Sashe 46
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*****
Zeey ce zaune a ɗaki ta shige cikin bargo tana kallon korean drama ‘Killing Vote’ mind dinta gaba ɗaya yana kan tv ɗin dake manne a bangon ɗakinta, wayarta ce tayi ƙara da takaici ta janyota, number ce hakan yasa ta kara a kunnenta ba tare da tayi magana ba, Baqeer shima kasa magana yayi sai sautin numfashinsu ne daya sauka a tare, Zeey cike da mamaki ta kalli wayar tata ta sake karawa a kunnenta haka kawai taƙi yin magana don rainin wayon ya isa a kira ka a waya a ƙi magana kuma. Baqeer kuwa ji yayi ya kasa cewa komai, to yace me? Mun gode karki sake? Ko kuwa karki sake zuwa? Bayan yasan in tace ta daina ba daɗi zai ji ba. Takaicin kanshi da rashin sanin abinda zai ce duk ya isheshi.
Zeey ranta ya ƙara ɓaci don ta tabbatar wannan kuma rainin wayau ne, a speaker tasa wayar kawai ta ajiye a gefe ta cigaba da kallonta, Baqeer ganin kuɗin shi na tafiya ba tare da yasan me zai ce ba yasa ya kai hannu zai kashe wayar, mamaki ne ma ya kamashi da ya fara jiyo sautin kallo a cikin wayar, nan ya kashe tare da ajiye wayar akan katifarshi, haushin kanshi ya ƙara kamashi, haka zai zauna komai bai iya ba kamar wani yaron da aka haifa yanzu?
Ƙofa ya buɗe Dada na ganinshi ta ɗauke kai ta cigaba da tsinke zogalen da take yi, kusa da murhu ya nufa ya sunkuyo taga yana neman haɗa wuta, duk yanda taso ta ƙunshe dariyarta kasawa tayi haka tana gani ya haɗa wuta yasa tukunya da ruwa, Dada abin sai ƙara bata dariya yake da yanda fuskarshi take a ɗinke babu alamun fara’a, yana gamawa ya koma ɗaki. A hankali ta girgiza kai lallai Baqeer babu shakka zuwan yarinyar nan da shawarar da take bashi yasa ya fara canzawa, murmushi ta saki ko ƴar gidan wacece? Tabbas zata tambayi Maryam in tazo.
Zeey kuwa ganin an kashe wayar tayi tsaki tace “Ni dai kwanan nan ban san da wasu irin mutane nake haduwa ba.”
Ta sake maida hankali kan kallon aka sake kiran ta, kanta ta cusa cikin bargo ta ɗan yaye bargon tana bubbuga ƙafafunta, cike da takaici ta janyo wayar gwara ta dauka in kudinsu ya ƙare sun daina damunta, tana ɗauka tasa a speaker ta ajiyeshi a gefenta “Don Allah a maidani kunne bana son a ajiyeni a gefe.”
Kalaman da suka fito kenan daga cikin wayar wanda ya sata bin wayar da kallo, ganin number Junaid ya sata sakin murmushi sosai wanda har haƙoranta suka fito “To ya?”
“Haka dai zaka cigaba da saka mini ido kamar mai CCTV ko?”
Shima murmushin yayi yace “To ni dai ɗari bisa ɗari ina da yaƙinin babu wanda yasan ki sama dani.”
“Shiyasa ka turo a ganni?”
Dariya yasa yanzu kam tace “Kar ka wani wayance nasan kaine.”
Ya ɗan yi juyi a kan gado yace “Wato dai kin gama sanina kema?”
Kafaɗa ta ɗaga kamar a gabanshi take tace “Ai ƴar ƙure ne abun?”
“Na sakar miki ƙotar don nasan tabbas aka fara tsab za’a ƙure ni.”
Hira suka cigaba dayi sosai wanda kana ganinsu kasan sun saba da juna sosai, can tace “Ya aikin ba zaka dawo nan ka cigaba ba?”
Ajiyar zuciya yayi yace “Dole na dawo tunda an ce na aureki.”
Kai ta girgiza tace “Kasan dai bazan aureka ba, na sha faɗa maka abota ne kawai a tsakanin mu.”
“Nima na sha faɗa miki abota tana komawa soyayya, kuma a kaina zaki amince.”
Shiru ta yi jin wani abu yazo ranta, da sauri ta gyara zama tace “Junaid please serious magana when will you be back? Akwai wani brothern ƙawata da ya samu matsala a kafafunsa, an dai ce paraplegia ne so nasan ku da yake aikin ku ne kun san ko akwai wani abu da mutum zai yi.”
Cike da kulawa yace “Subhanallah, garin yaya?”
Tace “Am not sure exactly nasan dai accident yayi.”
Ya ɗan yi ajiyar zuciya yace “Lallai he needs us, kinga karatun da aikin da nake kenan na physiotherapist so ina saka ran nan da 4days zan dawo don abinda ma na kira na sanar dake kenan, idan na dawo zan fara aiki a asibitin Dad ɗina in yaso sai ki ma friend ɗin taki magana su kawoshi mu gani, ko bai warke ba at least zai iya controlling ɗin jikinshi.”
Wani irin daɗi ne ya kamata wanda yasa shi cewa “Yana da aure ne?”
Tace “A’a menene?”
Shiru ya ɗan yi sai dai yasan Zee ba yanda za ayi taso gurgu yarinyar da manyan maza kyawawa masu kuɗi ma bata kulasu ba. Da wannan suka cigaba da hira kafin suyi sallama, wani nishaɗi ne kawai yake sake rufeta don Junaid har shaidar yabo an bashi saboda ƙwazonshi tana saka ran zai taimaki Baqeer sosai, ji take ba zata ba gobe saboda akwai inda zasu da Mummy amma jibi zata je ta sanar mishi.
******
Hadiza ce kawai ke share hawayenta ganin ta rasa me zata dafa a cikin gidan, gidan babu komai balle ta lallaɓa ta dafa wani abun, gashi ko naira biyar bata da shi balle ta sa a siyo mata kuka, yarinyarta tasa a baya ta fito daga ɗaki, kishiyarta dake wanke tsakar gida ta kalla don ko abinci basa hadawa saboda ita tana ɗan aikinta na gwamnati tana samun ƴan kuɗaɗen ta.
Gida ta nufa tana tafe tana hawayen tunanin Baqeer don tabbas wannan abu ita yafi shafa.
A ƙafa taje tafiyar sama da minti ashirin, da Salim suka haɗu shima zai je gidan Umma, nan suka gaisa suka ƙarasa gidan sun ƴar hira, ta bayansu kawai suka ga an tallewa Salim ƙeya sai ji kake tass.
Da sauri suka juya a tare, Kamalu ne anci riga da wandon gayu yana girgiza ƙafa, Bashir na gefenshi don ya kira shi zai aikeshi ne ya hango Salim ya taho da sauri shima yabi bayanshi.
Da mamaki Salim yake kallonshi yace “Kamalu menene hakan?”
Daƙuwa yayi mishi yace “Gidanku ne, uban me kazo yi gidan mu? Ko zuwa kayi kaja faɗa dani don na ƙwace Roshni ta dawo inda ya kamata?”
Wani kallon mamaki yayi mishi yace “Yanzun ma zancen Roshnin ne?”
A ƙufule Kamalu yace “Kasan Allah inma ni kake nema da fitina daidai nake da kai, muje filin casu kaga hauka.”
Tsaki Salim yayi yana neman shiga ciki Kamalu ya finciko shi yace “Wai ni ka yiwa tsaki? Kai dan gidanku ni sa’anka ne?”
Salim na neman ƙwace jikinshi amma Kamalu sai hayagaga yake yi yana zage-zage wanda yasa Hadiza saurin shiga ciki don ya kira azo ayi mishi magana.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Umm Asghar Ce*
*Da*
*Ayusher Muhd*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS*
{28}
Bashir ne ya rirriƙe Kamal daga ƙoƙarin kaiwa Salim duka da yake yi shi dai Salim yayi tsaye kawai yana kallon shi da haukar da yake yi don baya saka Kamal a sawun mutane masu hankali. Umma ce ta fito daga cikin gidan tana cewa "Kamal lafiya kuwa?" Don ko da Hadiza ta shiga gida ta faɗawa Abu ko zata fito tayi mishi magana gashi can a ƙofar gida yana cakumar Salim da faɗa cewa tayi babu inda zata, ai haka nan Kamalu ba zai nemi rigima dashi ba sai idan shi ya fara tsokanarshi don haka a ƙyaleshi yaci ubanshi yadda gobe ko kallon banza bai isa yayi mishi ba tunda yasan idan yayi ma ba ƙyaleshi zai yi ba, sai Umma ce ta saka hijabinta ta fito jin da Salim ake faɗan tasan kuma wurinta yazo tunda dai Baqeer baya gidan yanzu bare tace ko wajenshi yazo.
Wani banzan kallo yayi wa Umma yace "Malama ki rabu dani na koyawa wannan tsageran yaron hankali, kai har ka isa kayi mini tsaki a ƙofar gidanmu don ubanka?" Ya nuna Salim da yatsa yana ƙoƙarin kai mishi mari sai dai Bashir ya rirriƙe shi ya hanashi kaiwa ga Salim ɗin. "Umma ina yini" Salim ya durƙusa yana gaisheta kamar ba da shi Kamalu ke faɗan ba.
"Lafiya lau Salim, me ya haɗa ka da Kamalu ne?"