← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 168

Sashe 36

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*******
A bangaren Baqeer kuwa Dada ta sakashi ya fito falo yana zaune yana kallonta tana ta ƙoƙarin bashi labarin tasowar Umma duk don taga ya saki jikinshi sai dai kawai kallon gefe yake yi babu alamar hankalinshi na inda take, jiki a sanyaye take kallonshi ita kam Baqeer ɗin daa take son gani, sallamar Salim suka jiyo, ta amsa ba tare da tasan wanene ba, sai daya shigo ta ganshi, cike da fara'a ta amsa tace "Salim yau kai ne a gidan?"
Ya shiga yana dariya yace "Tunda kin gujeni kuma me zaki ce mun?"
"To kai in banda abinka in na aureka ai sai dai a binne ni da kai don tabbas baka isa ka rabu dani ba sannan ko aure baka isa kayi ba ko na mutu."
Dariya sosai yasa yace "Wai abun haka ne dama? To ai ana auren ɓoye."
"Ahaf kai na mutu'a ma kagani."
Sun dade suna tsokanar juna sai dai Baqeer ko kallon inda suke bai yi ba, jiki a sanyaye Salim ya mika mishi hannu yace "Baqeer don Allah kayi hakuri kaji?"
Bai kalleshi ba har yanzu idanunshi na gefe, yana murmushi yasa hannu a aljihu ya ciro kudi yace "Umma ce ta bada zamu je muga likita yanzu."
Da kallo yabi kuɗin nan da nan yaji kanshi na wani irin sarawa, ina Umma ta samo kuɗi haka? Kanshi kawai ya shiga girgizawa yana neman tunano inda ta samu wannan kuɗin, ya tabbatar injin taliyarta ta sayar kila ma har da kayayakin ta. Hannu yasa kawai ya hau dukan ƙafarshi da hannun hagu yana wani irin numfashi, A zabure Salim ya taso yana ƙoƙarin janyeshi sai dai Baqeer cikin sauri ya tura kekenshi ya fara tafiya, binshi Salim ya nemi yi Dada ta girgiza mishi kai, har Baqeer yayi ciki ya banko ƙofar da karfi kai kace ɓallata yake son yi.
Suna daga waje suna jiyo yadda yake ihu da alama kafar yake ci gaba da duka, dukkansu basu san sanda hawaye ya gangaro musu ba, Salim yana hawaye yace "Dada ya zamu yi da Baqeer?"
Ido kawai ta runtse tace "Addu'a babu yanda zamu yi dashi sannan wannan halin da yake ciki shine zai maidashi jajirtacce, dole yasan rayuwarshi ta daa da kuma ta yanzu ba ɗaya bace, sannan dole ya miƙe ya nemarwa kanshi mafita ni da kai da ita Fatiman duk babu abinda zamu iya yi mishi in har shi bai shirya canzawa ba."
Ya daɗe a cikin wannan yanayin kafin ya samu nustuwa, me za ayi da rayuwarshi? Ya tabbatar iyayenshi da zai faɗi ya mutu yanzu hankalinsu sai yafi kwanciya.
Jin shiru yasa Dada ta buɗe ƙofar tace "Kazo kuje asibiti lokaci na ƙurewa, magana ce bai son yi sai dai yaja ya turje, ta kalleshi tace "Kasan dai ni kakar kace ko? To in har na isa da kai ka wuce ku tafi."
Kallonta yayi yana son sanar da ita kuɗin injin taliyar Umma ne fa sai dai ba zai iya ba ji yake yi baya son ko furta kalma ɗaya har ajalinshi yazo. Haka Salim ya jashi suka shiga mota, wani kamshi ne yaji wanda yasa yaji zuciyarshi ta samu wata nutsuwa da shi kanshi bai san daga ina ta fito ba, idanunshi ya maida ya kulle yana ɗan maida numfashi sama-sama, har suka isa asibitin bai yi magana ba, suka shiga ciki Doctor ya musu magana akan tun last week ya kamata suzo amma basu zo ba, nan Salim ya bada hakuri aka kwance naɗin karayar da aka yi mishi ya sake duba Baqeer sannan ya rubuta musu magunguna, dubu takwas Salim ya siyo magungunan, suka koma mota, har yanzu kamshin motar ɗazu yana nan, ya sake kwantar da kai jiki a sanyaye ya cewa Salim "Salim don Allah ka ji da kasuwancinka kada ka damu dani wannan yawon da kake zai iya dakushe maka kasuwarka."
"Baqeer mu dai fatan mu ka cire wannan damuwar dake ranka kana dai ji Dr yana cewa depression ne yake damunka don Allah ka....."
Kanshi ya kawar gefe wanda hakan yasa Salim yin shiru, sun dade babu wanda yayi magana sai can yace "Motar waye wannan?"
Kallonshi Salim yayi, anya yace mishi ta Zainab ce? Bayan kaf unguwarsu shekarun baya sun san cases ɗin daya shiga tsakanin mutanen biyu? Wanda a dalilinshi su Zeey suka tashi daga unguwar?

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Umm Asghar ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*

*BAQEER*
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
*DA*
*UMM ASGHAR*

*PAID BOOK*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA ƊAYA*

{22}

"Ta wani abokina ne da muke mutunci sosai na aro tunda kasan ba zai yiwu mu ɗauki motar haya a wannan marrar da ake ciki ba ga nisan wuri ga tsadar mai". Jinjina mishi kai kawai yayi ya juyar da fuskarshi yana kallon waje. Har suka ƙarasa gidan Dada babu wanda ya ƙara magana don tun Salim na takalarshi da zance har ya haƙura yayi shiru ganin ba kulashi zai yi ba. Da taimakon wasu almajirai da suke yawan zama a ƙofar gidan Dada Salim ya samu suka fitar da Baqeer daga cikin mota suka ɗaurashi akan keken. Godiya yayi musu sannan ya turashi suka shiga cikin gidan. Sai da yayi wa Dada bayanin duka magungunan da aka rubuto mishi ta tabbatar mishi zata kula da bashi akan lokaci sannan ya sallame su ya tafi.

Yana shiga unguwarsu yayi kiran Zeey a waya yace mata ya dawo ya za'a yi ya kawo mata motar, sai cewa tayi yayi parking ɗan nesa kaɗan da gidansu zata fito ta karɓa. Hakan kuwa aka yi don bai wani daɗe da tsayawa ba sai gata ta fito, yana ganin fitowarta ya buɗe motar ya fito shima yana murmushi. Miƙa mata mukullin motar yayi yana ta godiya don sosai ta taimaka musu da basu aron motar da tayi in banda hakan da sai dai ya ɗauki drop ɗin taxi ya kuma san kuɗi ne za'a kashe ba ƴan kaɗan ba. Karɓa tayi tace mishi "haba dai ai babu komai yiwa kai ne, ni nasan irin taimakon da zaku yi mini ne a gaba, fatanmu dai Allah yasa an dace da abinda kuka je yi asibitin".

"Ah Alhamdulillah don an kunce ɗaurin ma kuma likitan yace gyaran yayi kyau sosai sai fatan Allah ya ƙara mishi lafiya".

"Masha Allah, ni bari na wuce sai mun ƙara haɗuwa kenan".

Yace mata "to Zainab nagode ƙwarai Allah ya bar zumunci".

"Ameen Ya Rabbi" kawai tace ta shige motarta taja ta ƙarasa da ita gidansu, sai da tayi horn maigadi ya taso ya buɗe mata gate har ta shige ciki sannan Salim ya juya zai bar wurin. Yana juyowa suka kusa yin karo da Kamalu da tun ɗazu yake dakon dawowar Salim ɗin don haka akan idonshi Salim yazo ya wuce da motar Roshni ɗin tashi, har tsayuwarshi da duk maganganun da suka yi shi da Roshni ɗin akan idonshi suka yi sai dai baya jin me suke cewa, shi satar babur ɗin da aka yi mishi ma bata dameshi ba kamar tsayuwar Roshni da wancan tsageran yaron da yake jin kanshi kamar yafi kowa saboda kawai yana abota da wancan gurgun. Ƙwafa yayi cikin ranshi yana jaddada dole ma yaci uban yaron nan Salim don yaga alamun yana so ya kawo mishi raini tunda har yake zuwa wurin Roshni masoyiyar zuciyarshi.

Kallonshi Salim yayi yace "Mallam lafiya zaka tare mini hanya?". Wani irin kallo yayi mishi irin na sama da ƙasa ɗinnan kafin cikin fusata yana nuna shi da ɗan yatsa yace "zuwa nayi naja maka kunne ba naga kanka yana rawa ba ka fita daga hanyar Roshni ɗita ita ɗin ba sa'ar yinka bace idan kuma kaƙi ji wallahi kaji na rantse jikinka ne zai gaya maka". Wata irin dariya ce ma ta zowa Salim ganin yadda ya dage yana zuba masifa har kamar ya kai mishi duka, kasa riƙe dariyar yayi sai da yayi abarshi sannan ya tsagaita ya kalli Kamalun da irin kallon da yake yi mishi yace "wacece kuma hakan? Kai kaga nayi maka kama da wanda zai tsaya yana kula irin tarkacen ƴammatan da kake kulawa marasa nutsuwa da kamun kai? Da Allah Mallam kauce mini daga hanya ni na wuce don ina da abun yi ba irinka bane zauna gari banza marasa aikin yi sai dai yawo daga wannan inuwar zuwa waccan kuna jiran ƴan Allah ya baku mu samu".
Chapter 36 · 0% Book details