← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 168

Sashe 88

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yaye bargon yai ya ganshi daga shi sai gajeran wando, kanshi ne yai wani irin sarawa ya sa hannu ya rike kan yana sake tariyo abinda ya faru, dawowarshi kenan daga yawonshi na abokai ya shiga ɗakin shi, kayan jikinshi ya fara cirewa dan bacci yakeji ko ganin su Mumy ba baisa ranyi ba dan kuwa yasan sun kwanta, ya cire kaya ya rage daga shi sai gajeran wando zai sa kayan bacci ta turo ƙofar, kallanta yai nan danan hankalinshi ya tashi, da sauri yasa hannu ya rufe saman kirjinsa yana cewa "Dan Allah fita, akan me zaki ɗinga shigowa ɗakin mutane ba tare da kin kwankwasa ba?" Mai makon tai abinda ya sakata sai ƙara takowa datai zuwa inda yake, nunata yai da yatsa fuskarsa a ɗaure yace "Wai ba magana nake miki ba? Karki kuskura ki ƙara so," nan ma bata kulashi ba sai ƙara takowa da take, tana isowa inda take ta rungumeshi, yawun bakinsa ya hadiya ya fara ƙoƙarin tureta, sake kankameshi tai tace "KB plz ka bari ba zina zamuyi ba, balle kace zunubi muke ɗauka." Da mamaki ya kalleta yace "Wai Nabila kinsan me muke yi kuwa? Me zai faru in wani ya shigo ya ganmu a haka? Dan Allah......" kiss ɗin data fara mai ne yasashi kasa cewa komai, tun yana neman janyeta tana rikoshi harya kasa, nan ya shiga maida mata martani, kan gado ya jata ya cigaba da sumbatarta, saman wuyanta ya gangara gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, Nabila kuwa gani take hakan shine daidai dan wannan ne kadai abinda zai hana Mumy rabata da Kabir dan indai aka hanata auran Kabir to fa har abada bazatai aure ba sai dai ta karashi rayuwarta haka, ko duniya zasu zageta in dai akanshi ne to fa bata damu ba. Kabir cak taji ya tsaya sanda ya fara zuge zip ɗin bayanta, hakan yasa ya saketa sai kuma ya kwanta rigingine yasa hannu ya shafi fuskarsa yace “bazan iya ba, am sorry.” Hawaye ne ya zubo saman kuncinta ta kankameshi tace “Naji amma dan Allah ka soni.” Hannunta yaje janyewa ta sake kankameshi wanda hakan yasa ya kyaleta, yana ji tana hawaye amma ya kasa hanata, a haka bacci ya ɗauke su wanda bai farka ba sai yanzu.
Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ya sauke jin komai ya dawo cikin kanshi, Alhamdulila da bai tafka kuskure ba dole yasan abinyi ya kuma kare kanshi daga aikata zina, haryau yaran da ya buge a mota yana zuwa mai cikin rai ya kuma san hakki na nan na binshi dan haka bazai bari ya sake aikata wani babban aikin dazai ƙara mikashi wuta ba. Yanda taja bargo ne yasa shi tsorata ya kalleta hankali a tashe yace “Menene kuma?”
Kuka ta fashe dashi tana cewa “Kabir sai fa dana ce maka kar mu gangara,” ta ƙarasa maganar tana kuka, mamaki ne ya rufeshi yace “To ai bamu gangara ba.” Ta girgiza kai tana sake shashekar kuka tace “Da alama ba’a hayyacinka kake ba nikam na shiga uku na, wallahi ban ɗauka zakamin karfi ba.” Jiyai kanshi ya ɗaure nan ciwon kanshi ya ƙara tsanan ta yace “Me kike san cewa? Bayan na tuna komai kuma ba abinda ya faru?” Ta sake sa kuka tace “Iya abinda ka tuna dai kenan amma bayan na kwanta bacci kawai naji ka yayemin bargo ka hau cire mun kaya kamin ta ƙarfi……….” Ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani irin kuka, hannu yasa ya toshe mata baki da sauri yace “Bangane nasa miki ƙarfi ba bayan ko taɓa ki banba. Yaye zanin kaɗan tai sai gata ba pant, sai jini a matse-matsin kafafunta, idanu ya zaro jikinshi ne ya hau rawa, yama kasa gane meke faruwa dan shi dai a iya saninsa bai ko ta ɓata ba, to menene wannan? Hawaye ta share tace “Shikenan ka cuceni, shiyasa nake ta cema na zina ba, dan kaga ina sanka shiyasa kai min ƙarfi, na shiga uku nikam shikenan rayuwata tazo ƙarshe.” Kabir gaba ɗaya ya kasa tunani, jikinshi ne kawai yake rawa dan hanayensa ma sai rikesu yai saboda rawar da sukeyi, da sauri ya mike ya nufi hanyar toilet, cikin sauri tace “Ka ƙira min Mumy tsoro nakeji….” Tai maganar cikin rawar murya, dawowa yai da sauri yace “Na kira miki Mumy kamar ya?” Hannunshi ta kamo tace “Bazan iya tashi ba, nan dina zugi yakeyi.” Tai maganar tana nuna gun da hannu, gaba ɗaya zufa ke keto mai wannan masifa da bala’i da me yai kama yaushe ya kusanceta? Shi ba shayeshaye ba taya zaiyi abu baisan yayi ba? Shikenan rayuwarshi ta kare ace kamar shi fyade yakewa mata? Matqn mq kanwar Mumy? Inalilahi, kalaman Nabeela ne suka dakatar da tunaninsa datace “Kabir ka ketan haddi ka maidani budurbazar shikenan gwara na mutu na huta.” Kallanta yai yace “Nidai kome zai faru karki sanar da kowa abinda ya faru, bansan sanda nai ba haryanzu na kasa gasgata zuciyata, taya zanyi abu bansani ba?”
“Hmmm! Dama ance haka maza suke sai suyi abu su maidashi tsautsayi ko suce basu san me hakan yake nufi ba, bari na ƙira Mumy ta maidani gun Inna,” tai maganar tana ɗaukan wayarta, da sauri ya amshe wayar yace “Ki bari mu samo mafita yanzu ki tashi ki wanke jiki ki fita zan fitar da bedsheet ɗin.” Man ta fara ƙoƙarin mikewa ya taimaka mata ta shiga banɗaki shi kuma ya fito da bedsheet kamar munafiki yasa a bayan motarshi sannan ya dawo, yai sa’a daya dawo bata ɗakin, kasa bacci yai kawai ya zauna ya dafa saman goshinsa, meke faruwa?

*******
Maryam ce ta kalli Baban Areef idanunta sun ciciko tace “Yanzu haka zamu cigaba da rayuwa shikenan mu bamuda sirrin kanmu? Ni kenan komai zakamin sai abinda aka tsara ma?” Fuska ya tamke sosai yace “Kiyi hakuri kyaje nan gaba.” Idanuwanta ne suka ciciko da kwalla tace “Wannan wani irin aurene ace sam ban da ikon kaina bare insa ran samun ƴanci na? Ace kullum sai yanda akai dani, komai muka tsara sai ka kwashe ka sanar mai? Bamu isa muyi sirri ba?” Hannu ya ɗaga mata alamar ta dakata sannan yace “Kul wallahi na faɗa miki duk wani abu daya shafi Abbana dole ki darajashi kin kuma san sauran in baki bi ba.” Yana kai nan ya mike ya fita, hawayenta ta share ya dade yana cewa zata cigaba da karatu yana ki amma yanzu da ya amince ta sa ran amincewar ta gaske ne saboda har takardunta ya amsa kawai sai gashi an dawo mata dasu wai Baba yace kula da yara zatai ko karatu?
Chapter 88 · 0% Book details