Sashe 72
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ameen Ya Rabb, nagode Salim. Ka tabbata aminin ƙwarai, kai kaɗai ne baka gujeni ba tun bayan da iftila'in nan ya afko mini, da yawa daga cikin abokanmu ma ko dubani basu zo sun yi ba bare su tausayawa halin da nake ciki, kai kaɗai ne ka tsaya tare dani ka kula dani da jikinka da aljihunka, nagode ƙwarai Allah yayi maka mafificin sakamako da aljannarshi da yayi tanadinta wa masu yin abota domin shi" haka nan yaji ƙwalla na taruwa a idanunshi, ƙoƙari yayi ya mayar da ita bai barta ta zuba ba. Shi kanshi Salim sai da jikinshi yayi sanyi da abunda Baqeer ɗin yace don shi shaida ne yadda abokansu duk suka juya mishi baya shi kuwa Bello ma sai ya haɗa da cin amana mafi muni bayan duk a cikinsu tasu tafi zuwa ɗaya shi da Baqeer saboda ra'ayinsu da yazo ɗaya na yin zane. Mai adaidata sahu Salim ya tarar musu ya faɗa mishi inda zai kai su, da taimakon mai adaidaitan suka saka Baqeer a ciki ya zauna sannan Salim ya naɗe wheelchair ɗin ya shigar da ita shima ya shiga ciki ya zauna. Suna tafe suna ƴan hirarrakinsu har suka ƙarasa wani store anan kan titin hotoro. Salim na tura wheelchair ɗin suka shiga cikin kantin bayan sun biya mai adaidata kuɗin shi. Kayan amfanin shi ya saya irinsu sabulun wanka, toothpaste da brush, man shafawa, hair cream sannan suka ƙarasa ɓangaren turare. Kallon wajen yayi idanunshi suka kai kan turaren intense oud (Gucci) da yake amfani dashi tunda ya fara riƙe kuɗi na ƙashin kanshi sai dai yanzu yasan bai isa ya iya saye ba tukuna, ɗauke kanshi yayi ya cigaba da duba turarukan mata yana so ya sayawa Zainab. Yana son saya mata turare mai tsada sai dai kuma yana jinjina kuɗaɗen su gashi shi ba wani kuɗi bane dashi masu yawa, dubu ɗarin da akatura mishi ce a account jiya, haƙuri yayi ya ɗaukar mata turaren da bai haura dubu ashirin ba ya nemi wanda bai gaza dubu biyar ba ya ɗaukarwa kanshi. Yanzu ba lokacin sayen abubuwa masu tsada bane lokaci ne da zai yi ƙoƙari ya gina kanshi in yaso komai yake son yi yayi daga baya. Kallon Salim yayi yace shima ya ɗauki turaren sai yace a'a ya saya mishi wata rana amma ba yau ba. Harara ya watsa mishi sai ya ɗaukar mishi irin wanda ya ɗauka yace "Gashinan sai muyi anko.” Dariya kawai Salim yayi sai dai bai ce mishi komai ba, har sun juya zasu bar wurin idanunshi suka sauka akan wata rose flower me kyau an sakata a cikin wata garai-garai ɗin roba. Tsayawa yayi yana kallon rose ɗin yana tunanin ya dace ya haɗa mata da ita to show his appreciation. Salim dai na kallonshi bai ce mishi komai ba sai da yaga baya da niyyar barin wurin yace "Malam idan saya zaka yi ai gara ka ɗauka mu tafi mu bar ɓata lokaci rana tana ƙara yi idan kuma ba saya zaka yi ba to mu tafi don ina so naje kasuwa bayan na mayar da kai gida.”
Kallon Salim yayi ya haɗe fuska don baya so ya kawo wani abin a ranshi sannan ya ɗauko flower ya saka a cikin basket ɗin suka bar wurin. Dariya ce ma taso kama Salim ganin yadda ya ɓata rai wai shi a dole kada ya kawo mishi wasa sai kace idan yayi niyyar tsokanarshi shan ƙamshin shi zai hanashi ne, ai ba wannan ne lokacin tsokanarshi ba don yasan yanzu yana buɗe baki yace zai yi magana fasa sayen flower ɗin zai yi shi kuma ba zai so ya fasa abinda yayi niyya saboda shi ba, shi yasa yayi shiru ya ƙyaleshi. Haka suka je wajen cashier aka buga musu kuɗi ya fito da atm card ya biya. Sai da suka fita har sun hau adaidaitan da zai mayar dasu gida sannan ya cewa Salim "Dan Allah idan ka samu lokaci kazo ka rakani banki nayi updating account ɗina kasan tunda na rasa wayata ban yi welcome back na layina ba don haka bana ganin alerts idan anyi min.”
“To sai nazo wajen jibi In Sha Allah" sai kuma ya kalleshi yana ƴar dariya ƙasa-ƙasa yace "Shi turaren da rise flower wa ni aka sayawa?" Harararshi yayi ya ɗauke kai bai amsa mishi ba, shi dama yasan ba ƙyaleshi Salim zai yi ba sai yayi ta tsokanarshi akan wannan flower ɗin da yaga ya saya.
“Ah to nidai na mata na gani kuma ni namiji ne amma ba matsala zan iya amsa na kaiwa crush dina.”
Wani kallo Baqeer yamai yace “Hala Habi ce crush ɗin?”
Salim yai gyaran murya yace “Nidai ban ce ba, kaine ma za’a tambaya tunda kai ka siya.”
Gefe ya kalla baice komai ba dan dama sun saba haka da Salim indai cacar baki da zolaya ne.
*****
Tunda ta samu Umma ta bata kuɗi ta sayi injin markaɗe shikenan aka daina jin kansu da maigidanta don yanzu ta daina damunshi da bani-bani akan abinda zasu ci. Har wani ƴar daɗi suke yi bare idan yazo yaga ta shirya mishi abincin da bai san yadda tayi ta samu ta girka ba, haka zai zauna yaci yana washe baki yayi tayi mata kame-kamen zancen abinda bai shafeta ba. A yanzu bata da wata damuwa don tana samu tayi duk wasu ƴan hidingimunta a cikin ɗan abinda take samu duk da har yanzu cinikin bai zauna ba soaai saboda ba kowa yasan tana markaɗen ba duk da lokacin data fara ta tura ƴan biyu makwabtansu na kurkusa duk sun sanar cewa ta fara yin markaɗw na kuɗi idan suna buƙata, to amma ko a haka babu abinda zata ce sai gidiyar Allah domin kuwa sun daina zama da yunwa tunda duk tsiya bata rasa abinda zata girka musu abincin da zasu ci kullum har ma ta samu na sayen sabulun wanka da omon wanki. Wai kuma sai da kishiyarta taga ta samu canjin rayuwa tunda ta fara markaɗen sai ta tsiro da tsurfar wai ƙarar injin tana damunsu tana hanasu walwala a cikin gida markaɗen da ba kowane lokaci take yi ba amma shine ganin tana samun na rufin asiri take neman rabata dashi, sosai suka yi rigima har sai da maigidan ya saka baki sannan ta haƙura ta ƙyaleta ta cigaba da yi anan soron gidan nasu don da cewa tayi sai dai ta fitar dashi ƙofar gida don haka nan ba za'a kashe musu kunne da ƙarar inji ba.
*****
Kabir bai shigo gida ba sai wajen ƙarfe sha ɗaya na dare bayan kowa ya tafi ya kwanta, tun Daddy na tambayar ina yake Mummy na kakkarewa har ya haƙura yayi ahiru ya daina tambayar. Cikin sanɗa yazo zai shige ɗakinshi don baya so aji motsin shigowarshi har Daddyn da baya son yasan bai yini a gida ba ya fito ya ganshi a yanayin da yake ciki. Ya kai tsakiyar parlourn kenan yaji ansa hannu an riƙo shi, sai da gabanshi ya faɗi don baya son ganin kowa a wannan lokacin. Ƴar nutsuwa ya samu da yaji kaurin hannun alamun na mace ne. Fitilar wayarshi ya kunna yana fatan ace ba waccan ƴar sa idon bace ta zauna zaman jiranshi don yasan idan har ita ce to asirinshi ya gama tonuwa. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke da yaga Nabila a zaune tana yi mishi wani narkakken kallo. Ƙwace hannunshi yayi ya haɗe rai don kada ma tace zata kawo mishi raini yace mata "Me kike yi har yanzu baki je kin kwanta ba?"
Narkar da fuskarta tayi tace "Taya zan iya bacci alhalin baka dawo gida ba har wannan lokacin, wai shin ina kaje nema Kabir tun rana fa Daddy yake tambayarka.”Tsaki yayi yace "Koma ina ne ina ruwanki da inda naje, kin san sarai dai bana son yawan sa ido.” Yayi wucewarshi ya barta a wurin, yasan dai ba zata faɗawa kowa ba amma ya lura sai ya taka mata burki don yaga alama nema take yi ta takura rayuwarshi akan abinda daga shi har ita sun san ba mai yiwuwa bane. Sai da ya shige ɗakinshi ya mayar da ƙofar ya rufe sannan ta tashi ta bar wurin zuwa ɗakinta tana share hawaye.
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA BIYAR*
{45}