← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 168

Sashe 2

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan kallon shi likitan yayi yana tunanin ta yadda zai fara faɗa mishi halin da ɗan nashi yake ciki ganin yadda hankalinshi yake a tashe "A yanzu dai ba zance komai ba, sai abinda gwaje-gwajen da aka yi mishi suka nuna, mun dai yi ƙoƙarin tsayar da zubar jinin da yake yi sai dai muna buƙatar wanda za'a ƙara mishi ina fata kun zo da wanda zai bashi jinin, sannan akwai karaya a hannunshi na dama da ƙafarshi ta hagu".

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlif li khairan minha" Kawai Baba ke nanatawa. Cikin wata irin kasalalliyar murya irinta wanda abun duniya ya taru yayi wa yawa yace "Ko nawa jinin za'a iya ɗiba matukar jininmu ɗaya ai, Allah ya sauƙaƙa mishi ya tashi kafaɗunshi.” Ya ƙarasa maganar cikin murya mai karkarwa.
Dukkansu suka amsa da 'Ameen' banda kaninshi da yake tsaye a gefe sai faman cika yake yi yana batsewa shi a dole bai so zuwa asibitin ba ya biyoshi ne kawai dan mahaifiyarshi ta turo shi akan yazo yaga meke faruwa ya kai mata labari.
Jikin Baba a mugun sanyaye ya shiga cikin ɗakin, ja yayi ya tsaya yana jin kafafuwanshi nayi mishi nauyi ganin ɗan lelen ɗan nashi a kwance wanda duk wani mai imani in ya ganshi sai ya zubar mishi da ƙwalla saboda gaba ɗaya kamanninshi sun sauya don ba ƙaramin buguwa yayi ba, Bello da Salim a gefe suka tsaya kawai dukansu hawaye sukeyi shi da Salim, don abun akwai ban tausayi ace awa biyu baya kana cikin koshin lafiya yanzu banda numfashi ba abinda kakeyi, hancinsa ɗauke yake da na’urar taimakawa gun yin numfashi na oxygen, a hankali Baba ya ƙarasa wurin har a lokacin bai dawo hayacinsa ba ya kalli Bello cike da tausayin ɗan nashi yace “Garin yaya hakan ta kasance?” Jiki a sanyaye Bello yake faɗa mishi iya abinda ya sani sannan yaran daya mai motar a yanda ya musu kwatance suna zargin yaran gidan Alhaji Sunusi Karaye ne shine wanda ya bugeshi, da yadda yaja motarshi ya bar wurin ba tare da yabi takan Baqeer ɗin ba wanda hakan yasa basu gane ko tabbas shi ɗin bane.
Nan da nan Baba ya sake fusata, yana ji ranshi na sake soyuwa, tabbas zai je har gida ya samu ubanshi don ba zai yarda da ganganci a cutar mishi da yaro ba. Baba ne ya fito aka gwada jininshi ganin girma ya kamashi suka bukaci a gwada na kanin nashi, kallan Bashir yayi yace “Wuce a gwadaka.” Ji yayi kamar zai yi ihu haka ya wuce dan tabbas suna tsoron mahaifinsu sosai, dawowa yayi ɗakin yana jin kwalla na sake taso ma idanunsa, zubawa Baqeer ido yayi kaf cikin ƴaƴanshi yafi ji da Baqeer sannan ya kwallafa rai a kank Baqeer ɗin ne zai samu abinda shi bai samu ba.
Hannunsa yasa ya riƙo hannunshi yana sake bin fuskarshi da jikinshi da kallo zuciyarsa na sake karyewa, ya daɗe riƙe dashi kafin yace “Allah ka dubeni ka tashi kafaɗn yaran nan, Allah ka dube ni da idan rahama….” nurse ce ta shigo ta ƙara sa mishi wani jinin wanda aka ɗebe daga jikin Bashir.
Baba kallon Salim yayi shida Bello da suke tsaye carlo-carko a gefe yace “Please ku tafi mun gode da kulawa.”
Jiki a sanyaye suka juya, Baba ya saƙe riƙe Baqeer bayan fitarsu kawai hawaye ne yaji sun zubo mishi, tabbas in har wani abu ya samu Baqeer ba zai yafema Alhaji Sunusi Karaye ba, idanunshi ne suka sauka kan bandage ɗin da ke naɗe a wutsiyar hannunshi na dama, hankali a tashe ya ƙarasa ɓangaren daman ya ɗan ɗaga hannun, nan danan ya fito cikin sauri yana neman nurse ɗin data fito daga ɗakin, a gaban wani ɗakin ya hangota cikin sauri ya ƙarasa yace “Nurse me ya samu hannun daman yarona?”
Kallonshi tayi sannan tace “Muje na duba.” Tare suka shigo ta nufi ɓangaren dama tana dubawa ta kalleshi tace “Karaya ce a wurin…….”
“Karaya? Kinsan me yake yi da hanun da zaku ce karaya?”
Cike da rashin fahimta tace “An mai ɗori insha Allahu zai warke.”
Cike da faɗa yace “Kina tunanin dan kun mai ɗori hanunshi zai dawo yanda yake ne? In ya kasa amfani da hannun fa ko ya kasa yin aikin painting ɗin da ya saba? Gasar da zai shiga ta zane da za ayi a karshen watan nan fa?”
Bashir ne ya ƙara so da sauri dan ance ma ya kwanta ya huta yace a’a ahi gida zaije, nan ya wa nurse alamar ta tafi, tana fita ya zabgawa Bashir wani kallo yace “Baka da hankali ne? Ko ka ɗauka ban ganka bane?”
“Baba ita me nene laifinta? Kula dashi fa kawai suka yi? Sannan shi me yasa kowa na zaune agida amma shi yana yawo a titi da majalisa?”
“Kana sake magana zaka ga ɓacin raina, shashashan banza kawai.”
Bashir bakinshi yaja yayi shiru, Baba kallon hannun yayi yana ji ya zai yi idan yaron nan bai warke ba? Shikenan rayuwarshi ta shiga garari, duk wani buri nashi ya tarwatse.

Hmmmm...

#Baqeer
#Shalele
# RayuwadaKaddara
#Hawayena
#UMMASGHAR
#AYUSHERMUHD

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕
Duk guda ɗaya 1k

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya

*BAQEER*
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
            *DA*
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*
*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*
*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”
*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*
Mun gwada mun gani 💯
Mun gani mun shaida 💯
Anyi mun gani 💯
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
GYARAN MAIJEGO
MALLAKAR MIJI KO MATA
SUBULU DA SCRUB
MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
MAGANIN TSUMI
INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

08142800199
07068558096

*2*
Yau tunda ta tashi take jin jikinta babu daɗi gabaki ɗaya yayi mata nauyi ga wani irin ƙunci da ya lulluɓe kirjinta lokaci zuwa lokaci sai taji gabanta ya faɗi, komai take yi tana yin shi ne cikin rashin karsashi tunda tasan ba rashin lafiya take yi ba sai dai yanayin data samu kanta a ciki sam baya yi mata daɗi. A kasalance ta yunƙura daga inda take kwance a tsakar ɗakinta ta tashi, tsakar gidansu ta fito ta hau tattare wajen da suke yin girki don itace da girkin ranar, haka nan cikin dauriya ta samu ta haɗa wutar ta ɗora tukunya, aikin take yi salalaf-salalaf kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki don sam jikinta baya da wani ƙwari.

Tana lura da abokan zamanta da suke ƴan maganganu ƙasa-ƙasa a gefe da sun ganta sai suyi shiru suna zunɗenta da baki abinda yasa ta ƙara tunanin tabbas akwai abinda ya faru da suke ɓoye mata duk kuwa da ba yau ne karon farko da suka taɓa yi mata irin hakan ba sai dai na yau ɗin yayi tsanani ga kuma yanayin data tashi dashi tun safe yasa tayi tunanin tabbas ba lafiya ba, gashi ma maigidan tunda ya fita bai dawo ba haka nan Baqeer yau yayi nisan kiwo abinda ba halin shi ba ya fice waje yayi zamanshi in har ba wani muhimmin uzuri ne ya riƙe shi ba ba tare da ya leƙo yaga a halin da take ciki ba don duk inda ya tafi hankalinshi yana kanta sanin irin zaman da take yi a cikin gidansu yasa baya son yin nesa yana barin gidan don kaɗan da aikin mutanen gidan suyi mata wani abun na cutarwa ita kuma ba iya kare kanta take yi ba.

Har ta gama girkin ta raba kamar dai yadda suka saba Baqeer bai shigo gidan ba abinda ya ƙara ɗaga hankalinta don baya taɓa kaiwa magriba a waje duk inda yaje yana ƙoƙarin dawowa gida kafin ayi sallar magriba idan kuma ya zama lallai sai ya daɗe a wajen to tabbas zai kirata a waya ya faɗa mata. Sai da ta kawar da komai ta tsaftace wurin kafin ta tashi ta koma ɗakinta, wayarta ta ƙara ɗauka ta kira number Baqeer sai dai har yanzu a kashe ake ce mata, juya akalar kiran tayi zuwa ga wayar maigidan sai dai har ta ƙari ɓurarinta ta gama bai ɗauka ba, ƙara kiran wayar tayi amma har yanzu bai ɗaga ba. Tunani tayi watakila sallah yake yi don haka ta ajiye wayar da zummar ta sake kiranshi in anjima, tashi tayi ta fita don ta ɗauro alwalar ita ma tayi sallah sai dai abinda taji a tsakar gidan yasa ta sakin butar dake hannunta ta faɗi sauran ruwan dake cikin butar ya tsiyaye akan simintin tsakar gidan nasu.

Kamar wacce aka jeho sai ganinta suka yi a gabansu tana cewa "Me ya samu Baqeer ɗin kuke ɓoye mini? Ni dama nasan shirun nan nashi bana lafiya bane tabbas akwai abinda ya faru dashi, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta ƙare da ɗora hannayenta bibbiyu a kanta tana kuka.
"Ke dallah kada ki cikawa mutane kunne da kwakwazo a cikin gida, wani abu kika ji ance ya samu Baqeer ɗin da zaki cika mu da iface-ifacen kuka," Uwargidansu Jamila tayi maganar cikin yi mata tsawa.
Chapter 2 · 0% Book details