← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 168

Sashe 70

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A duk sanda Habi taga Asiya na wannan zumudin kasa ɓoye mamakinta take, yanzu ma tana kwance bayan sallar asuba take juyo kunkunin Asiya, farkawa tai ta ɗan juyo tana cewa "Yau kuma menene da sassafan nan ke da bakya rabo da neman magana?"
Asiya tsaki tai tace "Ni dasu Inna ne wallahi badai ni za'awa kayan ɗakin dubu dari biyar ba kamar wacce wace ba tada gata? Ai ko miliyan biyar ni yamin kaɗan a jeran gidana."
Sake baki Habi tai tana kallanta tace "Miliyan biyar? Asiya kanki kalau dai ko?"
Wani mugun kallo ta mata tace "Banasan iskanci ke in bikinki yazo kice kin yafe kayan ɗaki ku zauna a tabarma, aikin kawai tun yaushe ma aka daina kayan ɗakin 700k? Na tabbatar ko mutanen kauye yanzu suma sun waye."
Daga waje Habi ta juyo Inna tana ƙoƙarin haɗa murhu, ta mike tana gyara inda ta kwanta tana cewa "Su masu miliyan biyar ɗin rainan gas ne ke kuwa rainan itace ce ko gawayi sai ai sati ba'ai amfani dashi ba a gidan da kika taso.”
Ai da sauri ta mike tana neman jawo Habi, ganin haka yasa ta ruga waje da gudu tana ma Asiya gwalo wanda ba karamin ɓata mata rai yai ba.
Kwafa tai tace "Zaki dawo wlh."
Habi kuwa tana fita tai tsaki tace "Auren cin amana akewa zumudi haka, mutum sai karya kamar ɗan wani? Kawayenta har yau ba wanda ta taɓa bari yazo gidansu amma dan san a sani harta bisu ta sanar dasu zatai tafiya."
Muryar Inna ce ta katseta "Habi shine ke baki ɗan kwanta ba zaki fito da safen nan?"
"Ke kika fito bare ni Inna?" Ta faɗa tana ƙarasa was tare da ɗaukan abin tatar koko.

****
Zeey a ƙofar gidan Umma tai parking, kallan kanta tai a madubi wai yau itace take bin namiji? Itadai sam tasan wannan rayuwar ba tata bace, gabanta ne ya ɗan faɗi kadan ya Baqeer zaiyi in yasan itace Zainab? Wani yanayi ne ya bayyana a fuskarta ta daure ta buɗe ƙofar mota ta fito.
Jamila na waje ta shimfida tabarma tana yanke farcen kafarta, yau sau ƴan harare-harare sukeyi uta da Abu dake busar da aya zatai sana'ar data saba.
Zainab ce ta shigo ko kallan inda suke batayi ba ta fara neman wucewa bangaren Umma.
Abu a kufule tace "Ke cokal? Kin wani cokalo takalmi mai tsini kinzo mana gida kina neman shigewa ciki? Hala dangin mijin Maryam ce? Dan nasan kaf zuri'arsu Fatima ba wanda zai sa atamfar jikinki."
Duk yanda sukeji da faɗa ita da Jamila sai ji mukai Jamila tasa dariya tace "Yoo wannan ma dangin nata da su ai da babu duk daya, uwar ma bakiga ba ganinta zuke zuwa yi ba."
Zainab ce ta waigo tana murmushi tace "Dama aiko ni akai naga yawanku dan shugaban mu yace zai fitar da zakka amma da akama mace ɗaya ce a gidan."
Jamila ce tai zuruf tace "Shareta ƴar nan wannan fa dama haka take duk wani kursusun gulma daga gunta yake fitowa nace wanene shugaban?"
Abu ce tai tsaki tace "Andaiji jiki wlh mutum ya nemi sana'a yaki sai yaji za'a raba ɗari biyar ya hau bin layi."
Zeey kam ganin suna masufarsu yasa ta shiga ciki ta barsu, Umma na ɗaki tun safe take jin kanta babu daɗi ga wayarta ta kunnu amma tana tsoron ƙiran Baqeer kar ya gane halin da take ciki daga muryarta.
Sallamar Zainab ce yasa ta miƙe tana amsawa, ganin Zainab yasa fara'arta ta ƙara faɗa da tace "Zainab kece?"
Zama tai ta gaisheta sannan tace "Daga ina haka?"
"Dama nakaiwa Dada sako ne Ya Baqeer ya aikoni gunki."
"Baqeer? Ya yake? Ya jikin naashi? Ya yake rayuwa?"
Umma tai tambayar a jere idanunta na cikowa da kwalla, murmushi Zeey tai tace "Umma yanzu komai ya daidaita?" Kai ta jinjina tana murmushin yake tace "Indai har su yaran suna zaune lafiya ni ko ma menene bakomai." Tausayin Umma ya kamata dole ta taimaki Baqeer ko dan ya ƙara tsayawa da kafarsa, hannu tasa cikin jakarta ta ciru kuɗin ta ajiye gabanta, Umma da mamaki ta zaro ido kafin ta tamke fuska tace "Kindai san bazan karbi kuɗin iyayenki ba, ban rikeki ba abaya ban kuma......"
Da sauri Zeey ta katseta tace "Inji Ya Baqeer sakon ne."
Mamaki ne ya hana Umma magana tace "Baqeer?" Kai ta ɗaga zatai magana wayar Nabeela ta shigo kamar bazata ɗauka ba saboda tunanin kar a gane inda take sai kuma ta daure ta ɗaga.
Nabeela tanaji ta ɗaga tace "Zeey kina ina? Dady ya kusa isowa, yana Kano."
Da sauri ta mike tace "Okay, nagode Aunty Nabs."
Kashewa tai sannan ta kalli Umma ta mata bayanin yanda Baqeer yace a kasafta kudin sannan tace "Zan wuce Umma ana nemana."
Harta fita Umma na riƙe da kuɗi mamaki ya gama rufeta, ina Baqeer ya samu kuɗi? Kuɗin ma har haka?
Wayarta ta ɗauko tadan bubuga bayan sannan ta tashi, ƙiran Baqeer tai ta ɗau kudin ta shiga dashi ɗaki ta zauna a bakin gado, karin mamakinta ma ya akai Baqeer yaba Zee sako?

Zeey cikin sauri ta fito tana ji su Jamila na gulmarta itada Abu itakam ko ta kansu batai ba tai waje, dan tasan in Dady ya san yawo take tabbas hanata fita ma zai gaba ɗaya ita kuwa yanzu aka hanata ganin Baqeer to fa an mata giɓi sannan batajin zuciyarta zata iya dauka.
Kamalu ne ya sauka akan babur da mamaki yaga wata kamar Roshni ta shiga mota, cikin sauri ya ke tahowa yana hadawa da ɗan gudu-gudu, sai dai kafin ya iso taja motarta ta tafi, motar da take hawa ne sai dai bayaji Roshni zatazo gidansu, gida ya shiga ya nufi gun Abu wacce ganinshi yasa tace "Kamalu? Hala yunwa ta koroka?"
"Roshini ce ta shigo gidan nan?"
Da mamaki tace "Rasheeda? Au wai sunanta kenan? Yo ai ni ban sani ba."
Da takaici cikin dan ɗaga murya yace "Wace wata Rashida? In ma Rabi ce ni bai damenba."
A fusave Jamila tace "Karka sake kiran sunan mahaifiyata in zakai zagi ko magana ku kare can tsakaninku.
Tsaki yai yana kumboro baki kawai ya fita daga gidan, ya banko ƙofar gida kai kace ɓalata zaiyi.
Da gudu ta shiga ciki, saura kiris ta buge Kabir da ya nufi hanyar waje, tace "Oops! Sry."
Kai ya girgiza ya bita da harara sam yarinyarnan ta rainashi wato ko dawowa ma ya bata hakuri baiyi ba? Duk an bari ta rainashi saboda bin bayanta da kowa yakeyi. Muryar Nabeela ce ta katse shi tana cewa "Are you alright?"
Kallanta yai ta sakar mai murmushi, kai ya girgiza kawai ya fita dole ma yaje gun abokansa suje club, waya ya ɗauko bayan ya shiga mota ya ƙira Mumy. Ta dauka tana cewa "Abu kake so?"
"No Mumy please fita nakesan yi zanje gun wani friend dina ne in Dady ya dawo kice ina bacci, ba dadewa zan ba.” Kafin tai magana ya kashe wayar ya shiga motar ya bar gidan.
A ɗaki ta ajiye jakarta sannan ta cire mayafi ta fito gun Mumy inda take shiryawa Dady abinci.

*****
Baqeer ne ya ɗaga ƙiran Umma, bayan sun gaisa tace “Baqeer meke faruwa? Ka barni riƙe da kuɗi ina kokonto.”
“Umma badai so kike kice baki yarda da ɗan ki ba wanda kika haifa kika kuma raina, kindai san bazan yi abin banza ba.”
Ajiyar zuciya tai tace “Bawai abin banza ba kawai tsoro abin yaban.”
Jiki a sanyaye yace “Umma insha Allahu Allah bazai wulakanta mu ba, Allah zainzama gatan mu, kedai ki cigaba da mana addu’a.”
A hankali tace “Allah ya dafa mana Baqeer sai dai nayi mamaki sannan yaushe kuka……” sai kuma tai shiru a matsayinya na mahaifiya da dama batasan wannan gabar tun shekarun baya me zai sa ta tambayeshi har ta kara taso da abin? Haka sukai sallama yana Dada wayar.
Dada fitowa tai waje dan ta bata labari ta kuma san yanzu Baqeer zai kwafsawa hirarsu.
Umma ce ta katseta da cewa “Dada nikam Baqeee yasan Zainab ne?”
Dariya tasa tace “Sani kai ai duk wannan abin da taimakonta ya tabbata.”
Mamaki ya kama Umma sai dai Alhamdulila da Baqeer ya cire wannan mumunan abin a ransa ya saki jiki suke gaisawa da Zainab, sai dai kasan zuciyarta na tsoro kar abinda ya faru baya irinshi ko shigenshi ya ƙara faruwa.
Kai ta girgiza sannan tace “Dada dan Allah kar wanda yasan sana’ar da Baqeer yakeyi yanzu, mu barshi a matsayin sirri ina tsoro kar tsautsayi yasa mahaifinshi yaji labari.
Kai Dada ta jinjina alamar hakan yayi nan suka ɗan yi hira kaɗan da Dada sukai sallama.

Ba shiri Umma ta fito tai alwala ta koma ɗaki tai sallah tanawa Allah godiya akan abinda ya faru lalai babu shakka Allah shine maj bayarwa kuma shine mai hanawa.
Chapter 70 · 0% Book details