Sashe 146
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
****
Baqeer kuwa ya tattara komai ya sashi a gefe, duk da Zainab na cikin ranshi amma ya danne bai bari a gane, shagonsu sun kammala gyarashi da sanya kayan aiki, yin aiki da mutanen nan ba ƙaramin alheri yake samu ba, hakan yasa yace ko ya buɗe shagonshi zasu cigaba da aiki tare, wani idea ne yazo mishi na yanda yake fitar da ɗinkin maza, style ne wanda ba'a taɓa ganin irinshi ba, sai suka yi meeting akan yanda zasu ƙayata ɗinkin ya karɓu a wurin mutane, Salim ya bada shawara akan su haɗa shi kamar gift su dinga sayawa kayan huluna da takalmi suna ɗaurawa a social media, designs ɗin jikin hulunan su suke bayarwa ayi musu sai suyi wa kayan aiki irin shi, keken da zai yi aikin sun yi sa'a ba irin wanda zai taka bane, yana daga zaune zai yi dan shi kaɗai yasan yanda yake son style ɗin ya kasance, kuɗin siyan injin aikin suka maida hankali wurin haɗawa don kuwa yana da tsada sosai, gashi baya so su je wani wurin suyi aikin wani yaga idea ɗin ya sace, dole su zasu fara in suka fara tallanshi wasu suka kwafa a kalla kowa yasan sune dai asalin masu abun.
****
Yau Bello tun cikin baccinshi yake ji ana buga ƙofa, miƙewa yayi don sam basa kwana ɗaki ɗaya da Asiya, ganin ƙazantar ta na neman illa tashi yasa ya nemo mai aiki take zuwa safe da yamma tana gyara gidan ta tafi, Asiya sam bata damu ba sai ma wani halin banza data tsuro mishi in taga an gyara gidan sai ta ɗauki abu ta saida ta gayyato ƙawayenta suzo ayi ta hira ana koɗa jin daɗin da take yi a makeken gidan nan.
Tsaki yayi jin buga ƙofar tayi yawa, ya fito yana murza ido don dama yau zai sake fita neman aiki ko Allah zai sa a dace, kwanan nan kuɗin cefane ma mahaifinshi ke basu.
Ƙofar shigowa ya buɗe don yasan Asiya nacan na baccin asara, idanunshi ne suka sauka kan mai gidan daya basu haya, gaban Bello ne yayi wani mugun faɗuwa, ba dai har sun cinye kuɗin hayar su ba? Tabbas tun wancan watan yake ganin kiran mutumin yana ignoring gani yake yi surutun banza zai yi mishi. Yanda mutumin ke kallonshi ne yasa jikin Bello ƙara yin sanyi.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN*
{90}
Murya na rawa yace mishi "Yallaɓai barka da asuba." A wulaƙance mutumin ya kalle shi yace "Kai ba wannan ya kawo ni ba," hannu ya miƙa mishi yace "Bani." Kallonshi yayi ya kalli hannun da yake miƙo mishi yace "Me zan baka?" Gabanshi yana dukan uku-uku don yasa yau dai ƙaryarshi ta ƙare. Wani irin kallo yayi mishi yace"Kuɗin hayata ko makullan gidana." Duk da yasan abinda ya kawo mutumin kenan sai da yaji wata irin faɗuwar gaba ta ziyarce shi, yanzu idan aka koreshi daga gidan nan ina zai je? Cikin ƙasƙantar da kai yace "don Allah kayi haƙuri zuwa..." Ɗaga mishi hannu mutumin yayi ya dakatar dashi daga abinda yake cewa yace "Tun wancan watan hayarka ta ƙare don rainin wayo ina ta kiranka a waya kayi banza ka rabu dani ko bin bayan ƙiran baka yi ba sai yanzu ne zaka wani karkace wuya zaka yi min ƴar murya, to bazan lamunta ba idan kana so ka cigaba da zama a gidana ka biya kuɗin haya idan ba haka ba kuwa ka tattara ya naka ya naka ka ƙara gaba ina da mutanen da zan sa a gidana."
Karkata kai yayi ya hau bawa mutumin haƙuri don yasan idan yace ya fita ya bar mishi gidanshi baya da wurin kamawa, "Dan Allah kayi haƙuri Yallaɓai kayi min lamunin kwana biyu In Sha Allah zan kawo maka kuɗinka har gida." Haka nan dai yayi ta bawa mutumin haƙuri har ya samu ya haƙura akan idan kwana biyu ta cika bai biya shi kuɗin hayar gidanshi ba zai fita ya bar mishi gida. Mutumin na tafiya ya juya ya shige cikin gida yana tunanin abun yi, yanzu a ina zai je ya samo wannan iyayen kuɗaɗen a cikin kwana biyu shi ba aiki ba shi ba wata sana'a ba. Ɗakin shi ya shige ko wanka bai yi ba ya canja kaya ya ɗauki makullin motarshi wacce da ƙyar ya samu Asiya ta dawo mishi dashi hannunshi ya fice daga gidan yana tunanin inda ya kamata ya fara zuwa.
Tunani yayi gara yaje ya samu mahaifin shi watakila akwai taimakon da zai iya yi mishi. Bai damu mahaifinshi a gida ba fon haka ya bi bayanshi zuwa kasuwa. Ya yiwa mahaifinshi bayanin abinda ke tafe dashi. Wani irin kallo yayi mishi yace "To yanzu ya kake so ayi?" Ɗan shiru yayi yana sunkuyar da kai don sai yanzu yaji takaicin zuwan shi gaban mahaifin nashi bayan ko lokacin da zai kama hayar gidan sai da ya hanashi amma yaƙi ji, to amma idan ba Baban ba wurin wa zai je ya faɗi damuwarshi?
Kanshi a ƙasa yace "Kayi haƙuri ka yafe min Baba, ban kasance ɗa na ƙwarai a wajenka ba duk abinda ka haneni dayi shi nake yi, wallahi nayi nadamar abubuwan da nayi tayi, ka taimakeni na samu na biya kuɗin hayar In Sha Allah zan yi ƙoƙari na biyaka cikin lokaci." Tsaki Baban yayi yace "Dame zaka biyani idan na ɗauki iyayen kuɗi da yawa tsababa na baka kai da ba aiki kake yi ba ba sana'a ba?" Da sauri yace "Ai ina neman aiki In Sha Allah ina sa rai da zan samu da an fara biyana zan yi ƙoƙarin haɗa maka kuɗin ka." Kallon baka da hankali Baba yayi mishi sai kuma yace "To ita motar da kake yawo da ita miye amfaninta da baza ka sayar ka biya kuɗin hayar ba?" Ai bai san lokacin da ya ɗago ya kalli Baba ba, taya zai ce ya sayar da motarshi motar da ita kaɗai ta rage mishi, kai gaskiya a'a ba zai taɓa yiwuwa ba sam ya sayar da motarshi.
"To idan ba zaka sayar ba sai ka tattara ka bar musu gidansu idan yaso ka dawo gida ku buɗe ɗakinka na da ku zauna a ciki." Tashi yayi jiki a saluɓe ya bar wajen Baba, zai dai yi ƙoƙari daga nan zuwa kwana biyu yaga ya haɗa kuɗin hayar ya biya idan kuma hakan bata samu ba dole Asiya tayi haƙuri su tattara su koma gidansu da zama idan yaso sai su sayar da kayan ɗakin da yayi mata yaja jari tunda gidan nasu ɗaki ɗaya ne babu inda za'a zuba duka waɗannan kayan a ciki.
*****
*BAYAN SHEKARA GUDA*
A cikin shekara guda data gabata Baqeer yayi nasarar buɗe shagon shi na ɗinki mai suna *MOHBAQ TAILORING SERVICES*, sosai Allah yasa mishi albarka a ciki ta yadda kullum cikin samun sababbin customers suke. Designs ɗin ɗinkunansu idan har suka yi maka baka taɓa ganin su a ko ina sai a jikin wanda suka yiwa irin shi. Saboda yadda suke tsara designs ɗin su yasa ba kowa ke iya kwafarsu ba masu gwadawar ma sai dai su kamanta amma ba dai suyi shi sak da sak irin yadda suke yin nasu ba. Sosai shagon shi ya samu karɓuwa saboda bayan kaya da mutum zai kawo su ɗinka mishi har da ready-made suna ɗinkawa daga kayan maza har na mata babu wanda basa ɗinkawa kuma duka styles ɗin da suke yi Baqeer ne ke ƙirƙirar designs ɗin su kuma yaran shagon sai su ɗinka yawanci ma shi yake yin yankan da kanshi ko shi ko Tanimu, ganin yana samun kuɗi sai ya zuba irin machines ɗin da yake buri, wasu irin machines ne da suke amfani da computer. Hoton designs ɗin da ake so kawai za'a saka shi zai ɗinka maka automatically don haka aikin yake zuwa musu da sauƙi, idan machines ɗin suka yi zanen surfanin da suke so su kuma sai su haɗe kayan. Bayan shi da Tanimu da ya kasance kamar manager a wurin ya ƙara samun wasu yaran da suke yi musu aiki saboda yadda suka samu karɓuwa ayyuka na yi musu yawa.