Sashe 94
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*****
Wannan shine karo na ba adadi da Baqeer ya ɗau wayarsa ya duba sannan ya ajiye, ganin da gaske ya kasa bacci gashi har karfe sha biyu da rabi yasa kawai ya danna ƙiran Zee, ya gashi da duba sunanta yana rufewa, kallan wayar yai ganin da gaske katsewa zatai ba ta ɗauka ba? Ji yai an ɗauka hakan yasa ya kara wayar a kunensa, ga mamakinsa kin magana tai, shima yai ɗan shiru ganin bazatai magana ba yasa yace "Ɗazu naga yanayinki ya canza wani abin ne?"
Cike da mamakin kalamansa tace "Nima dazu naga yanayinka ya canza wani abin ne?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ni ba komai."
"Nima!" Da sauri yace "No ke akwai abinda ya sameki."
Shiru taɗan yi kaɗan kafin tace "Ya akai ka san abinda ya dameni? Bayan ba damuwa kai da yanayin da zan shiga ba?" Kalamanta ne yaji sun dakeshi, me take nufi bayan shi kanshi tsoron matsayin data samu a zuciyarshi yake?
"Nasan kinje gun saurayinki so bansan ko abinda yafaru tsakaninku bane ya saki ɓacin rai." Sam baisan sanda kalmar saurayin ta fito daga bakinsa ba, kamar tace mai ba saurayinta bane kawai sai taji batasan faɗa tunda itama batasan menene matsayinta a gunshi ba hakan yasa tace "Wai J? Ni ko kaɗan ba shi ya ɓatan rai ba, ni bana ji ma ya taɓa min abinda zai sani ɓacin rai kawai bana san naga inama magana kana shareni ne, ɗazu abinda kamin ka kyauta? Kamar wanda mukai faɗa ko bamu san juna ba?"
Kenan saboda shi ne? Tambayar datazo mai kenan hakan yasa yace "Kenan akai na ne?" Cike da shagwaba tace "Nifa banasan naga ina magana ana disgani gashi kuma a gaban Tanimu ka dinga wulakantani kallo na ma kin yi kai." Shiru yai saboda jin gaɓobin jikinshi sunyi laushi jin yanda take magana kamar mai shirin kuka.
Sannan ta cigaba "Allah a faɗan me nai ko aban hakuri."
Shidai bazai iya faɗar kishi yake ba, dan tabbas yanzu kam ya shaida kishi ne, kuma hakurin ma bai san badawa tunda yana gani ai an mai ba daidai bane yai, hakan yasa yace "Me kikeyi yanzu?" Tace "A kwance nake." Yace "Hmm akwai pen kusa dake?" Ɗan mikewa tai ta kulla side bed lamp dake gefen gado ta ɗauko da paper tana cewa "Zane za'a koyamin?"
Yace "A'a rubutu." Da mamaki ta maimaita kalmar tana cewa "To na shirya."
"Yauwa rubuta A" ta rubuta yace "Rubuta S," nan ma ta rubuta yace "Sai ki rubuta F" ta rubuta tana cewa "Sai me?" Yace "Shikenan" kallan abin tak tace "Asf? Me kenan?" Ka faɗa ya ɗaga yace "Ki bincika, ni zan kwanta." Kallan takardar ta sake yi tace "Hakurin fa Allah ba'a bani ba."
"In kin san amsar ki dawo ki sanar dani zan baki."
"To naji, amma Ya Baqeer please karka sake disgani cikin mutane kaki kulani."
"Kema ki daina......." Sai kuma yai shiru ya kashe wayar da sauri, Baqeer me kake tunani? Badai kana gurgu kake neman jawo soyayyar wace ko a haka ka ganta kasan ƴar wani bace?
Zee kuwa ta dade tana kallan takardar kafin ta kwanta, zuciyarta fess kamar ba itace sukai faɗa da Baqeer ba.
*****
Kwance take a ɗaki Zeey ta shigo tace "Aunty Nabs tashi ki fadamin menene ma'anar kalmar nan?" Kasa magana tai sai sake lumshe ido take, Zeey tace "Nikam kalau kike?"
Nabila ta sauke huci tace "Banajin daɗi Zeey ki duba google mana." Cike da kulawa tace "Me ya sameki?"
Kai ya girgiza tare da cewa "Ban sani ba haka nan nake jina ba da ɗi." Da sauri Zeey ta kamo hanunta tace "Kila ma yunwa kike ji, muje Mumy na jiran mu muyi breakfast." Kamar bazata mike ba sai kuma ta tashi ta suka fito, zama tai Mumy ko kallanta batai ba sai Dady dake tsokanarta wai ina ta shige kwana biyu? Murmushi kawai tai suka fara cin abinci, Dady sai yaban Nabila yake Zeey kam baki ta taɓe tace "Bakomai Dady tunda nasan gun Mumy I'm the best."
"Oho dai kuyi ta yi nidai na fadawa iyayen Junaid suzo muyi magana." Tunda ga haka bata sake magana ba harya gama ya tashi yai ɗaki, Zeey ta bishi akan zata mai magana.
Mumy ce ta kalli Nabila da ta kasa cin abinci sai wani jujuyashi take tace "Wai meke damunki?"
Ta buɗe baki zatai magana sai ta fara yunkurin amai, cike da mamaki Mumy tace "Meye hakan?"
Nan ma zatai magana ta fara yunkurin amai, da sauri ta miƙe tai ɗaki tana sake yunkurowa, Mumy kasa ko motsawa tai sai kuma ta tashi da sauri har tana harɗewa tai ɗaki hankalinta a mugun tashe.
(Hmmm wai inji me ciwon baki.)
*ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*.
*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar
*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu
*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce
*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari
*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan
Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500
VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k
NORMAL GROUP 500
VIP 1000
ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130
KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730
Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
+234 903 056 9336
*Ayusher Ce*
*Da*
*Umm Asghar*
*BAQEER*
*NA*
*UMM ASGHAR*
*DA*
*AYUSHER MUHD*
*RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA TAKWAS*
{58}
Hankali a tashe Mummy ta bita cikin ɗakin sai ta jiyo kakarin Nabila daga cikin toilet, cikin sassarfa ta faɗa banɗakin a take taji wani mugun rashin hankali da bata taɓa tsintar kanta a ciki ba ya rufto mata lokaci guda ganin Nabila durƙushe a gaban toilet bowl tana kelaya amai. Muryarta na rawa tace "Ke Nabila baki da lafiya amma baki faɗa mini ba? Me ya same ki?" Ita dai Nabila babu baki don sosai ta galabaita da aman da take yi, kusa da ita Mummy ta matsa ta dafa kanta tana yi mata sannu sai dai a ƙarƙashin zuciyarta tana jin wani irin tsoro, tana tsoron kada tarihi ya maimaita kanshi akan Nabila. Da sauri ta kawar da wannan tunanin ta taimakawa Nabila bayan ta gama aman ta kuskure bakinta, tana riƙe da ita har sai da ta kwantar da ita akan gado sannan ta ƙara kallonta, sai taga tayi mata wani irin fayau fuskar nan ta ɗashe tayi fari tas duk kuwa da Nabila ba fara bace, kalar fatarta chocolate color ce. Sannu ta ƙara yi mata sannan tace "Me ke damunki kuma tun yaushe ne baki da lafiya baki yi magana an kai ki asibiti ba sai ki zauna da ciwo. Ki tashi ki shirya na kai ki asibiti a dubaki, hankalina ba zai kwanta ba idan ba kai ki nayi aka duba mini lafiyarki ba."
Gaba ɗaya jikinta yayi yaushi don haka ko magana bata son yi, da ƙyar ta iya buɗe baki tace wa Mummy "ai na samu sauƙi ba sai mun je asibiti ba, dama cikina ne yake ɗan murɗata amma tunda na samu nayi aman sosai naji relief, kawai dai hutawa nake son yi nasan daga na samu bacci na tashi gaba ɗaya nauyin jikin zai sakeni."
Wani irin kallon tsaf Mummy tayi mata sai dai bata ce komai ba ta haɗiye abinda take ji a cikin ranta ta kaɗa kanta ta fita daga ɗakin bayan ta faɗawa Nabila lallai taci abincin da zata bayar a kawo mata kafin ta kwanta don bata son zama da yunwa. Tana barin ɗakin Nabila ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya data ke riƙe da ita tun shigowar Mummy ɗakin, gyara kwanciyarta tayi ta janyo wayarta tana kiran layin Kabir sai dai har ta ƙara i rurinta bai ɗaga ba, sake kiranshi tayi amma har ta katse bai ɗauka ba, ajiye wayar tayi akan bedside drawer, dama tasan zai yi wuya Kabir ya amsa kiranta a yanzu da yake ƙoƙarin yakiceta daga jikinshi ta kowane hali sai dai ita kuma babu niyyar barin shi a tare da ita, bata fara don ta daina ba don haka sai dai yayi kauce-kaucen shi ya gama amma dole ya dawo wajenta don bata shirya haƙura dashi ba.