← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 168

Sashe 127

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*******
Zee dake zaune a falo ce ta miƙe ta nufi kitchen inda su Ummi suke don dama abinda ya fito da ita kenan daga ɗaki, tana son bin shawarar Baqeer hannayenta na baya yana ɗan motsi dasu tace “Ummy dame zan taya ku?” Kallonta Ummy tayi kafin ta ɗan sauke ajiyar zuciya tace “Me zaki iya daga abubuwan da muke yi?” Kallonsu tayi Ummy na yanka kayan miya, Inaya na tsinke zogale, cike da son jin bakinta Ummi tace “Ko zaki tayamu da wanke-wanke?” Ido ta zaro da sauri tace “A’a gwara abinda Inaya ke yi bansan taɓa kayan da aka ci abinci.” Mamaki me ya kama Ummi kawai ta girgiza kai don bata san ma me zata ce mata ba, zama tayi babu kunya suka tsinke zogale sai wani daɗi take ji tana so taji Ummi ta yabeta, ita kam Ummi kasa tanka mata tayi don bata san me ma zata ce ba saboda takaici. Inaya ce ta shiga banɗaki tana fitowa taji wayar Zee na ƙara hakan yasa ta fito mata dashi ta bata, kallon wayar tayi ganin Kabir yasa ta ɗauka da sauri don ta haɗa su da Ummi su gaisa, shi kam tana ɗauka yace “Wato kinci moriyar ganga ko? A wani dalilin Mummy zata yi ta nemanki ki dinga ƙin dauka? Naji tayi miki laifi amma ai sai ki yi mata uzuri kiji dalilinta ko? Ko ba haka ake so ƴaƴa su yiwa iyayensu uzuri ba?” Zee ta kalli Ummy da ita ma kallonta take yi sannan tayi ciki da sauri, ba tare da ta rufe kofa ba ta shiga ɗaki tace “Ya Kabir me kake yi hakan? Sannan ai kaima kasan abinda tayi mana bata kyauta ba ko?”
Tsaki yayi yace “In ta mutu kya yafe mata tunda wacce kika tafi wurinta itace ta raineki har kika kai girman haka, wannan halayen naku na mata shi yasa mata suke tsoron riƙe yaro da zuciya ɗaya.” Hankalinta ne ya ɗan tashi tace “Bata da lafiya ne?” Cike da takaici yana haɗe fuska yace “Eh gata nan ana ƙoƙarin sa mata drip kada Allah yasa kizo kiga jikinta,” yana kaiwa nan ya kashe wayar, Zee tace “Yaya! Yaya! Yaya!” Sai dai ya riga ya kashe, fuskarta tasa da hannaye biyu ta shafa, kallon bakin ƙofa tayi inda Ummi ke tsaye da alama biyota tayi da son jin meke faruwa, idanunsu ne ya haɗu da juna, Ummi tayi murmushin yaƙe tace “Kije kafin wani abun ya faru, na ɗauka ta daina wannan ƙananan shirmen ashe har yanzu bata san ta girma ba.” Kalaman da taji Ummi ta furta kenan wanda yasa ta kallonta fuskarta cike da mamaki, ganin Ummi zata juya yasa ta saurin cewa “Me kike nufi da kalamanki Ummi? Kina nufin ƙarya Mummy take yi kenan ko me?” Waigowa tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace “Ki koma ki tambayeta, sannan ki haɗa da tambayar da nima nake son sanin amsarsu, me ƴan uwana take cewa sun yi kamar yanda kika ce shine dalilin hanasu zuwa da Babanku yayi? Dan a iya sanina babu wanda ya taɓa zuwa don neman taimako gidanku duk zuwan da wani zai yi to fa lallai babban dalili ne ya kai shi saboda dukansu sun san waye Sulaiman, kayan da nake ɗinka muku shekaru kusan ashirin suna ina? Sannan number wayar data aiko min da sunan wayoyin ku nasu waye? Ahh abu na ƙarshe me da me muka yi da har Sulaiman ya aiko har Ɗambatta akan kar ya ƙara ganin wani daga cikin mu a gidanshi, in har ta sanar dake duka ina so ki sanar dani don mu san dalili,” Ummi tana kaiwa nan tayi gaba zuciyarta na wani irin zafi don lallai abubuwan nan sun fara isarta shekaru nawa rabon data sa su a ido ace sati guda baza ta iya ƙyale mata ƴarta tayi mata ba?
Zee kuwa ji tayi kamar an daskarar da ita kalaman Hajiya Goggo ke sake dawo mata, gabanta ne ya shiga faɗuwa ba dai yanzun ma ƙarya Mummy ta dinga yi musu ba duk yawan shekarun nan? Ji tayi kanta yayi mata wani nauyi nan da nan tasa hannu ta riƙe kanta tana sauke ajiyar zuciya.

******
Kamalu ne ya kalli yaron da yake bawa ajiyar kaya yace “Yauwa fito min da kayan nan inga ko sun haɗu.” Nan yaron ya fito mishi da tulin atamfofin daya sace a shagon Badaru, dariya yasa sai kuma ya tamke fuska kamar wani mai aljanu yace “Matsalar babu lace bare shadda. Maida kayan yayi ya fito yana tunanin zuwa kasuwa ya ɗan yi samfe, sam bai kula da Salim dake tahowa ba da alama shago yaje, sai da Salim yazo daf dashi ya ganshi, kauda kai yayi yana neman wucewa sai ji yayi yace “Kai soko baka ganni bane?”
Salim ya kalleshi ya girgiza kai cike da takaici yana cigaba da tafiyarshi, dariya Kamalu yasa yace “Saurayi soko da alama an kasaka ne shi yasa tafiyar ma kake yinta ba cikin hayyacinka ba, to ya zaka yi? Manya sun ƙwace maka wacce kake so.”
Duk yanda Salim yaso ya kauda kai sai da yaji dariya ta kwace mishi yace “Ah kace kai da Roshni abu ya kankama?”
“Sosai, ba dai baƙin ciki kake yi ba?”
Ya dan girgiza kai yace “Ni? Ai ban isa ba, na bar muku ai ku manya, yaushe ne bikin?” Kamalu ya maka mishi harara yace “Malam ba zuwa zaka yi ba, don mu ba kowane soko muke gayyata ba, kaje can in abokinka zai yi aure kaje.”
Dariyarshi ya sake guntsewa yace “Tab gaskiya kam ai da alama abokina yafi guarantee gwara na tsaya a ɓangaren shi,” ya ƙarasa maganar yana tafiya, shi dai Kamalu ya bishi da harara yace “Wawa kawai.”

****

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*

*UMM ASGHAR*
DA
*AYUSHER MUHD*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA TAKWAS*

{78}

Tunda taji wannan maganar a bakin Ummi kanta ya ɗaure ta shiga tunani, kada dai ace duk tsawon shekarun nan Mummy ƙarya take yi musu take nuna dangin mahaifiyarsu na yin tattaki takanas suna zuwa har gidansu kawai don suci mutuncinta duk don tana riƙon su. Tukuna ma tsaya, wacce magana taji Ummi nayi akan duk shekara sai ta aika musu da kayan sallah abinda ita ko Kabir wani bai taɓa sani ba, tasan farkon zuwanta tayi magana makamancin haka amma bata gama fahimtar me take nufi ba, ya Mummy take yi da kayan da take aika musu ko kuwa dai ɗan aiken ne baya kaiwa sai ya dawo yace mata ya kai? Tana ganin hakan nema don babu ta yadda za'a yi Mummy ta ɓoye musu abu irin wannan, wani ɓari na zuciyarta taji yace Mummyn kuwa? Har kin manta da ɓoye muku da tayi akan Nabila ƴarta ce in banda Allah ya nufa sai kun ji Inna tayi suɓul da baka ta fallasa sirrin da suke ta ɓoyo kina tunanin da zaku sani ne? Girgiza kanta tayi tana kasa gasgata wai Mummy ce tayi musu duk waɗannan abubuwan tasa suka ƙullaci mahaifiyarsu da gangan alhakin tasan duk abubuwan da take zaunar dasu tana faɗa musu ƴan uwan Ummin sun yi mata duk ƙarya ne. Kai Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ita kuwa Mummy me yasa zata yi musu haka? Me zai sa ta hana ƴan uwan mahaifiyarsu kusantar inda suke? Laifin me suka yi mata da zata yi musu irin wannan cutarwa? Eh cutarwa mana tunda tasan duk abinda take faɗa musu ba gaskiya bane sai ma ƙara nesanta su da mahaifiyarsu da yake yi. Kawai sai taji hawaye yana zuba daga idanunta, tausayin Ummi ne taji ya kamata yadda suka rayu suna jin haushinta ashe babu laifinta ko ɗaya a cikin watsar dasu da suke zargin tayi.
Tana zaune a wurin tana saƙa da warwara taji wayarta tayi ƙara, da kamar ba zata ɗauka ba sai kuma tayi tunanin ko Baqeer ne ya ƙirata duk da basu wani daɗe da gama waya ba abinda yasa ta janyo wayar don ta amsa kenan sai taga ashe Daddy ne yake ƙiran ta. Sai da gabanta ya faɗi cikin ranta tace Allah dai yasa ba wani abu ne ya samu Mummy ba. A sanyaye ta amsa wayar don bata cikin yanayi na jin daɗi, bayan sun gama gaisawa da Daddy yace mata ta shirya ta dawo gida gobe hutun ya isa haka nan. Murya na rawa tace "Amma Daddy..." Katseta yayi yace "Kiyi abinda nace Zainab, lallai gobe na dawo gida na iske ki bana son zamanki a wannan garin ya isa haka nan." A sanyaye tace mishi "to," tun yanzu tana jin kewar Ummi na lulluɓeta, ga kuma Inaya da suka yi wani irin sabo da yarinyar tasan idan ta tafi ba ƙaramin kewarta zata yi ba.
Chapter 127 · 0% Book details