← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 168

Sashe 53

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kasa karɓar kuɗin daya miƙa mata tayi ta kuma kasa haƙuri sai da tace mishi "Saboda Allah haka zamu cigaba da rayuwa duk lokacin da Baffa yaso kawai sai dai mu ganshi tsaye akan mu ya shigo mana wuri babu tunanin a wane irin hali zai iya riskarmu kuma kai baza ka iya yi mishi magana ya daina ba, wannan wace irin rayuwa ce ace ni da gidana amma bani da wani sakewa a cikinshi, shikenan ni ban isa nayi wa mijina kwalliya ba saboda fargabar kada a shigo a tarar dani da shigar da bata dace ba. Gaskiya ni dai ya kamata a sake tsari ko dai ya daina shigo mini ciki ko kuma ka canja mini wurin zama amma ba zai yiwu ya dinga shigo mini ɗaki koyaushe ta raya mishi ba.”

Wata uwar harara ya watsa mata yace "Duk waɗannan maganganun a Baffan kike yi? Mahaifin nawa? Shine kike iya buɗe baki kina faɗar duk maganar da tazo bakinki a kanshi, to da zaki ce ya daina shigo miki gida nan ɗin gidanki ne? Nace gidanki ne da zaki ce ba zai shigo ba, ina ce dai gidan ɗanshi ne ai ko kuma yadda yake da iko dani haka yake da iko da duk wani abu dana mallaka don haka ke baki isa ki kafa mishi doka ba a cikin gidan nan, idan kina ganin zamanki dashi akwai matsala zaki iya fita ki bar mishi gidan tunda zaman bai zame miki dole ba shi kuwa baya da wani wurin zuwan idan ba nan gidan ba.” Ya watsar da kuɗin a tsakiyar parlourn yayi ficewarshi ya barta anan babu wani tausasawa bare lallashi sai kace ba ita aka yiwa laifi ba.
Sai da taji kanta ya fara ciwo saboda kukan da tayi ba kaɗan bane sannan ta bawa kanta haƙuri ta goge fuskarta ta tashi ta tattare kuɗin daya watsar mata a ƙasa ta adana sannan taje ta sakawa ƙofarta makulli duk dai da baya shigo mata wuri sai idan Baban Aareef na nan amma bata so ta sakankance tunda shi bai san ya kamata ba. Tattare kwanukan abincin da ta ɓata lokacin ta wajen shiryawa tayi ta mayar kitchen don gaba ɗaya sai taji abincin ma ya fita daga ranta halin ɓacin ran da ta samu kanta a ciki ya cika mata ciki. Haka nan ta yini sukuku zuciyarta duk babu daɗi komai take yi dauriya kawai take yi har lokacin ɗauko Aareef daga makaranta yayi ta fita ta ɗauko shi. A harabar gidan sai data tsaya ta ƙarewa motarta kallo wacce Baffan ne yasa aka karɓe daga hannunta kawai don ta fita tayi hidimar ɗan uwanta da ita gata nan yanzu an ajiye ta kawai tana busar iska ita kuma duk wani uzurinta sai dai ta fita ta hau napep duk da ma ba wani fita take yi ba kai Aareef makaranta da ɗauko shi ne kawai sai kuma uzurin zuwa gidansu idan ya kamata da take fita a motar taje ta dawo amma shine sai da yasa aka ƙwace kawai don dai ya nuna mata iyakarta bayan shi nashi ƴaƴan kowacce na warwasawa a gidan aurenta sai ita da yazo ya sakawa ido.

*****

Haka nan ta tashi yau sukuku da ita zuciyarta fal tunanin Baqeer da duk mafarkanta na yau shine a ciki, ta rasa me yasa ta damu dashi har haka alhalin tun asali ma ba wai suna wani shiri bane bare tace ko yarintarsu take tunowa yasa yanayin da yake ciki a yanzu ya tsaye mata a rai. Ta dai fi bayarwa tausayin halin daya samu kanshi a ciki ne yasa take yawan tunawa dashi ta damu da dukkanin wasu al'amuranshi da har idan bata je taga halin da yake ciki ba bata samun nutsuwa. Tunda ta tashi tana kwance akan gadon bata tashi tayi komai ba sai dai ta juya nan ta juya can sai Nabila ce kawai take kaiwa tana kawowa tana ƙoƙarin tsaftace gidan. Ɗakin Inna ta shigo ta watsa mata harara tace "To sannu ƴar mai da ba'a koya mata komai ba sai sakalci da lalacin tsiya, kina nufin haka zaki yi ta kwanciya ba zaki tashi ki kamawa Nabila komai ba ita kaɗai zaki bari da aiki kina naɗe akan gado sai idan ta gama abinci kice zaki buɗe ciki kici. Ke dai wallahi baki ji daɗin halinki ba kuma ni dai idan kin san ba za'a amfana da zamanki ba gara tun wuri ki tattara ki koma gidanku inda ba'a sakaki ba'a hanaki amma ba zai yiwu kizo sai dai ki naɗe akan gado ba kice ba zaki yi aiki ba ah to.”

Tashi zaune tayi tace "Haba don Allah Inna daga tashi na bacci kawai zaki rufeni da faɗan ki na fama da baya ƙarewa tun ban gama wartsakewa ba, shi yasa wallahi ban cika son zuwa wurinki ba don nasan takura mini kawai zaki yi da yawan faɗa kamar irin kina jin haushi na ɗinnan.”

"Ungo naki nan ƴar ƙaniya mai bakin tsanya, wacce baka kasheta a zance" tayi mata daƙuwa da duka hannayenta bibbiyu. "Shikenan ke ba za'a yi miki faɗa ki saurara ba sai kin mayar da amsa saboda a gidanku ba'a yi miki tarbiyyar sanin darajar manya ba, to ni gidannan ba'a yi mini iya shega in ƙyale, idan kinga ba zaki iya zama ba ƙofa a buɗe take ki tattara ya naki ya naki ki bar mini gidana dama ai bani na gaiyaceki ba". Tagumi kawai Zeey tayi ta zubawa Inna ido tana ta faman zazzaga mata masifa sai dai sam yanayin da take samun kanta a ciki a ƴan kwanakin nan yasa bata ji zata iya tanka mata ba don haka har tayi ta gama bata ƙara ce mata komai ba, sai bayan data fita tayi mata gwalo tana cewa "Jarababbiyar tsohuwa kawai, haka kurum daga tashi na zata zo ta cika mini kunne da masifa kamar ance mata ina da energy ɗin ɗaukar jidalinta yanzu da sassafen nan”.

*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.

*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

NORMAL GROUP 500
VIP 1000

ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730

Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336

#Baqeer🦼
#Zeey
#RayuwadaKaddara
#Hawayena
#Samudarashi
#UmmuAsgar
#Ayushermuhd

*BAQEER*🦼
     *NA*
*AYUSHER MUHD*
         *DA*
*UMM ASGHAR*

*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA UKU*

{33}
Chapter 53 · 0% Book details