← Book details Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 168

Sashe 134

Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shiga ɗakin ya ganta a kwance tana danne-danne a waya, ita ko damunta ƙazantar data haɗawa ɗakin bata yi, haushi ne yaji ya ƙara rufe shi, ayi mace bata san komai ba sai baƙar ƙazanta tun yanzu ma kenan da take ita kaɗai bata iya tashi ta tsaftace muhallinta ba ina ga idan ta fara tara yara kuma yana ganin wannan lokacin sai dai ya haƙura da zama gidan don yasan iska ba zata shaƙu a cikinshi ba. A fusace yace “Ya kuma isheki haka nan Asiya, na lallaɓaki iya lallaɓawa amma sam ba kya gani. To wallahi bazan ɗauka ba kuma ki fito mini da makullin motata tunda bada ubanki muka haɗa kuɗi muka saya ba." A fusacen itama ta tashi don dama irin haka take jira ranar da zai buɗe baki yayi magana ita kuma ta yagalgala shi son ranta. "Bello ubana kake zagi?"  "An zagi uban naki idan kin ji haushi ki fito min da makullin motata, haba ya daga abun arziƙi yana nema ya zama na tsiya. Tunda na dawo baki barni na sha ruwa ya tsirga mini ba, ance miki nima daɗin dawowar nake ji da zaki sakani a gaba da masifa da bala'i kawai don ban fita dake ba ko da kin san ko hanyar airport ne banda Allah ya haɗaki dani da zaki bi ki isheni da masifa saboda baki fita ƙasar waje ba kamar yadda kika ci buri, ni da naga samu naga rashi kuma fa nace me?"
Murguɗa baki tayi tace "Wannan kuma damuwarka ce ni dai ai alƙawari kayi min kuma baka cika ba don haka ka dinga ganin tashin hankali kenan idan har baka ciki ba, haka kurum bayan duk nabi ƙawaye da ƴan uwana na gama yi musu kurin ba'a ƙasar zamu zauna ba sai ka dawo kace wani wai kai ma koroka aka yi?”
Ƙwafa yayi yace "Au haka ma kika ce? Shikenan mu zuba ni dake shege ka fasa kuma wallahi ki fito min da makullin motata kin ji na faɗa miki." Wata uwar harara ta danƙara mishi ta saki tsaki tana girgiza jiki tace "Na ƙarfi ne idan kana dashi ka ƙwata," tayi shigewarta banɗaki ta banko ƙofar ta rufe.
Duk bala'in da Bello yake ji sai da ya kasa magana don kullum mamakin rashin arziƙi irin na Asiya take yi. Juyawa yayi ya fita daga ɗakin yana jin wani irin dana sani yana kamashi, shi wai waya aikeshi ne ma gashi yanzu duk yabi ya cakalkala al'amuranshi da hannunshi. Shi sai yanzu ma ya gane ashe ba wani so yake yiwa Asiyar ba kawai don tana tare da Baqeer ne yasa yake ganin kamar shima sonta yake yi ashe ba haka bane burinshi na son mallakar duk wani abu daya kasance na Baqeer ne yasa yake tunanin sonta yake.

*****
Baqeer kuwa tunda ya karanta saƙon da Zeey ta turo mishi yake saƙa da warwara, ta ina ta yaya zai fara tunkarar Alhaji Suleiman a matsayin manemin ƴarshi? Shi yasan ko yana da lafiya ko ace ya cigaba da harkarshi ta painting Suleiman Ƙaraye ba zai bashi ƴarshi ba bare kuma da yake gurgu a yanzu wanda ya damu wata tawaya a jikinshi ga sana'ar ma yanzu yake ƙoƙarin ginata yasan babu ta inda zai fara tunkararshi a matsayin wanda yake son Zainab. Da yaga yawan tunanin da yake yi na neman saka mishi ciwon kai sai ya ɗauki waya ya ƙira Salim, tana fara ringing Salim ɗin ya ɗauka. Baqeer na jin muryarshi ya sauke wata ajiyar zuciya yace "Zainab na neman saka min ciwon kai Salim, wai kasan bayan dawowarmu saƙo ta turo mini akan naje naga mahaifinta gobe."
"Daidai kenan, idan har da gaske kuke son juna dama ai kasan dole sai iyaye sun shigo maganar." A ɗan tsawace yace "Ka kuwa ji abinda nace Salim?"
Yace "Ƙwarai kuwa naji ka kuma san hakan shine daidai kaje ka samu mahifinta kuyi magana shine zai san da gaske kake kana son ya baka auren ƴarshi." Wani zazzafan huci ya furzar yace "Wai ka manta waye mahaifin nata hala, Alhaji Suleiman Ƙaraye ne fa mutumin da kasan ko ina da lafiyar ƙafafu ba zai taɓa ɗaukar ƴarshi ya bani ba bare yaga naje mishi akan wheelchair."
"Why do you lack confidence in your self Baqeer? Wannan abun da kake yi is an act of cowardice, idan har da gaske kake son Zainab bai kamata kaji tsoron haɗuwa da mahaifinta ba tunda kasan in dai har auren nata zaka yi dole ne ku haɗu."
"Tabbas ina sonta sai dai wannan ba dalili bane da zai sa na kai kaina inda za'a wulaƙantani ba," yayi maganar yana jin wani ƙunci yana ƙara lulluɓeshi. Me yasa Zainab ta ɓoye mishi kanta gashi nan yanzu abinda ta janyo musu sun faɗa halin da ba lallai su iya fita ba. Nisawa Salim yayi yace "Idan har zaka ji shawarata ka shirya kaje wajen mahaifin nata baka san me zai faru ba, sai kaga Allah ya juya al'amarin yazo da sauƙi ba kamar yadda kai kake tsammani ba. Ina ganin hakan kawai zaka yi ka nunawa Zainab tabbas kana ƙaunarta kana kuma tare da ita a cikin kowane hali."
Ɗan shiru yayi yana jinjina abinda Salim ɗin ya faɗa kafin yace "Shikenan Salim zan yi amfani da shawararka amma dai kasan bani kaɗai zan je ba ko? Sai kazo ka ɗaukeni mu tafi Allah ya tabbatar mana da alkhairi amma ni dai ina jinjina haɗuwar mu da Alhaji Suleiman Ƙaraye nasan zai yi wahala ya karɓe mu a matsayin manema auren ƴarshi."
Murmushi Salim yayi yace "Ko kai fa? You have to be brave idan har da gaske kake son Zainab dole ka fuskanci dukkanin wasu ƙalubale da zasu iya kawo muku cikas wajen cimma burinku na zama mallakin juna. Goben zan zo muje In Sha Allah, kamar ƙarfe nawa zamu je?"
"Ban sani ba gaskiya amma dai zan tambayeta naji sai na sanar maka." Da haka suka yi sallama da Salim yana fatan Allah yasa Suleiman Ƙaraye yayi musu bazata ya amince mishi ba tre da wata tangarɗa ba, sai kuma yayi wata dariya ta takaici don yasan abu ne mai wahala hakan ta kasance sai dai bawa baya cire da abinda yake so yana fatan kada su samu ko wacce irin tangarɗa daga wajen shi.
Wayarshi ya ɗauka ya turawa Zainab message. _What time Daddyn yake son ganin mu?_
Ajiye wayar yayi ya kwanta yayi rigingine yana kallon ceiling, gaba ɗaya zuciyarshi bata yi mishi daɗi, shi yasan mawuyacin abu ne taraiyarshi da Zainab ta cigaba don shi yasan waye mahaifinta ya kuma san irin burin da yaci akan ƴarshi, shi yasan ba irin shi ne mijin da yake yi mata fata ba to amma ya zai yi da soyayyarta da tayi mishi wani irin kamu, soyayyar da tasa yake jin ashe da can ba son Asiya yake yi ba don bai taɓa jin yadda yake ji akan Zainab akanta ba. Zumbur yayi ya tashi zaune jin ƙarar shigowar text a wayarshi. Ɗaukar wayar yayi ya duba. _Ƙarfe huɗu zuwa da rabi haka_ kawai ta rubuto. Ajiye wayar yayi haka nan yake jin gabanshi yana faɗuwa, sai yake jin kamar ranar rabuwarshi da Zainab ce tazo don shi dai ya kasa yardar wa ranshi wai Suleiman Ƙaraye zai bashi auren ƴarshi ko ace yana da lafiya kuwa abu ne mai matuƙar wahala bare yadda kowa yasan ƴar tsamar dake tsakaninsu shi da Badaru.

*****
Umma na zaune a ƙofar ɗakinta tana gyaran kayan miyar da take so ta yiwa Dada da Baqeer miya Badaru ya shigo. Dama sallama ba al'adar shi bace don yace gidanshi ne daya gina da gumin shi babu sisin kwabon uban kowa don haka bai ga dalilin da zai sa don zai shiga ace sai yayi sallama ba. Ko ɗaga bata yi ta kalleshi ba tayi mishi sannu da zuwa tana cigaba da aikinta. Kallonta yayi sheƙeƙe ya taɓe baki yans lura da yadda ta bawa aikin da take yi muhimmanci kamar bata san da tsayuwarshi a wurin ba. "Wato Fatima ba zaki fito min da kuɗin filina ba ko?"
Ɗagowa tayi ta kalleshi sai kuma ta sunkuye ta cigaba da cire hancin tattasai cikin sanyin muryarta tace "Ai na faɗa maka abinda aka yi da kuɗin filin tuntuni bana jin za'a samu saura." Wani irin takaici ne ya lulluɓeshi, shi ya rasa ne ya yiwa Fatima da tayi mishi irin wannan muguntar ta sace mishi takardar fili ta kaiwa nakasashen ɗanta idan ma shi ɗin ta kaiwa da gaske don ga labarin da Bashir ya bashi bai kamata ace zai hau adaidaita ba idan shi ta kaiwa takardar filin ai sai dai ya sayi mota ana jan shi.
"Ke dai wallahi Fatima muguwa ce azzaluma, sai Allah ya bi min hakkina a kanki wallahi," ya ƙarashe maganar kamar zai fashe da kuka, yana jin baƙin cikin filin nan da Fatima ta rabashi dashi. Ita kuwa ko kallonshi bata kuma yi ba haka ya gaji da tsayuwa ya shige ɗaki yana kumfar bakin kotu ce zata rabashi da Fatima idan har bata dawo mishi da kuɗaɗen filin ba tunda dai yasan an sayar gashi an faɗa mishi har an fara gini a wurin. Babbar damuwarshi jarin shi da yayi ƙasa bai san ta inda zai farfaɗo dashi ba, dama akan filin ya dogara to ashe waccan muguwar matar ta rabashi dashi yana zaune da baki buɗe shine bai sani ba.
Chapter 134 · 0% Book details