Sashe 111
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
{67}
Tana fita daga falon ɗakinta ta nufa nan da nan kuma tausayin Junaid ya ziyarci zuciyarta, ta sani bata kyauta mishi ba sai dai babu yadda zata yi don kuwa babu abinda zai sa ta aureshi, duk wani abu da Daddy zai yi sai dai yayi amma ita dai babu mai tilasta mata aurenshi, Baqeer take so kuma yanzu ta sani shine jigo na rayuwarta ko da ba zata iya furta mishi ba zata jira lokacin daya shirya sanar da ita abinda ke ranshi akanta. “Kina tunanin yana sonki ne?” Tambayar data zo kanta kenan ji tayi abin duniya ya isheta, pillow ɗin dake kan gado ta ɗauka ta cillar ƙasa, wani irin takaici na ƙara kamata, sallar magriba tayi sannan ta zauna tana jin yunwa amma ɓacin rai ya hanata neman abinci.
Junaid kuwa da ƙyar ya iya kwasar ƙafarshi ya bar gidan don ji yayi kamar an ɗebi ruwan sanyi an kwara mishi, mota ma da ƙyar ya iya shiga yayi zuru yana tunanin ta yadda zai yi ma ya kunna motar yaja ya tafi gida, yafi minti goma a ciki kafin ya daure yaja motar sai dai tafiya kawai yake yi babu wani laka a jikinshi.
Mummy ce ta turo ƙofar ɗakin riƙe da tire na abinci, Zee tana ganinta ta sake jan bargo ta rufa, zama tayi kusa da ita tace “Auta tashi don Allah kin dai san bana son wannan halin ko?”
Kallonta tayi cike da shagwaɓa tace “Allah Mummy ba wai naso wulaƙanta Junaid bane kawai dai nasan in ban faɗa mishi maganganu ba bazai ƙyaleni ba.” Kai Mummy ta jinjina tace “Hakan shine daidai in har kasan abu ba zai zama alheri ba to tabbas kar ma ka soma bawa mutum false hope, shi Daddynki muƙaminshi yake dubawa sai dai ni farin cikin ki nake dubawa, Nabila ta ruguza mana farin cikin gidan nan ba zan yarda ke ma a ruguza miki farin cikin rayuwarki ba.” Ƙanƙame Mumy tayi tace “Na sani duk duniya babu mai sona sama dake, ke kaɗai ce gatana shi yasa a koda yaushe nake alfahari da kasancewarki mahaifiyata.” Shafar saman kanta tayi tace “Nice zan yi alfahari Zeey baki san yadda nake farin cikin kasancewa tare da ke bane.” Ɗagowa tayi kaɗan tana kallonta tace “Wannan sakaliyar ƴar taki da bata iya komai ba?” Kuncinta taja tace “Sai me? Sannan menene zai sa ki koyi wani abu bayan muna da kuɗin da zamu yi providing ɗinki with everything you need? Burina kiji daɗin rayuwa bawai ki wahala ba, ko aure ki kayi na faɗa miki zan haɗaki da mai kula da komai naki babu abinda zaki yi sai hutawa.” Dariya taɗan yi kaɗan tace “Mummy ni kam tambaya, Aunty Nabila tana son Ya Kabir ne?” Yanayin Mummy ne ya canza ta ɗan janye kaɗan tana cewa “Bana son zancen yarinyar nan sam, sannan gobe da safe zamu je asibiti daga can wurin Inna zata koma.”
Cike da rashin jin daɗin kalamanta Zee tace “Mummy me yasa ne sam ba kya tsayawa ki fahimci halin da take ciki? Yanzu tun bayan faruwar abun nan kin duba ta? Kinji ya take ciki? Kin tambayeta halin da take ciki?” Mummy ta kalleta jiki a sanyaye tace “Ba sai na tambayeta ba don kuwa bana son jin komai, ni zamanta a gidan nan ma ba so nake yi ba, balle yanzu da ta gama ja mini cin mutunci.” Mamaki gaba ɗaya sai sake rufe Zeey yake yi kawai ji tayi bazata iya magana ba, hakan yasa ta sake jan bargo ta rufa, Mummy ta yaye bargon tace “Tashi kema kici abinci, ai Zabba’u tace kin sa an yiwa Kabir abinda zai ci amma ke baki yi tunanin kice ayi miki ba.”
“Aunty Nabila fa? Taci abincin ne?”
Mummy ta tsuke fuska sosai tace “So kike muyi faɗa?” Shiru Zeey tayi kawai tana kallonta, ajiye mata abincin tayi sannan ta shafi gefen kanta ta fita, ga mamakinta Nabila ce tsaye a ƙofar ɗakin kamar dama jiranta take yi ta fito, yi tayi kamar bata ganta ba sai jita yi tace “Ki gama kauce-kaucen dole zaki dawo kibi bayana.” Wani kallo Mummy tayi mata tace “Ke yanzu laɓe ma ba abin kunya kika ɗauke shi ba naga alama, ki haɗa kayanki da safe daga asibiti gidan Inna zan kai ki.” Da sauri tace “Babu fa inda zani don ina nan har sai anyi aurena da Kabir.” Wani banzan kallo Mummy tayi mata tace “Waye zai yi miki auren?” Da mamaki tace “Wa kuwa in ba Daddy ba?” Tsaki Mummy taja tace “Na kula har yanzu hankalinki bai dawo jikinki ba, mutumin da yace a zubar da cikin jikinki shine kike tunanin zai aura miki ɗanshi? To ki buɗe kunnuwanki kiji da kyau in ma bacci kike yi ki farka Senate duk yadda yake yabon kyawawan halayenki a wurinshi baki kai ya aura miki ɗanshi ba,” tana kaiwa nan ta cigaba da tafiya cike da takaicin shirmen Nabila, shi yasa take ta nuna mata a’a amma ita sam ta kasa ganewa. Nabila kuwa kasa ko motsi tayi har Mummy ta ƙule bata iya cewa komai ba, ɗakinta ta nufa hankali a tashe ta fara cin babban farcenta na hagu jikinta har karkarwa yake yi saboda tsoro, ta shiga uku, yanzu ya zata yi?
(Umm Asghar da Ayusher kam muka ce muma bamu sani ba🥴)
********
Baqeer kam da Zee ya kwana a ranshi yana tashi asuba bayan yayi sallah yayi addu’oi kiran wayarta yayi haka nan yaji zuciyarshi baza ta iya jira gari ya waye ba tare da yaji muryarta ba, Zeey ita ma tayi sallah kenan don ta ɗan makara kaɗan saboda tunanuka da suka yi mata yawa, ganin kiran Baqeer yasa tasa a ranta zata tambayeshi matsayinta da safen nan don ta samu ta yiwa Daddy bayani akwai wanda ma take so, ajiyar zuciya tayi sannan ta kishingiɗa akan gado ta ɗaga wayar. Shiru suka ɗan yi kaɗan kafin yace “Ba sallama?” Tace “Assalamu Alaikum!” Yace “Wa’alaikissalam kin ware yanzu?” Ta ƙara gyara kanta tace “Bayan baka damu dani ba baka kira da daddare kaji ya nake ba.” Da sauri yace “Inji wa?” Sai kuma yayi shiru, kallon wayar tayi cike da mamakin kalamanshi don ta tabbatar daga ƙasan ranshi ya fito tace “To ba haka bane?” “Umm!” Tace “Umm?” Yace “Eh to shikenan? Seriously na ɗauka kin kwanta ne.” Murmushi ta saki kamar yana ganinta tace “Guess what?” Yace “Me?” Tace “kayi guessing kai dai.” Ɗan nazari kaɗan yayi yace “Kun samo solution?” Ta girgiza kai tace “Nope! Abinda ya shafeni ne ni da kai.” Nazari ya sake yi yace “Menene?” Ta ɗan sake rage murya tace “Wasa nake yi.” Murmushi yayi sosai yace “Na manta wa nake waya da ita ashe.” Shiru suka ɗan yi kowa da abinda ke ranshi kafin yace “Is everything alright?” Ta ɗan yi shiru kafin tace “A’a komai ya sake wargajewa, sai dai ina fatan komai ya tafi daidai.” Jiki a sanyaye yace “In Sha Allahu komai zai tafi daidai.”
“Jiya Junaid yazo,” ta faɗa cike da son jin me zai ce, Baqeer kuwa nan da nan ya haɗe rai, ai bai tambayeta zancen saurayinta ba bare tace amsa ta bashi tunda ya tambayeta, shiru yayi hakan yasa tace “Ya Baqeer kaji me nace?” Cikin dakakkiyar murya yace “Eh!” Shiru tayi don yadda ya amsa yasa ta rasa me zata ce, can tace “Akwai abinda nake son faɗa maka amma ba gobe ba sai dai ko jibi.” Cike da son jin menene yace “Kuma sai a bar ni da tunani har kwana biyu?” Kallon wayar tayi kafin tace “Ni wacece a wurinka wacce in nace zan faɗa maka magana baka so ta daɗe ban sanar maka ba?” Shiru yayi yana son cewa “Muradin zuciyata, wacce zuciyata ke bege a koda yaushe," sai dai ganinshi a keken guragu da irin ƙatuwar motar da take hawa da ƙatuwar mota da aikin Junaid yasa yaji ya kasa cewa komai, shi a wa? Jin shiru yasa Zee jikinta yin wani mugun sanyi, muryarta cikin sanyi tace “Kayi tunani jibi in mun haɗu ka faɗa mini in har baka san matsayina a wurinka ba to a gabanka zan goge number wayarka sannan ni da gidan Dada kuma shi kenan har abada don banga amfanin cigaba da tarayyarmu ba.” Tana kaiwa nan ta kashe wayar, kifa kai tayi tana tunanin wannan shine mafitar data dace da ita, wai ita yarinyar da bata yarda da so ba ita ke zubar da ajinta akan ɗa namiji? Bayan tasan duk ranar da yasan ita wacece shikenan alaƙarsu ta ƙare? “Ya Allah!” Ta furta a fili tana jin wani yanayi a cikin zuciyarta.