Sashe 152
Baqeer Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ba, amma me za ayi da auren Badaru? *** Asiya ce ta kalli Mama da ta miƙo mata wake tace wai ta surfa ta wanke za’ayi alale, kamar ita? Ai ita ko a gidansu bata daka bare hannunta yayi kanta. Kauda kai tayi gana gyara kwanciya tana cewa “Mama bana jin daɗi kin sani don haka bazan iya surfe ba gaskiya,” ta ƙarasa maganar tana gyara kanta. Ajiye mata waken tayi tace “Sai ki zaɓa ko aikin dana saka ki ko kuma ku tattara ku nemi gidanku.” Komawa tayi ta zauna don kuwa tasan bata da wurin zama banda nan ɗin don ko banza yafi gidan su, bata son tuna wahalar da tasha a komawarta wai kamar ita zasu yi ta bawa ɗumame shima sai dai ta ɗumama da kanta, gashi itace ne, da farko kayanta na lefe taso siyarwa sai dai ba dama don kuwa Bello ya taho dasu nan gidan, dole ta tattara ta taho ai ko banza nan ɗin ana ci asha kuma gidan yafi na iyayenta. Haka nan ta amsa kamar zata yi kuka tana daka tana ƙunƙuni. **** A hankali Daddy yake bin ɗakin da kallo, idanunshi ne suka sauka akan Zainab dake gefen gado ta kwantar da kanta a kusa da ƙafar shi, hannu ya kai yana son taɓata kawai yaga ta ɗago, da sauri ta dawo inda yake tace “Daddy ka farka? Ya kake jin ka? Wurin yana yi maka zafi? Akwai inda kake jin ciwo?” Murmushi yayi yace “One at a time Auta, slowly.” Hawaye ne suka zubo mata tace “Daddy kayi haƙuri na tafi na barka, gashi abinda ya sameka, ka sani?” Kai ya ɗaga mata alamar eh, tare da lumshe ido yace “Kina tunanin zasu min aiki babu izinina ne? Ni nayi signing lokacin Kabir yaje gida ya dawo.” Murmushin tausayin kansu yayi yana ƙoƙarin riƙota da sauri ta mika hannunta ta kamo nashi tasa kuka. Lallashinta yayi har ta tsagaita sannan yace “Rayuwar kenan, sannan laifina ne dana bari diabetes ya shigeni haka ba tare da sanina ba ban kuma duba canjin da nake ji a jikina ba saboda hankalina yana kan siyasa, sannan ko na sani ma me zan yi Zainab?” Hawaye ta share ta ƙara riƙe hannunshi tace “Am sorry Daddy.” “Me kike ci a Dambatta da naga kin canza haka?” Fuskarta ta shafa tace “Kai Daddy.” Gefe ya kalka ya ɗan dubi ƙofa, Zee jikinta ya bata Mummy yake nema hakan yasa tace “Tazo ɗazu komawa gida tayi ta huta,” tayi maganar cike da son janye tunaninshi. Maida kallonshi yayi kanta yace “Ba ita nake nema ba Kabir nake jira, da alama tunda na kwanta bata zo ba.” Da mamaki Zee ta kalleshi tace “Daddy me kake nufi?” Murmushi yayi yace “Tunda aka yi aikin ina farkawa lokaci-lokaci sai dai bana iya magana saboda ƙarfin allura, a iya tsawon farkawar da nayi ban ga wata mace ba bayan ke.” Jikin Zee ne yayi sanyi don bata son yi mishi ƙarya, gashi Kabir da Mubashir sunje gida jiya ma suka ga bata gidan. Bai yi magana ba hakan yasa ta juya don ta kira nurse., da kallo kawai ya bita. **** A shagon Baqeer da aka yi mishi kwatance Kabiru ya tsaya, ido ya runtse tare da sauke ajiyar zuciya, bai ga ta zama ba dole ne yazo ya nemi yafiyar Baqeer, yana ji kamar laifukanshi ne suka sauka kan Daddy, mamaki yake yi yadda aka yi shagon dashi kanshi yasa yi kaya kusan kala biyar a wajensu ashe shagon Baqeer ne, fitowa yayi daga mota ya tsaya a jikin ta inda kana gano cikin shagon, Baqeer yana zaune sanye da riga da wando yasa table a gaba yana yanka, wuyanshi ɗauke da tape sai gefen kunnenshi da yasa pencil, ɗagowa yayi ya kalli waje ta glass door ɗinsu, idanunshi ne suka sauka kan Kabir.