aka ce kina ɗaki, sai dai kuma hakan bai dace ba a matsayinki na uwa a wajen Zainab ace ana hidimarta sai dai wasu daga waje ne zasu tsaya akai ke da kike cikin gidan kamar ba kya nan shi yasa na shigo nace kome Zainab tayi maki kiyi haƙuri zaki yi yaran ne ka haifesu baka haifi halinsu ba don haka kiyi haƙuri ki fita a tari baƙin nan dake idan yaso ko meye ma daga baya sai kuyi wannan siririn ku ne na cikin gida bai kamata wasu daga waje su sani ba".

Godiya tayi mata saboda taji daɗin yadda ta mutunta ta duk da abubuwan da tayi musu a baya, tashi tayi ta shirya cikin wani rantsatsen lace ta fita suka gaisa da mutanen da suka zo sai dai duk da haka ta kasa sakin jikinta sai take ganin kamar kowa na wurin yasan abinda tayi. Har ƴan kawo kaya suka zo suka tafi da sha tara ta arziƙin da aka haɗa musu Mummy na cikin su don duk wani abu da za'a nema ita Aunty Badi take tambaya don haka tun tana ɗari-ɗari dasu har dai ta saki jikinta aka yi komai cikin mutunci, a lokacin ne kuma ta ƙuduri niyyar samun Daddy ta bashi haƙurin abinda tayi mishi don tun dawowarta bata yarda ya ganta ba, kunyar haɗa ido dashi take yi. Da yan uwan Ummi zasu tafi da kanta taje ta basu hakuri akan kuskuren raba su Zainab datai da sharrin data dinga musu tayi haka ne saboda tana tsoron kar yaran su barta, haka tai ta basu hakuri ganin sun saki jiki sun nuna mata ba komai yasa ta ƙara samun nustsuwa.
Chapter 164 · 0% Book details